← Book details Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 47

Sashe 39

Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labarin ahalin ki haka ne ko? na tambaye ta,sai ta jinjina kai kafin ta ce lokacin da nake yarinya, gidanmu wuri ne mai cike da sirri da abubuwan ban tsoro. Zagaye yake da wani an madaidaicin jeji da ke can nesa da sauran auyuka,an zagaye wannan jejin da wasu manyan tsafi da yasa babu wani mahaluki da zai iya gigin shigarsa. Mahaifina mutum ne mai yawan fushi, da idanu masu hu a da kamar suna gani fiye da mayafin gaskiya abin da idon mutum ba zai iya gani ba shi mahaifina ras yake ganinsa. Ita kuwa mahaifiyata tana da taushin hali da auna, amma inuwar ba in ciki a kullum sai ta ga kamar tana nauyaya mata. Mahaifina mutum ne mai ilimin zamanin da, mai bin dabarun asiri. Ya na shafe dukkan dare ya na karanta abubuwan shirka,tsafi sannan ya na yin zane-zanen da aka haramta da kuma alamomin makirci a cikin urar asa. Mutanen kauyen sun guje shi, suna jin tsoronsa saboda iliminsa da ayyukansa na ban mamaki. Su na yin ra e-ra in cewa ya yi yarjejeniya da ba en ruhina , shi matsafi ne. Mahaifiyata, duk da cewa tana goyon bayan mahaifina a koyaushe,amma wani lokaci kamar ta na tsorata da ayyukansa. Na tuna na gan ta tana kuka cikin sauti asa- asa yayin da yake shirya surkullen shi. Duk da wannan, ta zauna a gefensa, ba tare da ta a yin orafi ba. Wata rana da dare, yayin da wata ya cika sai na ga wata inuwa tana rawa a kewayen gidanmu,mahaifina ya zo ya ja ni ya kai ni cikin babban aki inda ya shirya bagadin da aka rufe da alamomin ban mamaki. Mahaifiyata ta na a tsaya a can, idanunta a rufe, kamar mai bacci. Zuciyata ta cika da tashin hankali, don na ji alamun wani mummunan abu zai faru. Mahaifina ya fara karanta surkullen tsafi a wani tsohon harshe da ban fahimta ba. akin bai da yalwar haske,wutar kyandir ce da aka kunna, sai nuna wata inuwa take kamar ta fatalwa a jikin bango. Kwatsam sai mahaifiyata ta bude ido ta kalle ni da wani kallo mai cike da tsantsar kewa da so marar iyaka, kamar ta san abin da zai faru. Cikin sauri mahaifina ya fitar da wu a daga cikin wasu ruwa ya abawa mahaifiyata. Daskarewa na yi a tsaye, da na so in yi kururuwa, sai kawai na ji babu wani sauti da ya fito daga bakina tamkar wata baibaya. Mahaifiyata ta fadi a hankali, murmushin ba in ciki a le unanta. Daga nan na fahimci cewa mahaifina ya sadaukar da ran mahaifiyata don yin yarjejeniya da esprits in da yake yi wa hidima. A madadin power da ba za a iya aunawa ba, ya ba da rayuwar matar da yake auna. Amma abin da bai sani ba shi ne wannan yarjejeniyar ba ta tsinana masa komai sai dai ta kawo masa bala'i da halaka ta ne. Kwanakin da suka biyo baya sun zo da abubuwan mamaki da na ban tsoro. Gidanmu ya cika da inuwar ba aken esprits duk inda ka gifta inuwa ce, in ka shiga wani lungu haka za ka dinga jin us kamar eraye na yin hira wani sa'in ma har da dariya. Mahaifina, ya yi nadama, daga arshe ya bace a cikin dajin, ya bar gidan at har yau ban sake ganinsa ba. Har yanzu ina zaune da nauyin wannan gadon. Na bar gida na tsawon lokaci, amma tunanin wannan dare bai taba barina ba. Na san cewa har yanzu esprits in da mahaifina ya kira suna nan su na jirana , ko kuma suna j iran lokacin da za su bayyana a gare ni tun da shekaruna sun kai Marwan ya ce ko dai ki na ganin esprits in da ke tare da Mr Shakal su na da ala a da ke? Tun da shi ma kusan tsohon tsafi yake yi ba na zamani ba Ban sani ba Marwan sai in bincika wa za mu yi,ina tsoron kar wurin na je na nemo iba na samo rama.Banda tabbacin zan yi aure,amma ina da tabbacin muddin na ta ilo su to za su dawo kaina su addabe ni Shuru na yi ina nazari kafin na ce zan yi aikin da kaina Mi ? Da kan ki fa? Marwan ya tambaye ni da sauri,ita kanta Naila in cewa ta yi anya dai Sarah? Na ce zan yi! Abin da nake so da ke shine ki kawo min zaren kayan da kika ta a sakawa a jikin ki Marwan ya ce ko yanzu ta na iya cirar miki na uniform inta ko kuwa? Na ce shawara mai kyau sai na gama asan sket in Naila na ciri zaren kafin na ce muna bu atar shiga akin sirri don a can zan addamar da surkullen Mu je kawai Mu uku muka nufi akin sirrin makarantar,idona na juya suka kawo haske su suka zame mana fitila har muka isa gaban Ball in tsafin.Ni ce da kaina na sarrafa ta kafin na soma gudanar da aikin,zaren da na cira na ora kan lular kafin ta soma bani matakan da zan bi wurin cimma nasara. Marwan ebo ruwa please ka mi a wa Naila ta wanke fuskarta da su na yi furicin ba tare da na juyo ba. Cikin akin babu abin da babu na bu a,da sauri Marwan ya je ya ebo ruwan cikin wani kofi mai an fa i Naila ta wanke fuskar ta kafin ta mi o min ruwan. Na ajiye su kafin na zube kan gwiwaina, mi za ki yi Sarah ? Marwan ya tambaya muryarsa da alamun tsoro a cikinta. nelaaz shavise Naila am b sss! Awush Shakal zombw na soma karanta formula ido a rufe,ruwan da ke gabana ne na soma jin su na fitar da tiriri yayin da kuma suke wani zugur-zugur su na motsi kai kace akwai wata halitta a ciki. Waooo! Naila matso ki gani cewar Marwan,daidai nan ni ma na bu e ido fuskar Naila shimfi e a ruwan na saka yatsana manuniya na hagu a ciki ina mai aga murya na ce ki dawo bisa tawa ko gama rufe baki ban yi ba fuskata ta riki a zuwa ta Naila duk suka waro ido .Marwan ya ce Sarah wa ya koya miki wannan? Ba wannan za ka tambaya ba,cewa za ka yi yanzu ina za mu lalubo Mr Shakal ? Amma in wani ya gan ki fa zai auka ni ce,am..ina nufin sabuwar mahaifiyata wacce nake zaune wurinta Na sakar mata murmushi na ce kar ki damu don wannan,Marwan za ka binciko min inda Mr Shakal yake ni kuma zan shirya wani sabon shirin ya arsa don ba kai tsaye zan je gare shi ba Ok to babu damuwa,Naila zo mu duba cewar Marwan ya na matsawa kusan Ball Ni kuwa fita na yi na barsu,can cikin aji na koma da idona na tsakiya goshi na yi aiki har na samo aya daga cikin an matan ajin wacce ke period.Ban wani bai wa kaina wahala ba daga inda nake na yi amfani da idona na jawo period in nata ya dawo gare ni.Ko da na koma na tarar da har sun gama binciken, yanzu ya fita daga wani gidan sha atawa sun yi waya da wata budurwa akan cewa za su ha e hotel saboda ta ga period inta Shuru na yi ina nazari kafin na ce Naila power inki ta hawainiya ya kike ki na sarrafa ta? Ta ce kallon mutum nake sai na hardace kalar kayan jikinsa daga nan sai na canza. Na ce da kyau ! Za ki ban aronta zan juya siffa na zama budurwar da za ta je wurinsa Naila ta bu e bakinta tare da zazzalo dogon halshen ta Coken ina na fiddo daga cikin gashi na dangwalo yawunta wanda suke auke da dafi. Fita muka yi dukkaninmu muka samu taxi ta kai mu hotel in,motar Mr Shakal muka gani a ajiye.Haka muka tsaya a harabar hotel in duk wacce ta shigo sai mun yi mata magana saboda mu samu muryarta don ta wannan hanyar ce kawai za mu shaida ta. A haka har wata ba ar budurwa ta shigo,muka gaishe ta kamar abun arziki ta na amsa wa na yi amfani da power ta wurin saka ta yin bacci Marwan da Naila suka ja ta baya na bu e jakarta na ciro wayarta na kira Mr Shakal na shaida masa na zo.Tuni na riki a zuwa siffarta,lambar akin ya bani na shiga cikin yau i yadda na ga ta na tafiya har na je akin. Ya bu e daga shi sai towel,na lumshe ido ina sakar masa murmushi,ya bani hanya na shiga sai na tarar da akin babu wan lantarki haske yayi aranci. Bari na je na an watsa ruwa na furta ,da sauri ya ce no kar ki wanke ki bar min jikin ki haka ai ina son arnin jini yayi furicin tare da du awa asa ya na sunsuna ta tsabar maita har yawu ke masa zuba. akin ne ya ara yin duhu sai na ga inuwa kamar mutum ya wuce,sam ban damu ba sai kan Mr Shakal da na soma yamutsawa asan zuciyata na yin lugude tuni ya yi asa da wando jeans in jikina ya na shirin jan pant ina na ciro Coken ina na caka masa shi a ido yayi wani mugun ihu tare da yin baya.Tuni wan lantarki ya soma yin wasa ya kunna kansa ya kuma kashe kansa,inuwar da nake tunanin guda ce tal sai na soma ganin su na faso bango su na ara yawaita cikin akin.Farmaki suka soma kawo min ina tare wa,manyan esprits ne masu shan jini burinsu guda kawai su cije ni .Mr Shakal na ta arin cire Coken wanda ke zu e masa arfin iko amma ya kasa,baki ya bu e ya soma yin alasiman tsafi ya na kiran sunan wani babban doda asa da minti guda dodon ya faso rufin aki ya sauko bakinsa na zuba da jini ga wasu irin ha ora sun fi girman gatari ya bu e baki tare da yin wata hargowa zai farmake ni kamar daga sama na ga wata dun ulen wuta ta biyo ta bayana ta tarwatsa dodon. Na juya da sauri sai
Chapter 39 · 0% Book details