← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 104

Sashe 3

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren 3 tagama girkin tadauki tukunyar a wata tray tafito tai dakinsu dashi Babansu tasamu zaune kan kujera yana rikeda remote Mama zaune gefenshi da alamu abincin duk suke jira tana ganin Babanta tasake sakin murmushi da kana ganinta kasan daga zuciyanta yake, harara Mama ta watsa mata tace "Malama ajiye tukunyar ki kwaso kwano na zubama Baban ki" da sauri Baba ya watsa mata mugun kallo yace "bazaki bar yarinya ta hutaba" ya kalli Habib daya shigo yayi kini kini da rai sabida yunwa yace "wuce ka kwaso kwanuka azuba abinci" da sauri Mama tace "wai sai insa abu kanuna agaban yara ban isaba" ahankali Baba ta hanyar rage murya yace "tagaji ne tahuta, tanada kannai intai girki sai asaka kannan suyi wani abu ko" Mama zata kara magana ya kalli Fatima datake tsaye inda take kanta akasa sai zufa take yace "Zahra'un Baba ya jarabawan andubo"? Da sauri tadagamai kai tana murmushi tana kallonshi kana ganin yanda take kasan yarinyar na mugun son mahaifinta, shima murmushi ya sakin mata cikeda sonta yace "dauko takardan nagani" da sauri tai uwar dakin su Mama tabi bayanta da harara daidai lokacin Habib yakawo plates karba tayi ta zuzzuba musu abinci tazuba na Fatima kadan ta ijiye agefe har Baba zaiyi magana saikuma yayi shiru kawai baice mata komiba, yadau nashi yasa cokali ya shiga ci murmushi kawai yayi shi kanshi yana alfahari da Fatima wajen girki danko Ruka bazata nunama yar karaman yarinyar nan yanda ake girki ba. Fitowa tayi daga dakin hakan yasa tun kafin ma takaraso ya ijiye abincin shi agefe yamika mata hannu tasamai takardan wajen kafanshi yanuna mata yace "zauna ga abincin chan dauko kici" kallon abincin tayi saikuma ta kalli na kannenta ba tace komiba Allah ma ya taimaketa batada wani cin hauka data mutu da yunwa, daukowa tayi tazo ta zauna kusada mahaifinta shikuma yana duba takardan murmushi kawai yayi ya gyadakai yace "uhmm Masha Allah wanda baida Fatima baida mene....." dan murmushi tayi murya chan kasa mai shegen zaki tace "sa'a" bata fada da karfi ba sabida mamansu, murmushi Baban yasakeyi ya kalli Maman su yace "yarmu tacinye waec tass" sanan ya kalli Habib dake kallon takardan yanacin abincin yace "kagani haka nakeso kaima kadinga kokari a makaranta kaine namijin gidan nan, babanmu amman kullum na bayan kashi kake, abu daya kawai ka iya shine son abinci" daure fuska tamau yayi baice komiba Baba yataba kan Fatima dakecin abinci tana murmushi yace "yanzu sai kwaleji ko Zara'un Baba, lawyer gidan nan, Allah shi albarka, Allah ya sanya ma certificate din albarka yanzu dazaran wani tsayayye yafito sai aure ko" wani irin kunya ne yakamata da sauri ta tashi tadau abincin ta tai dakinsu, kyalkyacewa da dariya Baba yayi Habib natayashi, Baba ya girgiza kai kawai, tabe baki Mama tayi tace "yartaka da Batada mashinshini gwarama kadena tunanin aurenta yanzu dan ko almajiri batada shi ballema mutumin arziki" sosai maganan ya sosama Baba rai hakan yasa yace "aure lokaci ne Rukayya, yana zuwa akeyi kodako kana coma ne, dududu ma shekarun nata nawane? Ko ashirin bataiba dan haka kisha kurumin ki mijin Zara'una na nan tafe ko Habibun Babanshi" da sauri Habib ya gyadama Baba kai yana murmushi yace "eh Baba wlh inaso inga muma munyi biki kaman gidansu Mansur yayar su tai aure, nima inaso Ya Faty tai aure" murmushi Baba yayi yakai abincin shi baki yana sauraran labarin da Habib ke basu na bikin yayar abokin shi. Saida yagama tsaf sanan yatashi yakalli Mama dake bama Abida data tashi nono yace "bari nafita nema saina dawo" yataba kafan Abida dakeshan nono yace "Yan Matan Baban ta yauko kallona ba'ayi sabida an sami Mama" ture hanunshi tayi dagakan kafanta dan bata kaunar abinda zau hanata shan nonon nan, dan dariya yayi yace "au abun na fadane, zanga mai kawo miki cizi anjima kiyita shan nonon ki" ya kalli Mama yace "natafi" cikeda kuncin rai Mama tace "a dawo lpy" fita yayi rikeda takardan a hannunshi yana gungura machine dinshi ya kwalamata kira. "Zara'u" daga daki ta amsa "na'am Baba" cigaba da gungura machine dinshi yayi zuwa zaure, fitowa tayi sanye da hijabi kanta akasa tawuce tafita daga falon tai hanyar zaure Baba tagani haryay parking machine din awaje ya shigo zauren murmushi yamata yamika mata takardan waec din yace "Allah yamaki albarka yabaki miji nagari kinji, wanda zai soki sanan yakula dake sama dani, kome ake miki kicigaba da hakuri dudda nasan ke yarinya ce mai hakuri ga kunya, ga kawaici wata rana sai labari kinji" gyadamai kai tayi ahankali, ahankali yace "kin koshi da abincin data zuba miki"? da sauri ta gyadamai kai tace "nakoshi wlh Baba" shiru yayi yana kallonta kaman wanda yake wani tunani ganin yanda yake kallonta yasa saitaji tadamu tace "Allah Baba nakoshi kasan banamaka karya ko" sosai idanunshi sukai ja yace "nasani Zahra, bakimin karya na shaidake da wanan y'ata" hannunshi yatura a aljihu yaciro last 1k dayake da ita, mika mata yayi yace "gashi ki boye kidinga kashewa ahankali, kome kikeso ki dinga siya kinji yanzu banda kati awaya, nadawo zan loda kati saina baki ki kira Babarki ki fadamata sakamakon waec dinki kinji" karban kudin tayi tareda dan dukawa tace "nagode Baba Allah ya saka da alkhairi yakara budi" sosai idanunshi sukai jajir yace "wuce kitafi hudu nayi ki tattara kanninki kuwuce islamiyya kinji, ki dage dakaratu ilimi shine adon y'a mace" gyadamai kai tayi tace "Tom Baba" kanta yashafa da hannunshi yadan rungumota side dinshi yace "kiyi addu'a Allah bama babanki kudi, zan sayamiki waya tunda kema yanzu kin dawo budurwa kaman kowace budurwa, da sababbin zannuwan da takalma kinji, da kayan kwalliya" murmushi tayi akunyace tace "Baba karka damu komi lokacine, Allah ya azurtaka da arziki na halas katafi karkai latti" tai maganan tareda juyawa da sauri batason ta nunamai kalamanshi sun tabata, tsayawa yayi shima yabita da kallo harta shige ciki, maganan da Ruka tamai dazu ya sosamai rai ba kadanba kuma deep down yasan da gaskene Zara batada ko mashinshini guda, kuma laifinshi ne yarinya batada kayan arziki tana mace kuma budurwa datake tasawa yanzu amman kayanta sunfi name abincin saidawa kodewa, hijaban ta biyu kacal da maroon dawani mai ruwan toka sun kode harsun fara ja akai tsabagen kodewa, batada wani takalmi na fita sai silifas, kullum fuskarnan nata fayau babu komi aciki yaza'ayi saurayi zai gani ya yaba, koya sami kudi yace zai mata Ruka tahana, saisa yakeson yarinya yanzu ta shirya taje wajen Babarta hutu amman yasan Ruka bazata bariba, ganin dogon tunanin dayake yasa kanshi yafar*a sarawa yasa yajuya yafita kar hawan jininshi yatashi, machine yatada yafice daga anguwan gabaki daya.
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

✍� M SHAKUR

EPISODE 3️⃣
_FREE PAGE_
Koda takoma daki bataga Maman nasuba hakan yasa ta shiga dakinta ta ijiye komi taboye kudin da Baba yabata sanan tafito tatattare falon inda sukaci abinci ta share tafita da kwanukan ta wanke sanan tadawo ta kunna turaren tsinke afalon ganin ana kiran la'asar yasa tadauro alwala ta shigo tai salla sanan ta shiga dakinta ta sanya Ash color hijabin ta har kasa dan shine na islamiyyan su sanan tadauki jakar islamiyyan tafito, gaban dakin Maman su taje ta tsaya tai sallama ahankali, daga ciki maman tace "lafiya kin isheni da sallama yarinya saikace rainon mayu" batadamu da maganar ba dan inda sabo tasaba, ahankali tace "zantafi islamiyya ne Mama natafi"? Ihu tamata daga taciki tace "au so kike ubanki yazo yace nahanaki zuwa islamiyya ko uwar shairi da kinibibi wuce ki bacemin daga gaban daki, mayya mai neman rabani da mijina" juyawa tayi ahankali tafice tai waje da sauri sauri take tafiya kaman mai jiran wata, tayi nisa sosai tahango wata yarinya kana ganinsu kaga sa'oinnin juna itama tana sanye da Ash color hijabin kaman nata tana tsaye karkashin bishiya tun kafin takaraso wajen tace "wlh kika samu latti Fatima saina rama dukan lattin da za'a min ajikinki" dan dariya tayi ta bangaje mata kafada tace "dalla chan bamuyi latti ba har yanzu hudu bata cikaba" binta da sauri yarinyar tayi tace "au hakama zakice"? Murguda mata baki tayi tace "eh din" dariya yarinyar tayi tace "tokijirani sai sauri kike FatynBaba" juyowa tayi ta tsaya chak tareda rike waist dinta tace "ohkay ke Maryam dinan kin cika wayau, sabida muyi lattin kirama dukan ajikina ko saisa kike cewa najiraki" dariya Maryam tayi takaraso inda take tareda mika mata wani leda tace "gashi nakine" da sauri ta karba tabude taga sabon hijabin islamiyyan sune Ash wanan ma anyi dinkin mai hula mai kyau juyowa tayi ahankali ta kalli Maryam din dake kallonta, murmushi tayi ta bangaje mata kafada tace "ke dalla common, Babanmu nacema hijaban mu na Islamiyya sun tsufa, shine yace nazo shago anjima a aunani a dinka mana, shine naje kinsan yanada yadin hijabai masu kyau, na zaba yabama yaron shagonshi ya dinka mana dinki daya, nima bansa nawa bane sabida nasan bazaki saka naki yauba, sai gobe zamu saka mu fasa islamiyyan tareko" gyadama Maryam dinkai tayi saikuma ta rungumeta kawai, da sauri Maryam ta tureta tace "dalla ke dadina dake son jiki awaje zaki wani rungumeni sabida hijabi, har yanzu maganana nanan kikasa mukai latti saina rama dukan ajikinki" Maryam tai maganana tana dariya taredayin gaba, share hawayenta tayi ahankali sanan tabi Maryam din da sauri tace "toni kijirani" haka suka dinga tafiya suna shirme cikin ikon Allah koda sukakai ba'a fara taron latti ba hakan yasa suka wuce ajinsu direct aka fara karatu.
Chapter 3 · 0% Book details