Sashe 35
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gwiwa wurin kashe Guru ? Cikin ra in gubar da ke ratsa ta tace na gwammaci mutuwa da na sanar da ke! Tirrr da halinki ina ba in ciki da takaicin fitowa a tsatsonki.Ba in ruhinki da banzayen esprits in da kike yi wa bauta kun yi ka an da ku kawar da tambarin Siren a doran asar Gomo.Ki jira sai kin ce ni na fa a miki da sannu za mu mayar da asar nan tamu doli sai mun mulke ku Hhhh! aramar alhaki! Ke har tutiya kike da ke Siren ce ? Kar ki manta canzawa siffarki ta na hannuna sai in na yarda ne za ki koma kuma har abada ba zan baki wannan damar ba Ammy ta fa a tare da juya bindinta na Maciji ta bugi Soorabiyya da shi ta saki ara. ara ce wacce babu wani mutum normal da zai iya ji ballantana ta jawo hankalinsa,hatta ciwon da ta ji wa Soorabiyya sai matsafi ne kawai zai iya ganinsa. A wahalce Soorabiyya ta bar akin,sai a lokacin Ammy ta juyo idonta kaina a hankali kuma ta riki e ta dawo normal. Nafisa ta shigo akin hannunta ri e da kofin madara wacce ta kasance ta Soorab,shigowar ta yayi daidai da tashin Afnane Ammy ta saki murmushi tuni na gane shirinta ne. Nafisa ta bai wa arta madarar da ita kanta ba ta san guba ba ce,sai da ta shanye tasss sannan ta ora idonta kan Ammy ta na murmushi a zahiri .Amma a ba ini idonta tsiyayar da jini suke saboda da an cire wayar sai ramen kawai, Ammy mi na yi miki? Ki na ga za su tafi da ni zan bar iyaye ne shine Abin da Afnane ta fa a da ido. Ammy ta shafi kanta a zahiri ta ce ki kwanta ki huta my love zuwa an jima zan kai shopping amma a ba ini cewa ta yi ke ce ki ka cancanta na bayar,don iyayen ki za su iya haifar da wata Afnane ta je ta shige jikin mahaifiyarta ta ce ina son ki Mama Na kalle su sai suka bani tausayi,da sauri na fito na nufi akina ina bu atar aiwatar da wani aikin gaggawa cikin biyun nan ya kamata na taimaki guda. Sai da na rufe kowanne bango ta yadda wani ruhi ba zai samu damar shigo min ba kafin na jawo bokitina,ina son kai wa Daddy ziyara sai kuma na tuna ya ce min itaciyar nan da ya bani ta na maganin cutuka na tsinko a guda tare da jawo madubin tsafina na bi ta cikinsa tare da ulla akin Soorabiyya.A kwance na tarar da ita a gabanta duk wasu abubuwa nata ne na tsafi da take san ran za su warkar da ita amma shuru fatar jikinta sai ara rinewa take da dafin Maciji.Na ta e bakinta na matsa mata ruwan maganin,a hankali ta bu e idonta a sannu-sannu ba in cikinsu ya soma fita haka ma gangar jikinta. Muka sakar wa juna murmushi,na bata labarin komai abin da ya faru da muka je can gidan Boss .Muna cikin haka ne muka soma jin takun Ammy da alamu za ta shigo nan in ne,na kama Soorabiyya da mugun sauri muka bi ta cikin mirror muka dira a akina. Soorabiyya ba mu da sauran lokaci ha uri za ki yi ki koma can tushen ki,zan nuna miki hanya zuwa masarautar ku in kin je ki sanar da Abban ku komai abin da ke wakana, arfin power ka ai bai isa mu ya i Ammy ba na fahimci sunan ta na babbar matsafiya ne amma Boss amfani yake da ita akwai manufar da yake son cimma na fa i haka ina shafar aramin bokitina wanda ya riki a ya zama aton Teku ,da hannu na soma yi mata kwatance hanyoyin da za ta bi ta je can gidansu da ke asan ruwa. Wannan za ki shiga da kin zo daidai inda ke da aton tambarin Snake ki tsaya kawai za a zo a tafi da ke na yi maganar ina kallon ofar saboda yadda ake naushinta, Tsoro nake ji Sarah ban ta a rayuwa cik.... ban bari ba ta ida na tura ta cikin ruwan tare da shafar samansu komai ya dawo normal. Sarah! na ji muryar Ammy na kirana, na'am! na amsa, mi kike kika rufe ofa? Ina wasa ne Ammy jira gani nan na fa a tare da tashi na bu e mata,ta tsure ni da ido kafin ta ce Soorabiyya ba ta shigo nan ba? Na girgiza kai na ce a'a ki duba akinta Daga can nake Ki barta kawai ai doli za ta dawo tun da maganinta na hannun ki Haka ne! Zo mu je ba i sun fara zuwa haka na fito muka nufi akin da take tarbar ba i,kamar jiya haka suka dinga shigowa aya bayan aya har aka zo kan wannan matar ta jiya ta zo ita da awarta. Cak zuciyata ta daina bugawa,tamkar an ri e mini numfashi haka na ji .Ammy ta dube ni ta kuma dubi Suhaima tsananin kamar mu ai bai kai ace mini ita ce mahaifiyata ba. Ta yi baya za ta juya,da sauri na ce Mama... ta tsaya cak jikinta ya au kyarma kamar mazari ina shirin mi ewa ta yi saurin fita a guje, awarta ta take mata baya har zan bin bayansu Ammy ta ri e mini hannu gam ta na cewa kar ki fita ..... ```MRS SADAUKI *Book2* My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya ku in karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne . Babu bu atar sai kin bi ta,za mu san abin yi duk da tuni mijin nata ya arar da ita Ammy ta fa a ,haka muka ci gaba da tarbar ba in kafin mu fito mu je can cikin gida.Kafin mu rabu Ammy ta ce mini zan je na ziyarci Boss a akin sirri yadda muka yi da shi zan sanar da ke kai kawai na jinjina mata na zauna salon ina nazari kawai sai ga kukan Nafisa ya cika gidan,na ruga a guje na nufi akin sai na tarar da Afnane ta na ta zabura jini na yi mata zuba ta ofofin hancinta. Cak na tsaya ina kallon Ammy wacce ta zo a oyayyar siffa ta na zu e jinin Afnane,wacce na san tuni tata ta are mutuwa kawai za a jira.Tun ta na motsi har idonta suka tsaya cak, ta mutu! Nafisa ta furta na lumshe ido kawai ba tare da na motsa ba kamar wata zararra ta fita a guje kuma ta dawo ta na waige-waige kafin ta auki waya ta kira Nawaf.Babu jimawa ya zo shi da Nawas ,ko tambayar ina Ammy ba su yi ba suka auki Afnane don zuwa asibiti.Sai dai su na zuwa can aka tabbar musu da ta mutu suka dawo gida,Ammy kamar wata ta kirki haka ta fito cikin shiga mai kyau sai baza amshi take.Da ta samu labari ta fi kowa kuka,ni kuwa ido kawai na zuba ina kallon ta har sai da ta harare ni can ta ce je ki kira Soorab na mi afafuwana a sanyayye na isa akinsa.Bai nan sai motsin ruwa da nake ji a toilet,kai tsaye na je na shiga cikin bahon wanka na hango shi ya auki siffar Maciji.Da idonsa yayi min alama da na zo,ina shiga ruwan na zama Siren .Wata irin kulawa muka ba kanmu muka kasance da juna ta naturel siffarmu ba wai ta an adam ba,sai bayan mun fito ne nake ce masa Afnane... na sani! yayi saurin katse ni na zuba masa ido ya jinjina kai ya ce na ga duk abin da ya faru a mafarki ,amma Ammy sai ta san ta aika babban zunubi na cinye yarinyar da nake auna kayan takaici wai jikarta haka muka fita tare da shi. Tuni mutane sun cika gidan,Ammy ba a ma ganinta.Haka aka yi mata wanka aka kaita gidanta na gaskiya,yawaitar mutane ta sa na koma akina na rufe ko ina sannan na fiddo madubina ina yin wasu surkulle sai ga Daular su King Gandu ban yi sanarwar zan kawo ziyara ba hakan yasa ba su san da zuwan nawa ba.Ganin Soorabiyya na cikin oshin lafiya yasa na koma can wajen anty Sailuba na ci sa'a kuwa ta na tsaye gaban madubin saloon ta na gyara mayuka.Ta zabura kafin kuma ta ja ajiyar zuciya ta ce Haba Sarah sai ki sa zuciyata ta buga ai irin wannan bazata ko irin iskan nan da ya ta a tasowa wancan zuwan naki ba ki turo ba Na yi murmushi na ce anty ana ta aiki? Eh wallahi ya kike? Ina Hajiya? Hum! Ina dai muguwa za ki ce,duhun mine ne nake gani a goshin ki? na fa a hankali tashe . Ta shafi wurin ta ce kai babu komai A'a da matsala! Tabbas akwai wani mummunan abu da ke tunkaro ki sai da na kasa ganin mine ne ga shi kuma ni ma zan shiga bussy saboda muhimman aiki da zan aiwatar akan Mamana da na gani yau Wayyo kin ganta ashe? Kai na taya ki murna Anty ina shaida miki ki na cikin ha ari ke kuma sai fara'a kike abun ki,Mamana ma na cikin cakwakiya doli ni ce zan fitar da ita na yi furicin ina waigawa bayana saboda handle ofar da ake mur awa,da sauri na ce anty zan tafi ban san ranar da za mu sake ha uwa ba amma zan aje miki sa o kan dressing mirror inki a duk lokacin da kike cikin wata matsala a fuska za ki shafa ruwan maganin da zan aje miki da kin yi haka zan zo ina gama fa a na shafa madubin tare da mayar da shi ma'ajiyarsa daidai nan Soorab ya shigo.Sosai na yi mamaki yadda aka yi ya bu ofar duk uban matakan tsaron da na saka. Mine ne kike shirya wa? ya jefo min tambaya. Na ja ajiyar zuciya na ce Mamana! Yau na ganta ta na cikin matsala a daidai lokacin da zan bin bayanta kuma Ammy ta