Sashe 8
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wula anci da Sharifa ta yi min ar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na ri e munduwar wuyana, ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin da i na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo akina tashi ki yi sallah shine abin da ta fa a ,duk da ban ta a yin ta ba hakan bai hana ni mi ewa ba na fito. ofar falo na ga a bu e hakan yasa na fita,ban aki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan auki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo ba ar leda sannan na koma ban aki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na mi e ina dariya ni aya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda. Na fito na wanke jikina na koma akina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna. an ja ajiyar zuciya kafin ta ce da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari Shikenan ya bar zancen auren? ita ce tambayar da na yi mata. Ta ce eh ya bari sai kuma ya ullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da an uwansa ya gina kin san nan haya muke Na ce to ai hakan ba matsala ba ce kin ga ku in da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su Ta girgiza kai ta ce uwar mijina ar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ar aiki na auke ki Tashi na yi tsaye na ce babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ar aikin sai na zama tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a arshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na oshi. Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare Na ce kenan yau ba za mu bu e shago ba? Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na a'ide ta fa asa.Na yi murmushin mugunta har na matsu arfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki wa anda normal mutane ba su iya gani.Yawancin an kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na auke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar ku in ka. Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta mi a min su na ri e,daga nan muka wuce wurin an yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin an mitsimitsi in nan. In auki guda? na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce auka mana Cike da masifa anty Sailuba ta ce mi za ki yi da tsidagu kuma? na ce kawai ya burge ni ne sai na auki waya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen an sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi in kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na du a ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na mi e tsaye sai idona ya sauka kan wasu afafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na mi e sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido hu u muka ha a da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji. Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu Ni ma ta idon na mayar masa wane ne kai? Ya aka yi afafunka suke na jaki? Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu aya na warai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya auko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka fa i rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa Sarah ke? Tun azu fa nake yawon neman ki sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha Ta ja baki ta ce arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na ta a saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka i ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A arshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ar rige-rigen shiga ban na yace da dariya kafin kuma na ce to anty mi yasa kuka ci alhalin an fa a muku ya lalace? Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina saboda ita da mijinta normal mutum ne! sai kuma zuciyata ta bada darammm to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne! duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai. Mijin anty Sailuba ya kar i kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa atuwar tukunya na ora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama. Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ora kan tukunya.Tafarnuwa ta mi o min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sau i ne sannu-sannu sai ga shi ya auki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki. #GIDAN ANTY HINDA Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma wa anda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke. Sharifa ta ce Mama in muka ora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi Ita ma Hindar ta yace da dariya ta ce ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi Hinda ta ce o min atuwar muciya na motso miyar nan muciyar ta mi o bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta fa o kan tukunyar miyar kwacaaaa. Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ata murfin tukunyar . Cike da yami Hinda ta auke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya fa a ba auko muzubi ku juye min miyata Allah ka ai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba cewar Hinda , Sharifa ta auko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu. Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta bu e baki ta na zage-zage an hassada an ba in ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu ku in wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bun Customer inta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ar kallon-kallon suke ita da Sharifa. Na fa ji tsoro kar aje dai in sun ara tafiya sun kai wasu ku in wurin Malam,dubi shiru babu masu saya Sharifa ta turo baki ta ce ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki irga ku in mu ga nawa aka samu cewar Hinda . Sharifa ta auki robar ku i,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta auke shi ta jefar ku in ta irga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta mi a wa Hinda