← Book details Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 47

Sashe 15

Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki kwantar hankalin ki na yi miki al awari cikin satin nan ita da kanta za ta maido miki ku in ki Anty Sailuba ta shafi gefen fuskata ta ce na gode sosai daga nan ba ta sake cewa komai ba,ina jin bacci ya auke ta na tashi na sauka daga gadon. Kayana na bu e na auko madubina,na shafe shi da hannu ya kawo haske kamar lantarki na yi murmushi na ce ina son ganin Musty, Naser da kuma Azo kamar yaftawar ido suka bayyana a ciki duk murmushi auke da fuskokinsu sai dai ba a normal ba idonsu na ukun duk ya fito sa anin azu da na je ofishin su babu ita. Mi kike bu ata Siren? Musty ya tambaya,na yi murmushi na ce ina ne nan kuke? Mun zo wurin party ne ai sai da muka ce za mu zo mu auke ki amma kika Naser ya fa a ya na harare na,haka kawai nake jin wani abu na daban a tattare da shi. Ni kake harare? To yanzu ku zo ku tafi da ni na fa a cike da za uwa. Azo ya ce shi wannan madubin na hannun ki mine ne amfaninsa? Ki shaida masa inda kike son zuwa za kawo ki har nan Na waro ido kawai sai siffarsu ta canza haske ya fito,ta idon na sanar da shi ina son zuwa wurin su.Wani abu na soma ji kamar an zuba min ruwan sanyi zuuuu na ji na rabu biyu ,gangar jikina ta yi wani tashi sama tare da zuwa kan bed ta kwanta kusa da anty Sailuba.Yayin da kuma wata iri na ke tsaye,dariyar su ce ta maido ni daga duniyar mamaki,Musty ya ce au kin zata har da gangar jikin ki za ki zo nan in? Ai iya esprit in ki kawai zai zo Naser ya mi o min hannu ya ce abun mamaki ina saka hannuna cikin madubin na ji ya wuce tamkar na saka shi a ruwa.Hasken madubin ne ya ara yawaita da na ora afata ciki,kamar yadda ake bi ta ofa haka na shiga ta madubin na wuce sai gani a duniyar su Musty. Duniyar ce mai kamar wannan,zan iya cewa ma ta fi yi min da i fiye da normal duniya don ita ce ta fi dacewa da ni tun da ba normal mutum ba ce ni. Madubina bai gushe ba ya na tare da ni,don ta cikinsa zan koma gida.Ziyara muka fara yi ta asashen duniya,cikin abun da bai wuce minti talatin ba mune har Turai ga fararen mutane nan sai hadada suke. Ba a afa muke tafiya ba,hasalima tafin afarmu bai ta asa cikin iska ne muke yawo.Bayan sun gama nuna min duniya,sai muka dawo inda ake shagalin duk matsafa ne da Mayu daga mai kan kaza sai mai jikin doki,wasu kuma siffar mage amma irinsu Mayu ne suka fi aukar siffar.Sosai na dinga yi musu tambayoyi har na zo kan tambayar ya ake yi mutum ya ha a ruhinsa da na wata daba? Kamar za ka gani in dabbar ta ji ciwo to shi ma zai ji zafin a jikinsa? Protector ne! Ke ma da ace yarjejeniya kika yi da wani pacte ko loge za a baki shi.Shi in ya na wakiltar mutum ne,in wani abu zai same shi to protector in zai sanar da shi.Sannan zai dinga yin aiki ne kamar mutum duk abin da aka sa shi zai yi muddin kai ma ka na basa abin da yake so,yawancin su a na basu jini shine abincinsu.Kin ga Mayu ana basu adangare ko mage matsayin protector , arayi kuma za a basu era ko gafiya,matsafa masu son ku i maciji ko kuma zobe mai hoton maciji To ku mi yasa kuke da ido tsakiyar goshi? na tambaye su,suka kalli juna kafin Musty ya ci gaba da cewa an ce mai yawan tambaya shugaban gobe ne! Muna da ido aya ne saboda mu dinga ganin duk wanda ya zo da niyyar cutar mu ,sannan dodaninmu na ciki masu bamu ku Na waro ido na ce kuma kuka yarda aka saka muku shi ? To amma shi mi kuke basa matsayin abinci? in bani amsa suka yi duk yadda na so su sanar da ni,da na matsa musu sai cewa suka yi sai in na yi musu hanya sun ci galaba kan Bilal. Na ja ajiyar zuciya na ce ban so ku cutar da anty Sailuba ba don haka ba da na mi a muku Bilal Suka tur une fuska Azo ya ce to ai mu ita muke kwa ayi,kin ga har yanzu dodo bai samu sabon sperme na matar aure ba Mi yasa sai matar aure? Saboda tsafi ya fi arfi inda aka fi fatali da dokokin Allah Zan sake yin magana Naser ya ce ya kamata ki koma gida an kusa yin sallar asubah kar ki tsorata Antyn ki Ina son ku taya ni nemo wata mata ma da ta cuci anty Sailuba ta kwashe mata ku i ta hanyar bata ku in tsafi masu janye ku Sai da suka ci dariya son ransu,sannan azo ya ce ai kuwa muna son ganin matar nan,please tun da ba ki san sunanta ba cewa idonki su hasko mana matar ta madubinki Shawara mai kyau cewar Musty .Cike da warin gwiwa na haska madubin daidai fuskata,a sannu a hankali hasken idona ya soma zana hotonta har fito ra au kan madubin . Aiki mai kyau Sarah,kar ki yaftar ido yanzu kuma sai ki sa a binciko miki ita inda take ko bango duniya ne za mu ganta Naser ya fa a ya na mai kama hannuna wanda na ri e madubin, murmushi kan fuskata na aiwatar da abin da ya ce in kwatsam sai ga matar kwance ta na sharar bacci abun ta,gefenta kwalbar fanta ce da ragowar naman da ta ci. Azo ya ce alamu sun nuna ku in antynki an soma cin da i da su Na ce za ta amayo su yanzu nan sai na karkata wayar idona zuwa ga ledar naman asusuwan kazar na ce ku mi e tsaye ,har ragowar naman kai ma tashi,kwalbar fatan je ki daidai kanta ki buge ta Shewa da ihu su Musty suka soma yi lokacin da suka ga abin da ke faruwa don ba da baki nake magana ba,kumbutseee kwalbar ta buga kanta ta zabura ta tashi zaune ta na mai fasa ihu sai kuma ta yi tozali da squelette in kaza na nufar ta sai ta ara ru ewa ta nufi ofar fita duk da babu yaure a jiki haka na yi saurin dalla ido wurin ya inke ya zama irin jikin katanga. Musty uban mugunta ya ce ya kamata ki kai mata ziyara kawai ki je can,ki laka a mata shegen duka ki wace duk abubuwan mutane da ta sato Ban ce komai ba sai murmushi da na yi na nitse cikin madubin,ban bayyana ko ina ba sai cikin akinta.Ita ba ta ganina amma ni ina ganin ta,kafa arta na dafa na yi magana ta yadda za ta ji ke arauniya ta yi ihu ta juya bayanta na yace da dariya na ce wato kika bada kyautar 10k ta ha iye ku inmu ko? To yau za ki ji a jikin ki.Ko kin zata ke ce kawai kika san oyayyar duniya? sai na kwashe ta da mari har biyu. Ki yi ha uri na bari daga yau ki yafe min ta fa a cikin kuka. Wajen da take aje takalmi na je na auko aya irin mai tsinin nan na soma yi mata ran washi da shi ban barta ba har sai ta kusan mutuwa,a arshe na ce ina mai garga ar ki da gobe ki je ki mayar da ku in mai saloon in ba haka ba gobe gayyar Fatalwa zan yi miki mu cika gidan nan ina gama fa a na bi ta madubi na koma gida. Anty Sailuba na samu kai gare ni sai kiran sunana take ta na jijiga gangar jikina,ta mi ar da gangar jikin zaune amma abun mamaki sai ta yi luuuu ta fa i ta bugi kan gado tare da mirginawa asa. Na shiga uku na lalace,kar dai ace Luba ta kashe Sarah keeee? Bari na saki eran nan na huta ila.... ban bari ba ma ta kai arshen zancen na yi saurin mayar da esprit na a cikin gangar jikina. Tari na soma yi wanda ya jawo hankalin ta,haka ta tsure ni da ido ta na kallo. Haba Sarah saura iris ki saka zuciyata bugawa na yi tunanin Luba ce ma ta rama muguntar da muka yi mata Na sakar mata murmushi na ce Luba dai? Haba anty ai na fi arfinta don ba ki san wace ce ni ba shi yasa,in ba don na tsorata ki ba da na baki wani labari Ina jin ki wane labari ne? Ai ni yanzu babu abin da zai ban tsoro to mine ne a ban gani ba? Ku i masu cinye wasu ku i,mutum ya zama era ya na sata. Dabba ta yi magana a gabana ne kawai yayi saura Gobe matar da ta saci ku in ki za ta kawo miki ku in ki na fa a cike da yarda da kaina. Anty Sailuba ta saki baki ta ce wace gobe? Ai tuni an yi sallar asubah,ki ce kawai na yi wanka na wuce shago kar ta zo ba ta ba na nan Na ce Za ta jira ki sai kuma na sauka na fita daga akin,fitsari na yi na fito ina tunanin wai mi yasa Musulmi ke yin Sallah? Ni ban ma san ta amaimai wane addini nake yi ba Jikina na wanke kamar kullum sannan na yi shara na wanke kwanuka,ko da na shiga falo na tarar da Bilal a zaune kan kujera a tisa anty Sailuba gaba . Na ce ki bu e min akin na duba,don ta tabbatar min ke ce kike azabtar da ita Bilal ya fa a ,sai na fahimci inda zancen yake. Ba zan bu akina ba Bilal ,jiya ka ce na sace ma ku i ka yi min uban duka yanzu kuma ka ce na azabtar da matarka.To ta yaya ni da ba aljana ba sannan ba aki guda muka kwana ba? Bai ce komai ba ya tashi
Chapter 15 · 0% Book details