← Book details Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 47

Sashe 27

Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ce to Baba kafin ta kama hannunsa su soma tafiya ta na waiwaye na. Haka kawai na ji ina son sanin wace ce ita,bayansu na bi sai na ga sun shiga wata dan areriyar mota wacce hawanta sai manyan masu ku i irin su Ammy. Mi kike yi nan tsaye? muryar wani namiji ta katse mini tunani,na waigo na yi arba da shi na gane shi an ajinmu ne.Yaro ne mai kyau zai kai 23 zuwa 25 years haka.Ban kai ga basa amsar tambayarsa ba ya mi o min hannu sunana Marwan aramin matsafi mai burin zama shahararre Ban mi a masa nawa hannun ba na ce ni kuma Sarah Sarah! Suna mai kyau,amma da alamu ke ba uwa ce Ya aka yi ka san haka? Yanayin maganar ki,mu je lokacin cin abinci yayi ya fa a ya na nuna min wani angare inda na ga an ajinmu duk a zaune gaban wani dogon table.Ban musa ba na bi bayansa duk da ina tunanin zuwa gida ne,kamar ya karanci zuciyata sai cewa yayi sai dare ko mun tashi,makaranta ke da alhakin ciyar da mu ba iyayenmu ba Amma don mi? Haka tsarin yake,da sannu za ki fahimta ya fa a ya na sakar min murmushi ashe nan ne fa muninsa yake don bakinsa irin ha oran Zomo ne da shi wa anda ba su bayyana sai yayin dariya ko murmushin,na fahimci haka ne saboda tun azu da yake magana ban ga sun fito ba. Kan table in muka zauna kusa da juna,mai zuba abincin wata tsohuwa ce mai hujen hanci ta saka atuwar barima.Abu guda na lura abincin kowa da kalar nasa,ta zuba min a plate in gabana shi ma haka ta na gusawa na ce amma ya aka yi abincin ya fi kala ashirin kowa da nasa? Saboda kowannen mu da kalar abincin da protector insa ke ci ya bani amsa wacce ta sa na urewa abincin gabansa da ido,salade ne da karas an yi masa ha i da wasu ganye da ban san na mine ne ba. Zomo ne protector inka? na tambaye shi kamar mai jin tsoro,ya ago ya na dariya ya ce ya aka yi kika sani? da idona na yi masa nuni da bakinsa,sai ya gimtse dariyar ya ce oran Zomo ! Ke kuma fa wane ne protector inki? Naman da ke gabana na soma ci sai na ji anonsa ba irin wanda na saba ji ba ne wannan ya fi da i da gar i,na ce ka cinka da kan ka ai ga abincina nan Ya ce ba zan iya ganewa ba don protector masu cin nama yawa gare su,akwai Zaki,Damusa,Kifi,Maciji da sauran su Dukkansu protector ina ne na basa amsa ya ce tun da ba za ki fa a ba shikenan Abincin muka mayar da hankali wurin ci har sai muka kammala sai kuma aka fara raba mana lemu a irin kofinan nan da malaminmu ya bamu ruwan inibi.Adadin yadda ka sha iya adadin makin arfin ikon da zai aru.Wata irin power nake ji ta na bijiro min kamar na tashi sama,abubuwan da ido bai iya ganinsu tsabar aranta ni manya-manyan nake ganinsu irin su cinaka, uda,sauro da sauran su. A yanzu kuwa duk aliban da ke gabana zan iya ganin oyayyar siffarsu, dayawa daga cikinsu su na auke da manyan fuka-fuki biyu a bayansu,wasu kan Zakara,wasu kuma fuskar zaki. Waooo Siren ! na ji amon muryoyinsu,ni da na shagala da kallonsu sai na ji su na ambaton jinsina.Da sauri na kalli kaina sai na ga ashe tuni siffata ta rabi kifi rabi mutum ta bayyana. Siren ce ke! Amma na yi matu ar mamaki a tarihin duniya ke ce ka ai Siren in da ta ta a shigowa makarantar nan Marwan ya fa a ya na mai kai hannu ya shafi bindina da yake ta faman motsi. Yadda ake kallona in ne duk sai na ji na takura,so nake na bar wurin amma Marwan ya hana ni ya ce doli ne a kalle ki saboda duk fa in nan ke ce kawai a ba ki da an uwa a irin siffa Eh yayi gaskiya ni ka ai ce Siren . alibai a shiga aji cewar wani Aku da ya zo ya bubuga fukafukin shi,na aga kai ina kallonsa na ce shi kuma wannan wane ne? Mai kula da alibai shi ke kawo duk wani rahoto a makarantar nan ,sannan shi ne an aike Marwan ya bani amsa tare da mi e wa kan afafunsa irin na Zomo .Kowa sai tashi yake amma banda ni saboda ban san ya za a yi na taka da bindin kifi ba .Tuni sauran alibai sun fahimci haka sai wasu suka fara yi min dariya , in ba jaraba ba ina aka ta a ganin Kifi kan doron asa? Gwara ki koma ruwa yarinya can ne duniyar ku wata hawainiya ta fa a yayin da sauran suka saka dariya . Maganar ce ta yi min zafi zuciyata ta kawo wuya ban san lokacin da na yi wata irin ara ba,ji kake gaggga-gaggga cida ta soma yayin da gari ya soma rinewa ya na aukar yanayin hadari ba irin tsawa da wal iya suka ci gaba da wanzuwa . Hankalin kowa ya tashi musamman masu siffar mage da ba su son ruwa sai dai tuni lokaci ya zo a ure ballantana su gudu.Tuni ruwan suka fara sauka makarantar na cika da ruwa tan am ita mai siffar hawainiya ta cewa an uwanta mu haye bishiya ba ta rufe baki ba suka yi tsalle suka bishiyar bedi.Ido na soma juyawa ina ka a kaf bishiyoyin filin makarantar,ihu suka fara su na ri e reshe amma tsabar yadda nake girgiza shi yasa suka yi can sama tare da fa owa cikin ruwan can allll. Shugaban makarantar ne ya fito da sauri cikin aga murya yake cewa wane ne ya haddasa hadarin nan ana tsaka da karatu? babu wanda ya basa amsa idonsa suka yi masa tozali da ni, Sarah yi ha uri ba ko da yaushe ake aukar mataki ba ya fa a ,kamar ba zan auki maganar tasa ba sai kuma na yi wa ruwan magana da ido suka fara shigewa ashin asa yayin da kuma gari ya washe yayi haske ko alamar hadari babu. Ni da nake tunanin ya za a yi na yi tafiya da bindin kifi sai ga shi na riki e na koma mutum,a haka muka je muka shiga aji.Duk sauran abokan karatu sun shiga hankalinsu,kusa da Marwan na zauna ba a auki lokaci ba malama ta shigo wacce ba kowa ba ce illa Ammy. Da ido na tsure ta yau ko ka an ba ta oye siffarta ba,da hannunta na kaza ta rubuta sunanta a allo domin gabatar da kanta. Madam Gandu Tambara na maimaita sunan sai na ga ta ago kai ta kalle ni,sai ta sakar min murmushi kafin ta soma cours inta. Na san an yi muku bayani akan kofin tsafi,to zan kawo muku wani arin bayani game da wannan kofin.Ta hanyar shi ka iya banbance abubuwa da dama ciki kuwa har da ruhi da Fatalwa, kowannen ku ya kamata ya mallaki nas don ya na da kyau ku kasance da shi a duk inda za ku je musamman yanzu da kuka shiga wani level na rayuwa .A duk inda za ku je za a iya gane asalinki muddin kuka ha u da wani irin ku,kuma haka za ku gane shi.Chapter inmu na farko za mu yi shi ne akan MAITAR IDO wa zai fa a mana mi take nufi? ta yi tambayar ta na kallonmu wato dukkan an ajin kafin ta sauke dubanta gare ni ta ce Sarah mice ce MAITAR IDO. Sai da na yi an jim kafin na mi e tsaye duk idon kowa ya dawo kaina,dakyar na bu e baki na ce MAITAR IDO aba ce wacce marar kyau wadda duk aka yi imani cewa ta na wanzuwa a kallo aya, kushewa ko yabo daga wani mutum zuwa wani zai iya samar da ikon jefa la'ana ko mummunan sa'a akan an uwansa Madam ta jinjina kai ta ce ko za ki fa a mana ta wace hanya ce mutum zai gane in ya na auke da MAITAR IDO? Shiru na an yi kafin na ce amsar ita ce a'a.Dayan mutane su na auke da MAITAR IDO ko kuma ta baka ba tare da su kansu sun sa su na da ita ba.Sai dai mutanen da ke zagaye da su ne za su iya fahimtar haka,misalin kamar mutum ya fa i abu marar kyau akan an uwansa Allah sa takalmanki ya angwale ki fa i ,sai kwatsam kuma aga abun ya tabbata in .Ko kuma mutum ya kalli wani abu da ya basa sha'awa ko akasin haka sai abun ya lalace misali furanni za su iya bushewa,in mutum ne kuma zai iya fa uwa rashin lafiya ina gama amsa wa zan zauna wa sai kuma ta ara jefo min wata tambayar, In kuma mutum na son sanin shin an jefe shi da evil eye wato da Ingilishi,ko kuma mauvais il da faraansanci ta ya zai gane? Cikin osawa da tambayoyin na daidaita tsayuwata ina sauraren zuciyata da ta can ne nake samun amsar bayarwa don gano in an jefa ma MAITAR IDO ko kuma ka ta ile ta da kanka,da farko mutum zai binciki kansa,shin ya na fama matsananciyar gajiya ? Duk jiki yayi ma ciwo alhalin ba ka yi aikin komai ba,ko kuwa ciwon kai mai shegen naci? Shin ka na fama da ciwon irji? Ka ji kamar an danne ma irji ko kuma kamar wani mai ciwon olser? In dukkan wannan sun bayyana may be You victime of the evil eye ! Madam ta fara ta a mini sannan an aji,hakan kuma ba aramin da i yayi min ba sai na i ma zauna wa ina jiran wata tambayar.Sai ta yi murmushi ta mini alama da hannu na zauna,Marwan yayi asa da murya ya ce duk ya aka yi kika san wannan? Ko ke ma mayyar ce? ban basa amsa ba sai bangazar shi da na yi ina hararensa. Abin da na fa a ne Madam ta ara bu e shi ta yadda kowa zai fi fahimta inda a arshe ta ara da cewa a wurin
Chapter 27 · 0% Book details