Sashe 30
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yake ta wannan hanyar ta bi ta rufe ofar gam kafin ta je ta bu a akwati ta auko wani aton hoto ta ajiye shi kan bed. Idona na ora kan hoton,hoton ahali ne dukkan familyn su na ciki in ka cire Afnane wacce na yi imanin tun kafin a haife ta aka yi hoton. Wani abu ne ya soma fizga ta wato hoton shi mutumin da nake zaton mahaifin su ne.Fuskarsa na shafa ina mai ambaton sunansa can asan zuciya Ganduuu! iska ne ya soma tashi labulayen akin Soorabiyya suka fara yin sama,ina jin sautin murmushinta da dukkan alamu ta tsara yin haka ko kuma ta san hakan zai faru. asan tile na soma jin ruwa na ulowa, sannu a hankali akin ya cika tan am da ruwa na bu e ido tare da shafar daidai iya gangar jikinsa sai na bugi ruwa. Da farko hoton ne ya bayyana cikin ruwa gabanin ya soma motsi,cikin abin da bai yi minti biyu ba marigayi Gandu ya bayyana gare ni na tabbata kuma ita Soorabiyya ba ta ganin abin da nake gani don sai tambayata take abin da ke faruwa. Ido na ura masa ina kallo, ata Sarah! ya furta wanda na san ba shi ba ne esprit insa ne da na kira tun da asan ruwa ya zo nan Uncle na samu bakina da furtawa ina mai zaunawa hakan yayi daidai da bayyanar siffata ta Siren. Hannuna ya kama tare da ja na muka yi tsunduma cikin ruwa,ina jin Soorabiyya na faman kiran sunana ta na cewa Sarah ki na ina? sai dai ba zan iya bata amsa ba don tuni na tafi wata duniyar ruwa. Tsakiyar wasu blue in ruwa Uncle Gandu ya kai ni inda ke auke siffofin halittun ruwa iri-iri,akwai Siren irina akwai kuma masu rabi mutum rabi Maciji kamar yadda shi Gandu in yake.A cikin duniyar ruwan shi ne sarkinsu,haka ya gabatar da ni da mahaifiyarsa wacce ta kasance Siren .Wani furen fower ta auko ta ma alla min a gashi ta na cewa Princess Sarah muna ta tsumayen zuwan ki ke da Prince Soorab shiru har yanzu sai yaushe za ku dawo duniyar ku? oran asa ba naku ba ne Sarah ku dawo duniyar ku tun da mutanen samanta mugaye sun fi yawa daga cikinsu King Gandu wato mahaifin Soorab ya ce , akwai aikin da za su yi a gabansu doli sai sun arasa shi,ungo wannan ki adana shi a duk lokacin da kika samu lokaci ki ri e soke shi cikin rigar ki ta wannan hanyar za ki samu shu iyar rayuwata da na yi a doron asa,sannan ke ce wacce za ki dinga haskawa Soorab tarihinsa da asalinsa .Abu na arshe da zan sanar miki tun ranar da kika ora afarki cikin gidana a ranar ni da mahaifin ki muka ora aurenki da Soorab Wani abu ne ya mi o min mai kamar gashin kaza sai wal iya yake ya na yallin wuta,na kar a tare da ora shi tsakiya irjina a sannu a hankali ya fasa allon irjin nawa ya samu wuri ya zauna.Ban san ta ya aka yi na fito daga ruwan ba kawai dai na tsinci kaina a tsakiyar gadon Soorabiyya.Ina bu e ido ta saki murmushi ta na cewa yawwa Allah na gode ma ido na tsura mata sai ta ce tun jiya nake ta faman jijigar ki fa amma kika i tashi sai yanzu,tashi ki koma akin ki asubah ta kusa kar Ammy ta neme ki ba ta gan ki ba dakyar na sauka daga bed in ina jin kaina na juyawa,ba tare da nace mata komai ba na fita na koma akina.Toilet na shiga na sakar wa kaina ruwa,sai a lokacin abubuwan da suka faru da ni asan ruwa suka dawo min,da mugun sauri na bu e ido ina cewa ni matar Soorab ce? sai na dafe saitin zuciyata,hannuna ne na ji yayi girrr tare da soma fitar da haske sai na lura abin nan ne mai kama da gashin kaza ke wal iya. Fitowa na yi na saka wata doguwar rigar bacci kafin na nufi akin Soorab,a kwance na tarar da shi kan bed ya na sharar bacci kofin madarar da ya sha na gefensa ita ma irin maganin da ta zuba masa a abinci akwai shi ciki. Blanket in da ya rufa na yaye,siffarsa ta Maciji ta bayyana ko ka an ban ji tsoro ba don yanzu na tabbatar mu in ba jinsin bila'dama ba ne addara ce ta kawo mu doran asa. Idonsa ya fara bu e wa a hankali har ya zube su a kaina,ban yi wani jinkiri ba na haura gadon.Kamar wacce ake ingiza wa haka na since ullin da na yi wa rigar baccina,surata ta bayyana Soorab ya waro ido ya na shirin mi e na danne shi irjinmu suka ha e da da juna.Girrrr! Kake ji,da sauri ya birkita ni na koma asan shi,tambayar farko da yayi min ita ce ke wace ce? Ji nake kamar na san ki ban basa amsa ba sai idona da na lumshe saboda tarihinsa da ya soma yi min dirar mikiya a kwanya.Ina cikin wannan yanayi na ji bakinsa kan nawa ya na sumbata ta,na bu e idona tarau cikin nasa hasken su suka shiga cikin nasa in.Da sauri yayi baya ya na huci kamar Maciji in ga mutum ya na son sarar shi,a daidai nan na samu makullin amsar tambaya ta . Soorabiyya na son ta kusanci Soorab ne don banka o duk wani sirrin gidansu,sai in yayi mu'amalar farko ne da mace kawai power insa ta farin Maciji ga kyawu ga mugunta za ta bayyana....... ```MRS SADAUKI *Book2* My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya ku in karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne . Rigar baccina na ulle kafin na tashi zaune na ce ka ce kamar ka san ni ? Um haka ne ni ma ranar farko da na soma ganin ka sai da na ji kamar na san ka a wani wuri.Sai yau na gane ashe haka in ne,ka tuna wata rana a ashin ruwa mun ta a ha uwa har ka kar e min munduwar wuyana? Da mugun sauri Soorab ya juyo tare da kafe ni da ido,na gya a masa gira na ce eh Princess Sarah ar sarki Mohan wacce ka aura kwanaki uku da suka wuce ni ce nan! Ai na san ka gani a mafarkin ka ana aura ma aure? shiru yayi bai bani amsa ba,na saki murmushi tare da kai hannu ina shafar irjinsa na ce ka na ji Soorab abin da nake so kawai ka yarda da ni,ba zan ta a cutar da kai ba sai dai na kawo ma nasara a rayuwa.Zan koma akina,zuwa gobe da safe zan baka labarin wani sarki da ya ta a zuwa doron duniya ya auri wata bil'adama Har na fice daga akin bai ce komai ba,ni kuwa ina komawa sashe na zaune na yi na kasa komawa bacci.Har aka gama sallah ina a haka,Ammy ta shigo ta ce ki yi sauri ki shirya arfe bakwai yau za ku shiga aji da mamaki na kalle ta amma sai na mi e na shiga toilet na yi wanka na saka uniform. Ita ta zo da kanta ta fiddo ni zuwa falo na yi tunanin abinci za ta bani sai na ji kuma ta na wala kiran sunan Soorab,an auki minti biyar kafin ya fito cikin shiri mai kyau hannunsa auke da wata jaka kamar wani malami . Ku je ya sauke ki! Yau ba zan samu damar zuwa ba ina da ba in da za su zo Ammy ta fa a ta na mai sakar min murmushi,haka na bi bayan Soorab muka shiga mota,mai gadin da ya bu e mana get muka fita ba shi ne na jiya ba lokacin da muka dawo.Shiru na yi ina tunanin mafita ,sai kuma na tambayi Soorab wai ya aka yi kullum cikin canza masu gadi ake ko ba a biyan su albashi ne? Ki zuba ido ki kalla kawai,kamar yadda na yi ya bani amsa ba tare da ya ko kalle ni ba. Don mi? Amma ba ka tunanin... yayi saurin katse ni tare da ce min don Allah ban son ji,tun da aka haife haka na taso nake gani har izuwa yanzu ban san dalili ba.Kawai ki bani labarin da kika ce na Sarkin nan Na ja numfashi na ce a tarihin duniya an yi tifa in cewa Siren na kawo haske a rayuwar bil'adama, wannan dalilin ne yasa mutane ke tururuwar zuwa neman taimako ga esprits in ruwa wanda yawancinsu Siren sun fi yawa.An yi wani an sarki wanda mahaifinsa ya kasance rabi mutum rabi Maciji ,a kullum ya na ganin mahaifinsa na bai wa mutane taimako da ya tambayi mahaifin nasa dalilin da yasa mutane suke zuwa su na basa kyautar jini ko kuma su kafircewa Allah don kawai ya basu tabarakin abin da suka zo nema.Sai uban ya ce ai mu Allah ya bamu wata power ne ta yadda za mu iya cankar goben mutum sannan mu juya wani al'amari ya zamo gaskiya,da wannan ne kake ganin halittun ruwa ake samu jinsin Siren ,don wani lokacin sai mun yi amfani da su kafin mu biya musu bu atar sai na yi shiru ina kallon Soorab da bu e kunnuwa ya na saurarena, in na fahimta a can farkon duniya babu Siren sai esprit in ruwa kawai,yadda mutane suka butulcewa Allah su na zuwa neman taimako wurin ruhikan da ke cikin ruwa ,sai suke musu shara in sai sun yi lalata da su da wannan aka fara samun halittar Siren saboda cu anyar jinsi biyu? Soorab ya tambaye ni ya na mai waigo wa ya kalle ni. Na jinjina masa kai na ce eh haka ne, esprits in ruwa siffa biyu ce da su ko kifi ko kuma Maciji ,to ya danganta da wane ne yayi mu'amala da mace bil'adama ta hakan ne za a tantance irin da za a samu .Wasu rabi kifi ,wasu kuma rabi Maciji .To shi ma wannan an