Sashe 23
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ku tuntube ta ta wannan line +234 803 235 0261* Ido cikin ido muke kallon juna ni da hajiyar birni,fuskarta shaye da mamaki take kallona yayin da ni kuma na soma disashe hasken madubin da idona,ita kuma arin hana hakan in faruwa take.Muna cikin yin haka ne madubin ya gaji da azaba ya tarwatse.Na lumshe ido ina jin anty Sailuba na jan innalillahi wa'inna ileyhi raji'un amma ban bu e idon ba don za ta gane ni ce fa na tarwatsa shi. Hannuna na ji ta janye daga kan Sharifa ta je ta zauna da kan kujera,ba tace komai ba hakan yasa na an ware idona ka an ina kallon yadda ta soma gyarawa Sharifa gashi cikin sauri.Bayan ta gama mata ne ta jawo kujera sannan ta saka ni a gaba ta ce ina jin ki Na dube ta da mamaki na ce kamar ya anty? Ban son iskanci Sarah,ki yi min bayanin garin yaya madubina ya tarwatse? Sai na ja numfashi kafin na sanar da ita sannan na ara da cewa anty wallahi hajiyar birni ba in tsafi take yi.Duk gashin da kike bata ta na amfani da shi ne wurin janye taurarin an mata,za ki ga duk wani farin jinin budurwa ya tsaya cak in kuma matar aure ce mijin zai dinga ganin ba inta ya ji ta fice masa a rai .Matsalar ba a nan ta tsaya ba zai iya ta a karatun mutum,mai ilimi ya koma dolo ko an yi karatun ba zai fahimta saboda an yi blocking nasarar shi. Anty Sailuba ta ja wani dogon numfashi ta ce in kuwa haka ne na bar sayar mata,sannan naki gashin da muka zuba mata fa? Ba za ta iya yin komai da ni ba anty,dama na saka nawa in ne don tantance abin da take yi da shi sai ga shi kuma Sharifa ta dawo saloon da alamu kuwa an yi katari ta na kan aikin tsafe gashin Sharifar ne Tsoro nake ji Sarah anty Sailuba ta yi wani iri. Kin manta wace ce Sarah ? Anty kar fa ki manta ni Siren ce babu bu atar na je na bayar da ku i don samun arfin iko,haka banda shugaba ballantana ya alubalance ni akan duk abin da zan yi.Su kuma sai abin da aka tsara musu Tashi mu tafi asibiti dai,ya kamata ki sakewa Laura mara fitsarin nan ya bar zuba Na tuntsire da dariya na ce ai wallahi ka an ma ta gani Muguntar nan naki na bani mamaki anty Sailuba ta fa a ta na rufe shago da kwa Asibitin da aka kai Laure muka je,sai exam ake ta yi mata su na kashe ku i amma an kasa gane abin da ya haifar da haka sai kuka take. Na ta e baki na ce gobe ma in an ce ki zage ni to ki zagen ki gani wallahi ba fitsari zan sa yayi miki zuba ba sai dai jini na fa a ina zuwa na dafa jikinta cak fitsarin ya tsaya da ido take kallona ta na min tambayar dama duk wannan ke ce sanadi? na sakar mata murmushi. Laure ta dubi anty Sailuba ta ce ina kika samu wannan alja... iyar? Anty Sailuba ta kece da dariya ta ce baki dai shi ke yanka wuya , wallahi ki fita harakar Sarah in ki na son kwanciyar hankalin ki yanzu ma dakyar na lala a har ta tsayar da fitsarin nan Amma Sailuba an yi munafuka yanzu dama kin san maganin abin nan amma ba ki fa a ba sai da kika saka muka kashe ku i har da cin bashi? Ai kuwa wallahi sai na sanar da Saleh ya fa a wa Bilal muguntar da kuka yi min Da sauri na ce in na bar bakin naki ya ci gaba da yin magana ko? sai kuma na juya ido na dam o ma oshinta,Laure ta ri e wuya ta na fiddo ido waje ni kuwa sai juya ido nake ina langa ar da kai.Ban barta ba sai da na tabbatar na zuba mata gubar azaba a ma oshi. Tun kafin ma likita ko kuma mijinta ya dawo anty Sailuba ta ja ni zuwa gida,kafin nan sai da muka yi sayayar abin da za a girka . Tsakar gida muka tarar da Hajiya ta na zuba wa katanga ruwa sai ta kai hancinta ta na sha amshin ginin. Na yi murmushi na ce duk laulayin ne wannan? ta juyo muka ha a ido,na ci gaba da tambayar ta ko a sayo miki goriba? nan ma shiru ta yi na ce hanjin ligidi ko orowa wanne kika za anty Sailuba ta min dundu a baya ta ce ke ban son shiririta fa Sai kuma ta fuskanci Hajiya tare da jefo mata tambaya Hajiya yanzu kin fahimci illar zuwa gidan bokaye da yi tsafi? Kin zubar da cikina kin oye shi don hana ni samun wani cikin yanzu kuma ga shi nan ya koma gare ki.Kin saduda ko a baki magani? Hajiya na kuka ta ce ki yi ha uri Sailuba sharrin she an ne da son zuciya irin nawa amma yanzu na fahimta Anty Sailuba ta kalle ni,na turo baki na ce wai ke anty har yanzu zuciyar tausayi ce da ke,duk muguntar da ta yi miki tsawon shekaru har kin manta ni gaskiya ba zan fitar da cikin nan ba Kafin na rufe baki Hajiya ta zube gabana, na ji! Amma ke za ki haifo shi na fa a tare da yin gaba na bar Hajiya da juyawar mara,ina jin ta na nishi amma ko juyowa ban yi ba ballantana ta bani tausayi. aki na shiga na kwanta kan kujera idona na kallon sama, munduwar wuyana ce ta soma motsi sai na tuna da ruhin Kaka Anaba da na oye a ciki .Na kai hannu na ri o ta munduwar wacce ta auki zafi da alamu Kaka na cutuwa a ciki.Na gyara kwanciya kafin na lumshe ido na tambayar ka lafiya kike min motsi? Ki tausaya ki sake ni,kar ki manta ko ba komai ni na raine ki Kin san akwai ranar da za ki rabu da ni mi yasa kika auko ni ? Tsarin tafiyarmu ba zai ta a zama aya ba Sarah Kaka ta bani amsa,kamar wacce aka tsikara na mi e na fita ban tsaya ko ina ba sai gidan Kaka Anaba. A tsakar aki na tarar da ita kwance jikinta duk ya kumbura alamun ta sha wuya ba laifi ,da idonta da suka zurma take kallona.Na ce yanzu kin ji abin da wa anda kike kamewa kurwa suke ji ko? Tsabar rashin imani har da jarirai da ananan yara na arashe maganar ina bu e munduwar ruhin Kaka ya fita ya koma cikin gangar jikinta,da sauri ta mi e ta na yi min godiya kafin ta ce lokacin tafiyar ki ma na ga yayi,Sarah ki kula da kan ki a sabon wurin da za ki je duk abin da za ki gani kawai ki zuba ido ki kalla kar ki yi arin saka kan ki a ciki Wa ya fa a miki wannan? na tambaye ta. Ta saki murmushi ta ce ke dai kawai ki yi abin da na ce,sannan ina yi miki fatan nasara game da soyayyar ki Kaka ba ta a burge ni ba irin na yanzu ,na rungume ta gam a jikina.Ta bubuga bayana ta ce zan yi kewar ki,amma zan dinga kai miki ziyara #GOMO A lokacin da mutane ke ta hada-hadar zuwa Masallaci a daidai wannan lokacin ne Hajiya Tambara ta shiga akin sirrinta wanda koma na cikinsa ba i ne wuluk babu komai da ke wani launi hatta tile da kafata da can rufin akin duk an shafe shi da ba in penti,labulayen ma ba e ne. Cikin son fara gabatar da aikinta ta yi ko ta gama ta saka wata ba ar doguwar riga mai hulla kafin ta bu e wani aton lula mai tsananin haske da wal iya.Shafa lular ta soma yi da hannu ta na furta wasu alasimai kafin lular ta washe ta koma jikinta kamar madubi.Gashin da ta saya wurin anty Sailuba ta zazzage ta soma duba wa,yadda ta ga na Sharifa da tarin albarka yasa ta soma fara yin aiki da shi.Wasu kwalabe ta bu e ta dangwalo turarukan ta shafe gashin sannan ta ora kan lular.Taurarin Sharifa ne suka fara yin tsalle su na fitowa su na shiga cikin lular kafin kuma su tsaya cak sakamakon tsayar da su da aka yi.Ran Hajiya Tamba ra yayi mubun acewa saboda tuni ta fahimci wani ne yayi blocking in hanyar,cike da warewa ta soma lalubo ko wane ne amma idonta sai suka yi mata tozali da Sarah .Duk yadda ta so ta cutar da Sarah kuma abun ya cuttura don dukkan jikinta allon kariya ne babu inda za a a hudu,yadda aka yi yarinya arama ke da wannan arfin ikon yayi matu ar bata mamaki kuma,madubin da ya basu damar ganin juna na tarwatse Hajiya ta ja ajiyar zuciya. Haka ta ha ura da gashin Sharifa ta soma yin aiki da na gaba har ta kawo kan na Sarah, wannan karon tsoro abun ya bata yadda ta ga umbin taurari amma sam ba ta isa ta ta a su ba kuma sosai ta fahimci na Sarah ne.Da sauri ta aje aikin ta na cewa zama bai gan ni ba doli na je na binciko ainahin asalin ki,babu Siren a province orientale wannan arya ne sai in zuwa ta yi amma ba ar Sailuba ba ce.Rigar ta cire bayan ta kashe hasken lular sannan ta fita,wanka ta yi ta shirya cikin wasu tsadadun kaya sai amshi take yi.Takalma masu tsini ta saka ta fito babban falo,kowa na gidan ya na nan amma banda Soorab, ofar akin nasa Hajiya ta kalla ta ce Soorab? shi kuma ya na can cikin blanket tunanin Sarah ya adabi ruhinsa ita kawai yake bu atar gani sai da ta yi masa kira na uku sannan ya sauka ya fita.Sai a lokacin kuma ta amsa gaisuwar da an nata ke yi mata,Soorab na zuwa ya je wurinta kamar wani aramin yaro ya ora kansa kan kafa arta ya ce Ammy fita za ki yi? Eh amma ba zan jima ba,ka ci abinci ne? Ya girgiza mata