Sashe 28
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutane normal ne suke ganin wannan marar kyau amma a wurin mu za mu iya kiransa da wata baiwa musamman in har za ka iya sarrafa wannan MAITAR IDOn wurin motsa abubuwa.Misali,Sarah zo nan ta fa a tare da kirana,tashi na yi na je can inda take a tsaye na fuskanci alibai ni ma. Madam ta zuhe jakarta ta fiddo gorar ruwa da kuma kofin gilas ta ajiye kan table sannan ta zo ta tsaya kusa da ni ta ce yawwa Sarah nuna wa an aji yadda ake amfani da ido wurin sarrafa abubuwa,ki zuba ruwan can cikin kofi Ji na yi kamar an takura ni musamman yadda an ajin suka fara shewa su na jira su ga na yi, mu je mana yi Madam ta sake fa a ta na girgiza kafa ata. Saitin inda ta aje abubuwan na duba sannan na juya ido,da farko kofin na cira ya bar jikin table ya tsaya cikin iska sannan na bu e murfin gorar ruwan ya fa asa kafin na cira gorar na umarci ruwan da su shiga cikin kofi waoooo kake ji kafin a fara ta i,Madam ta je ta auki kofin ta ce Koma ki zauna Bayan na koma wurina ne,ta ce na san da yawan ka su so ace su ma za su iya yin wannan? duk suka amsa da eh,Madam ta ci gaba da cewa zan koya muku yadda ake sayen MAITAR IDO ta hanyar tsafi amma kafin nan zan ci gaba daga inda cours in mu ya tsaya sai ta ara fiddo wata kwalbar mai auke da mai sannan ta ce in mutum na son ya gane ya na da evil eye ko kuma an jefe shi da shi hanya mafi sau i sai ya samu ruwan ZamZam sai ya zuba su a kofi ,sannan sai ya iga mai a ciki igo uku.In man yayi sama ya ha e wuri guda to lafiyar ka lau in kuma man ya ha e da ruwa maimakon yayi sama to ka na da evil eye ko kuma an jefe ka da shi ta na gama fa a haka sai ta kira Marwan ,tashi yayi a tsorace ya isa gare ta kwalbar man ta basa ta ce ya iga.Hannunsa har rawa yake ya iga har sau uku,Madam ta yi murmushi ta ce kun ga bai da komai a jikinsa ga man ya yo sama duk sai ta bi kowa ta nuna masa a arshe kuma ta auko wani kofin ta cika da ruwa sannan ta kira ta bani man ni ma na iga,a nan take ya cakule cikin juna suka garwaye da ruwan. Wooo! duk suka fiddo ido, wannan kuma ya tabbatar musu da ina da MAITAR IDO,wata aliba Madam ta kira wato abokiyar fa ana mai siffar hawainiya. Sarah jefa mata wayar cuta ta hanyar kallo cikin salon burge wa ko kuma na Madam ta umarce ni ta na mai auko kofi na uku ta cika da ruwa,cike da iyayya na kalle ta jikinta sai rawa yake. Madam ta tambaye ta ya sunanta,kamar za ta yi kuka ta ce Naila Yawwa Naila kar ki ji tsoro dukkan mu nan abu aya ne,duniya guda muke zo ki iga mu gani hannunta na rawa ita ma ta iga mai da ruwan suka cakule,Madam ta ce yanzu kun gani da idon ku? To a cours na gaba zan nuna muku yadda mutum zai yi ya samu MAITAR IDO don haka ina bu atar kowa ya zo min da Kare in babu shi gidanku to ka saya.To kafin mu tashi yanzu ya za a yi Naila ta rabu da wannan cutar da Sarah ta jefa mata? Duk ajin yayi shiru hakan yasa Madam ta bai wa kanta amsa Akwai hanyoyi da dama,ta hanyar amfani da gishiri,zuba turaren magani,ko kuma wanka da ruwan Floris wanda shi kuma ya na bu atar addamarwa wacce sai an kunna kyandir ,an yi rawa da wa e-wa en baitoci ga ruhika.Don haka za mu auki hanya ta arshe dukkanku ku mi e za mu je akin sirri na makaranta Haka Madam ta fita mu kuma muka take mata baya,wani lungu muka bi kafin mu zo wata ofa mai auke da matatakala alamu gidan asa ne za mu shiga. Kar wanda ya ji tsoro ku shigo kawai Madam ta fa aya bayan aya duk muka tsintsi kanmu a cikin akin mai bala'in duhu ga uwar ura tamkar ana shara,tuni wasu sun fara yin tari.Muryar Madam ce ta fara yin wani baiti na tsafi a hankali sai kyandirori suka fara kawo wuta hasken akin na ta ara hauhawa.A alla kyandir zai kai ari biyu,don duk bangon akin aka zagaye haka muka dinga juyawa muna kallo adadin yadda Madam ke wa a adadin yadda suke ara kunna kansu har duka suka kawo wuta. Wani dandamali ne a gaban mu an yi masa ado da jan labulaye da kuma capet ,ta saman shi an yi zanen on kai da kuma warangwal .Naila Madam ta jawo ta kwantar sannan ta rufa mata jan yale,wasu ruwa ta auko koraye ta soma fesa mana a nan take kayan jikinmu duk suka canza launinsu zuwa jajaye hatta na Madam Ku nutsu yanzu alloli da ruhika za su sauka a nan,duk wanda yake da wani udiri a ransa to ya matso shi cikin tunaninsa za su amsa masa Madam ta fa a duk muka jinjina kai,wani farin abu ta soma zagaye Naila da shi wanda nake kyautata zaton gishiri ne kafin kuma ta kunna kyandir ta ora shi daidai kanta .Iska ne ya soma tashi wuuul-wuuuul aya bayan aya kaf kyandirorin akin suka fara mutuwa da kansu, akin na aukar duhu sai aka fara cida ruguguguuu! A sannu a hankali na soma jin wani yanayi mai nuni da bayan mu akwai wasu ba i da suka hallaro cikin akin,ido na lumshe na soma fa ar burina shi ne na zama mai arfin iko fiye da Ammy shine babban burina.Babban an yatsan afata ne na hagu ya soma yin girrr , bisanin na soma jin wani abu na shiga jikina kamar tafiyar tsutsa har ya zo daidai tsakiyar goshina .Wasu tafukan hannu na ji kan fuskata sun li e min idanuna yayin da tsakiyar goshina kuma ya soma yin motsi taram na ga ido aya ya bu e wanda ya bani damar ganin duk abin da ke faruwa,Ammy da ta shigo da mu nan don baiwa Naila taimako ta buge da cutar ta.Dogon suma ta jefa ta,ta yadda ba za ta san abin da take yi ba sannan ta ware afafuwanta ta na janye waya wayin ta na haihuwa wanda ko aure ta yi ba za ta ta a samun ciki ba..... ```MRS SADAUKI *Book2* My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya ku in karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne . Da mugun sauri na rufe idona ayan da ke tsakiyar goshi ganin Ammy ta juyo da alamu ta ji a jikinta ana kallonta ne.Can kuma na bu e shi a hankali,abin da na ara ganin sai ya dagula mini lissafi yadda Ammy ke urawa Naila wani abu ta gabanta,shi ma tuni na samu abin da yake nufi wato duk lokacin da wani namiji ya kusanci Naila to za ta dinga tatsar arfin jikinsa ne yayin da kuma Ammy za ta san dubarar da za ta yi ta kar e shi wurin Naila. Yanayin akin ne ya soma canza wa,tuni kuma hannun da na ji ya rufe min ido shi ma ya gusa akin ya au haske sai Madam wato Ammy ta ce kowa ya zo ya ibi ruwan nan ya watsa wa Naila haka muka dinga yi aya bayan aya har sai da dukkan aliban kowa ya zuba ma Naila ruwa,a arshe Madam ta zuba mata sai kawai muka ga Naila ta mi Duk ta i suka shiga yi banda ni da na ure Naila in da ido,sam kamanninta sun canza ba kamar azu ba daga muka shigo cikin akin sirrin ba. wayar idonta ta sauya launi daga fari zuwa ba i mai ruwan toka,na sani babu wanda ya gano haka sai illa ni aya tal ni ma in a iya idona na tsakiya kawai nake iya ganin haka amma idona biyu wanda aka haife ni da su normal nake ganinta. Fita muka yi daga akin sirrin,mun gama dukkan wani cours sai kuma gobe.Kafin mu watse Madam ta raba wa kowa wani aramin jan littafi,motarta muka nufa yanzu ita ta tu a mu zuwa gida fuskarta cike da annuri yayin da lokaci zuwa lokaci take ta a jakarta inda ta oye waya wayin haihuwar Naila.Haka kawai na ji raina ya iya mini,na sani na yarda ni matsafiya ce kuma muguwa sai dai ba akan kowa nake gwada haka ba sai wanda ya shigo gonata.Sa anin ita Ammy wa anda suka yarda da ita ma cutar su take yi,shiru na yi na kasa cewa komai a zahiri littafin da ta raba mana nake dubawa amma a ba ini tunani nake ta yaya zan sace waya wayin nan nake a haka har muka isa gida babu mai magana. Ana bu e get in na kalli mai gadin ,sam ba shi ba ne wanda na bari lokacin da zan tafi makaranta. angaren da aton macijin yake na kalla, Ammy ta ce ya dai Sarah mi kike kallo? na maido dubana gare ta kafin na yi murmushin ya e na ce komai flowers in can sun yi min kyau Ta daidaita parking kafin ta ce duk wani wanda zai zo gidan nan sai ya fa i haka su na da matu ar kyau Ban ce komai ba na fita,ni ke gaba ta na bayana,sam ban so ta fara zargina sai na ci gaba da duba littafin har na shiga falo.Kaina a du e yake,hakan yasa na yi arba da wutsiyar farin maci kan capet sai wani motsi take.A hankali na soma aga idona har na sauke su kan fuskar Soorab,wutsiyar na ara kallo wacce ta kasance matsayin afafunsa,na tantance hakan ne da na rufe idona na tsakiyar goshi na dube shi da iya idona biyun.Na lumshe