← Book details Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 104

Sashe 6

Masifaffiyar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba na kokarin zaunar da ita kan gadonsu Habib, Habib ya shigo ya mikamai ledan da Maman Dady tabashi tace "Maman Dady tace kabama Ya Faty" karba Baba yayi yabude ganin me aciki yasa yabata yace "kin iya amfani dashi Zara'u"? Gyadamai kai tayi idanunta na kukkullewa dan bata gani sosai, barinta Baba yayi akan gado yaje wajen kayanta yadauko mata wani atampan na riga da zani bakida da ruwan toka sanan yadau sabon hijabin da Maryam tabata dayagani saman kayanta ya ijiye mata komi gefenta yace "lallaba ki saka kayan kinji bari nahado miki shayi nazo" fita sukayi shida Habib yawuce uwardakan su ko kallon Ruka baiyiba yay wajen kayan shayi yadeba yazuba a kofi sanan yazuba ruwa ya yagi buredi yafito tsayawa abakin kofan yayi yace "kin gama Zara? Zara" yasake kiranta shirun dayaji yasa ya kutsakai ya shiga dakin ganinta yayi tasa pant din da pad ajikinta, tasaka riga amman takasa jan zip din ta kwanta akan gadon tana wani irin rawan sanyi kaman wacce zata mutu, rasama mezaiyi Baba yayi yace "innalillahi Zara'u karkimin haka kinji" dagata yayi jikinta kaman wuta yahada zip din yaja sanan yadau zanin dagakan gado ya daura mata sanan yazauna akan gado yana kwalama Habib dake falo kira. "kawomin shayin Habib" shigowa Habib yayi da shayin ya karba yace "sha tea kadan kidan samu karfi saimu tafi asibiti ko" girgiza mai kai tayi tareda sakinmai kuka ahankali da muryanta dabaya fita tace "Baba ni kasayo min magani allura za'amin a asibiti" murmushi yamata yace "sha shayin to mugani tukunna inkinsha da kyau sai na sayo miki magani" kai shayin bakinta yayi ta kurbi kadan ko idasa hadiyeshi bataiba sai amai bata kasan dakin tayi da aman da babu abinci aciki, tashi Baba yayi yace "bari na chanza kaya mutafi zauna da ita Habib" zama kusada ita Habib yayi yadau hijabinta yasaka mata shi karan kanshi saida tace "kai wanan hibajin mai hulan nan yamiki kyau sosai" daki Baba ya shiga ya chanza kaya yadau key machine dinshi sanan yajuyo ya kalli Mama yace "bari nakaita asibiti" yan dubu biyun dake aljihun wandon shi yaciro yakalla sanan yatura a aljihu sanan yawuce yafita ya gungura machine dinshi zuwa waje lokacin 8 dayan mintoci nasafe sanan yadawo ciki, dagata yayi Habib yakawo mata silifas dinta tasaka Baba yariketa tana ta karkarwa da kyar suka fita waje saida yafara daurata kan machine din sanan yahau yatada suka tafi General.

Ahankali yake gudu da ita jin yanda jikinta ke bari, saisa sukai kusan 30min kafin sukai, parking yayi inda ake parking ya sauko ahankali sanan yakamata ya saukoda ita yana tattare ta gudun karta fadi yace "sannu Zara'una, muje" riketa yayi suna tafiya ahankali tana binshi ahankali dishi dishi take ganin gabanta daidai sun shiga ciki dip tadena ganin komi daga sama sama taji muryan Babanta na ihu "ataimakamin ataimakamin jama'a".

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_

Dawani irin gudu nurses suka gungunro wani gado aka karbeta daga hannun Baba suka dagata sauka daurata akan gadon akai ciki da ita, wani babban examination room suka shiga da ita Baba zai bisu aka hanashi shiga sanan daya daga cikin nurses din tafito tashiga wani consultation room saigata tafito tareda wani Dr dabazai wuce 35yrs ba yana sanye da farin glasses a idanunshi wuyanshi sanye da stethoscope, wajen aljihun Lab coat dinshi ta gaban rigan anrubuta Dr Imam, da sauri sauri gudu gudu suke tafiya daidai zasu shiga dakin Baba yarike hannunshi gam hakan yasa yajuyo tareda tsayawa ya kalli Baba yakuma kalli hannunshi da Baba yarike irin lafiya, kaman wanda yazare dakin Baba yanuna mishi cikin wata irin raunanniyar murya yace "likita y'ata ce acikin dakin, dan Allah kataimaka mata kar wani abu ya saman mini Zara'una likita" wani calm smile Dr yayi tareda karbe hannunshi daga hannun Baba yakama kafadar Baba ya zaunar da Baba kan kujeran dake wajen yace "abinda nakeso dakai Baba shine ka kwantar da hankalin ka kazauna anan kama yarka addu'a, abangarena kuma namaka alkawari zanyi duk abinda zan iya naga na ceto rayuw........." bai karasa maganan ba wata nurse tafito tace "Dr come she's convulsing" da sauri yay ciki yana yana kallon Baba yace "just stay here" da gudu ya shiga dakin ya karbi handglove din da wata nurse ke mikamai yana sakawa a hannu yana kallon patient din sanan yace "ya za'ayi tana convulsing bazaku cire mata wanan hijabin ba, ku cire mata and someone should on the AC" yafada ba wasa sanan yakarasa inda take bayan yagama saka hand glove din, ahankali yakai hannunshi yajuyo da ita, tareda karban wani kalan spoon da nurse kebashi yakama kumatunta ya matste bakinta yabude yasa cokalin abakinta gudun karta taune harshenta, zafin dayaji ajikinta saida yabashi tsoro, sanan ya karbi alluran dayasa abashi yakama hannunta yanemo jijiyanta yamata allura, ko minti daya ba'a daukaba tadena convulsing yay stabilising nata, yasake saka wani sabon alluran ya debo jininta awani a syringe din yabama wata nurse yace to the lab" sanan ya kalli wata nurse yace "send in the father" fita tayi bata jimaba suka shigo tareda Baba hakan yasa sauran nurses din suka fita shikuma yadauki wani paper da byro ya kalli Baba dayaga yaje ya tsaya akan Fatima yana kallonta yace "ya sunan yarka Baba"? batare daya kalleshi har lokacin idanunshi nakan Fatima yace "sunanta Fatima Zarah Muhammad" gyadama Baba kai yayi bayan yarubuta yace "meya sameta, meka damunta, tamaka complain wani abu namata ciwone"? Ajiyan zuciya ya sauke yace "ni jiya narabu da ita lpy kafin natafi aiki, nadawo gida wajajen goma sunyi bacci, saida safen nan kaninta yakirani nazo naganta babu lafiya, ciwon cikine na al'ada dakuma ciwon kai" rubutawa yayi sanan yace "daman haka yake mata"? Gyadamai kai Baba yayi yace "eh haka yake mata amman kusan watananni biyu dasuka wuce ko ciwon kai batayiba sai wanan watan kuma, sumanta kusan uku agida, kome taci sai amai, batada karfi ko kadan, tun dare babu aiki sai kuka" sake rubuce rubuce yayi sanan ya ijiye takardan yadauko wata paper yay rubuce rubuce sanan yamikama Baba yace "yanzu dai kafara zuwa kasayo wayan nan magungunan a pharmacy kafin result din test dinta yafito mufara treatment yanzu kawai stabilising condition dinta nayi ba'a mata komiba tukunna sai kaje kabiya kudin kati da folder abaka ka kawomin anan da magungunan."

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani* dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍️M SHAKUR

EPISODE 5️⃣
_FREE PAGE_

Karban takardan Baba yayi kaman mara lafiya yajuya yana tafiya ahankali yafita daga dakin yay reception, tsayawa awajen yan kati yayi yabude kati da folder, folder dubu daya, karamin kati kuma dari uku yarage duka kudin saura dari bakwai, bai karayaba yarike komi a hannunshi yawuce Pharmacy ya tsaya gaban kanta tareda mika musu takardan da Dr yabashi, gani yayi anciro gorunan ruwa, allurai daban daban dawasu magunguna ankawo gaban table anyi wani tabe tabe a computer sanan aka fitomai da wata yar takarda, namijin wajen ya mikamai yace "Baba ga takardan biyan kudi je chan wajen account kabiya kudin saika dawo mana da takardan biyan kudin saika amshi magungunan katafi" karban takardan yayi ya kalli kudin dake rubuce awajen dubu takwas da naira Dari da talatin wani irin mugun faduwa gabanshi yayi ahankali yajuyo ya kalli saurayin dahar ya juya yakoma wajen zamanshi, dan gyara muryanshi dayaji ta shakemai yayi yace "Yallabai jimana" tasowa saurayin yayi yazo yace "gani Baba" cikeda damuwa Baba yace "kaga y'ata ce ba lpy, rai a hannun Allah, duka duka yanzu chanjin hannuna basufi dari shida ba, nace kozaka bani abubuwan nafara kaima likita afara mata treatment, inyaso kafin mubar nan wajen saina biya kudin daga baya yanzu dai afara bata taimakon gaggawa" dan murmushi pharmacist din yayi yace "Baba kenan, kayakuri Baba bama haka awanan asibitin" yanamai maganan yashiga attending to wasu mutane dasukazo wajen siyan magani, gajiya da tsayuwa Baba yayi awajen kafin ahankali yadaga kafafuwan shi dayaji sunmai nauyi sosai yawuce yafita, ahankali yake tafiya haryakai wajen parking space, sabida kar mutane su ganshi yasa ya zaga ta gaban motoci yazauna kan dakalin wajen yay shiru yana kallon folder da katin daya bude mata ga sunanta ajiki baro baro, Fatima Zara'u Muhammad, yarinyar nan tun tana yarinya wahala take yanzu gashi tana ciwo baida kudin kulada ita, jiya da yafita neman kudi yaje babu wanda yasani dayabashi kudi koda sisine, Rukayya ko yasan ko Mutuwa Zara'u zatayi bazata taba cire kudin ta tabada ba, dudda yasan itama ba lallai yasamu irin wanan huge kudin a hannunta ba amman bazai rasa yarsu dubu dubu biyuba, toya fita yay bara ne? Ya tambayi kanshi, but ayanda duniya ta chanza babu wanda zai ganshi yanzu haka ya yarda yabashi kudi yayi tsaf tsaf dashi gayar shaddar shine tsaf tsaf ne za'a yarda abashi taimako, jiyayi wasu hawaye masu shegen zafi sun zubomai yakai hannu ya share amman suka kasa dena zuba hakan yasa kawai ya barsu suka slcigaba d kwarara.
Chapter 6 · 0% Book details