Sashe 29
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ido ina mai umarta idon tsafina kar ki sake bu e wa sai in ni na umarce ki,in kika tsaya a haka na san da wuri Ammy za ta gano ina da power fiye da can farko wani abu na ji a ya ha e goshina tamau kamar ansa super glue an li e wurin. Anty Sarah! muryar Afnane ta katse ni,da sauri na bu e idona ina mai du awa na auke ta ina murmushi na ce My Afna ya kike? Mi kika ci yau? Uncle Soorab ya bani chocolat ta bani amsa. Ina tawa? sai ta bu e min bakinta alamun duk ta cinye,na ja kumatunta kafin na arasa tsakiyar falon. Anty Nafisa ta ce tun da kika tafi ta dame mu ina anty Sarah,har da kuka sai da Soorab ya auke ta ya fita da ita ya kwaso mata kayan za an satar kallonsa na yi sai na ga ashe idonsa na kaina,na an harare shi tare da turo baki. Ni bari kallona da wasu ido naki irin na kifi ya fa a tare da maido min martanin hararen,na saki murmushi a zuci na ce wato shi yasa idonsa ke kama da Maciji ashe shi in ne a Tunanin mi kike? ya katse ni,na ce ina ruwan ka? Kawai daga dawo wa ta ko sannu ba ka yi min ba To sannu antyna ya fa a irin na raina shi in nan,na yi dariya na nufi hanyar akina na ce ai kuwa da ma a haka kake kirana da na sa ma albarka ina jin dariyar shi har na shige aki. Kayana na cire sannan na shiga toilet,bahon wanka na cika na shige ciki ina mai aukar siffar Siren.Cike da burge wa nake kallon bindina na kifi,karon farko kenan da na ji haka.Sai da na yi wasa sosai kafin na koma mutum na fito,doguwar riga na saka ba a wuluk kafin na bu e jakar kayana da cusa a drower.Kambun Sarautata na auka na ora tsakiyar kai sannan na fiddo madubin tsafina,sai da na kulle ofa da mugun tsafi kafin na auki niyyar yin balaguro .Ta na shafi madubin tare da sanar da shi inda zan je,ko minti aya ba a yi ba sai gani a farfajiyar gidan su anty Sailuba. Duk su na waje tsakar gida su na hira,Hajiya na kwance kan shimfi a an kunna mata fanka ga kayan marmari nan gefenta alamu har yanzu jikin take ji tun bayan ta haihun. Babu wanda zai iya ganina a cikinsu,saboda iya esprit ina ne ya zo na bar gangar jikin a can Gomo.Bakin pampo na nufa na auki bokitina mai auke da kifaye da kuma protector ina.Tuni sun fara gaishe ni tare da yi min sannu da zuwa,so nake na yi wa anty Sailuba magana saboda na yi kewarta amma ban san ya za a yi na sanar da ita na zo ba. Dubara ce ta zo min kawai na kunna pampon gidan ruwa suka fara zuba shaaa,duk suka waiwayoyo su na mamaki ganin babu kowa kusa da shi.Kamar yadda na yi tunanin kuwa anty Sailuba ce ta taso domin kashe shi,duk da haka ko na yi mata magana ba za ta ji ba a doli ina da bu atar madubi.Duk yadda ta so kashe pampon haka ya i mutuwa sai ta nufi aki don nemo abin da za ta ulle shi.Na bi bayanta,ko kafin ta kai ga shiga bedroom na kunna wutar akin sai na ji ta yi murmushi mai sauti ta ce Sarah? urya akin na shiga na je gaban aton madubinta na tsaya ta yadda za ta ganina. Anty Sailuba na furta ina murmushi,anty Sailuba ta wato ido ta na mai nufo madubin ta sa hannu ta shafe shi ta na mai sake kiran sunana , fatan dai lafiya? Ki fito mana na gan ki Na saki murmushi na ce ni ce na so bayyana miki kaina anty da iya murya kawai za ki ji amma ana iya ganin mutum ta madubin? A'a ko an gani ba sosai ba sai dai buji-buji saboda dama madubi bai oyon mugu,ko aljanu da suke fito wa mutane ta madubi ai ba da dukkan siffar su ce suke fitowar ba Yaushe za ki dawo Sarah na yi kewar ki? kafin na kai ga bata amsa Bilal ya shigo akin tare da cewa pampon fa ya tsaya sai kace aljani shi ya kunna kansa kuma ya kashe kansa .Lafiya kike tsaye a gaban madubi? Waigowa ta yi muka ha a ido,na ce mata ai shi bai ganina haka bai ji na tun da iya ke aya na kira Amma in na yi magana zai ji ni ? anty Sailuba ta tambaya ta na kallona. Bilal ya ce wai lafiyar ki? Mu je Hajiya na kiran ki ya kama hannunta suka fice haka ta fita ta na waiwaye na.Ni ma a doli na koma can Gomo na shigar da esprit na wurinsa. Bokitin kuma na aje shi can kusan dressing mirror,sai a lokacin na bu ofar. Protector ina na shaida wa komai,tare da neman shawar shi ya bani amsa da in kika auke shi tabbas za ta gane sai dai ki yi mata masayan Ina zan samu wai? In na yi haka ai mun zama aya ni da ita Abu na farko da za ki yi yanzu ki binciko inda take ajiyar su,sannan ki gano mi za ta yi da shi ta yaya ne take sarrafa shi.Abu guda da zan baki tabbaci shine kowanne wai da za a yi aiki da shi sai yayi sati biyu a akin sirri kafin a soma sarrafa shi yadda ake so Shiru kawai na yi ina nazari kafin na mi e na fito,duk a halin gidan an taru ana cin abinci. Ammy ta tsure ni da ido kafin ta ce tun da muka dawo ban sake ganin ki ba sai yanzu,na aika a kira ki aka ce akin ki a rufe .Fatan dai lafiya babu wata matsala? A yadda ta yi maganar kawai na fahimci ta na zargina,kuma arya take babu wanda ta aiko ita ta zo da kanta ta tarar na rufe ofata da makullin tsafi shi yasa take son jin ba'asi. Na shagwa e fuska na mayar da kaina doluwa na ce na yi wanka tare da duba siffata murmushi ta saki ta ce kar ki wani damu na ji an ce kun yi hatsaniya a makaranta zo ki ci abinci Kujera na ja kusa da Soorab na zauna,kafin a kira mai aiki ta zo ta zuba min.Hankali kwance na soma cin abincin,kafin na bu e idona ayar nan ta tsakiyar goshi don haka kawai na ji ban yarda da abinci da Soorab ke ci ba ai kuwa sai na yi arba da wani magani da ta zuba masa.Ban san na mine ne ba amma tabbas babu alkhairi cikinsa,hanya guda ce za ta sa na gane shine na ana abincin. Cikin ikon Allah kuwa wayar Ammy ta auki ringing ta mi e ta koma can gefe ta na amsa wayar,cokalina na sa cikin abincin Soorab na ebo tare da kai bakina.Ko minti aya ba'a yi ba na soma jin wani abu cikin kwanyata,kamar yadda ake goge wa a daga memory haka abubuwan da suka shafi rayuwata ta oyayyar duniya suka fara guduwa.Da mugun sauri na kai hannuna na shafi munduwar wuyana zuuuu suka dawo daidai,don ara tantance zargina haka na ara ciko cokalin na ci abin da ya faru da ni da farkon ya sake faruwa. Na yi shiru ina tunani ita rayuwar nan sam ba ta san jini ba? Ta yaya mutum zai cutar da wani nasa? Akan mi Ammy ke baiwa Soorab magani domin ya dinga manta abubuwa? banda mai bani amsa ya zame mini dolina na binciko haka,yanzu aiki biyu ne a gabana. Sam Ammy ba ta ara bi ta kan abinci ba, akinta ta koma ta na mai cewa Soorab kar ka manta da madarar ka ta na cikin frigine inka ka sha kofi guda kafin ka kwanta da to Ammy ya amsa mata bawan Allah ya cinye abincin shi tasss.Haka sannu a hankali duk kowa ya fara tashi,Nawaf ya ja matarsa da arsa Afnane wacce tuni ta yi bacci,Nawas kuma amaryarsa ce ta kira shi a waya ya tashi.Soorab ya soma hamma alamun bacci shi ma ya mi e ya haura sama.Table in sai yayi saura daga ni sai Soorabiyya, hummm ! ta yi ila don ta jawo hankalina kuma ta yi nasara don sai da na aga kai na kalle ta muka ha a ido. Kamar jira take ta ce na san ki na da MAITAR IDO! Ko da na ki fa a mini ba na sani.Tun ranar da kika zo na fahimci haka,kafin ke Ammy ta kawo wasu an matan bila'adadin don ba zan ce ga yawan su ba.Da farko za ta nuna miki auna ta kira ki kamar ar cikinta,a arshe ta mayar da ke ma iyar ta Soorabiyya ta fa Na ce yanzu da kike fa a min mi za a yi? Ta yi wani murmushi ta ce ina so ki yi taka tsantsan,domin amfani take da ke a doli akwai wani aiki da za ki yi mata Shiru na yi ina nazari, Soorabiyya ta ci gaba da cewa duk abin da kike yi ina kallon ki,na ga kin ci abincin Soorab sannan zuwa yanzu kin fahimci mike faruwa,dalilin yin haka kawai kike son sani ko ba haka ba? Kai na gya a mata kamar wata doluwa ina kallonta,sai da ta waiga ta ga ba kowa sannan ta taso daidai kunnena ta ra a min saboda Ammy ba ta so Soorab ya san ainahin asalin shi da kuma power in da yake da sai ta koma wurin zamanta ta ci gaba da cin abincinta. To ke mi yasa kike son a doli sai kin yi haramtacciyar mu'amala ke da an uwanki? na samu kaina da jefa mata tambayar,ta ajiye cokalin hannunta ta ce kafin ki yi min wannan tambayar akwai wacce ta dace ki yi,duk lokacin da kika shirya yi min ita kuma ki same ni a akina ba ta rufe baki ba na ce na shirya Da kyau! ta furta tare da tashi ta nufi akinta ni ma na take mata baya,kamar yadda nake da kalar tsafina ita ma nata daban