Sashe 42
Maitar Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mota ta ka e ta tsabar yadda ta lula duniyar tunani,ta na isa gida ta ci karo da Laure ta fito daga wankan da take na ruwan zafi.Wani tausayinta ne ya kama ta sai ta ji kamar ta sanar da ita gaskiya,amma ta fasa ta je ta shige akinta.Kuka ta yi mai isarta har kanta na ciwo,bacci wahala ya auke ta nan ta soma yin mafarki ga ta kan gadon asibiti za ta haihuwa sai jini ke yi mata zuba amma yaron ya i fitowa.Can kuma kukan jarirai ya cika akin kafin ta soma jin yaron cikinta na magana Mama! Mama ki cece ni kar ki bari su kashe ni Mamaaaa wata irin zabura Sailuba ta yi a firgice ta farka.Wanka ta je ta ha i da alwala ta zo ta fara jera salloli da ita kanta ba ta san adadin su ba,tabbas kwana biyu ta yi sakaci da addininta musamman sallar Asar wacce ke iske ta cikin aikin salon can dama Sarah ce ke taya ta.Haka ta ci gaba da sa ar zuci har aka kira sallar azahar ta mi e ta yi,abinci ma kasa ci ta yi har Hajiya ta aiko mata da kwa on zogale amma ta i ci. Bayan sallar la'asar Bilal ya aiko wani yaro ya kawo mata nama sai ta ora girki,kamar wata mayya haka ta ji yawunta na tsinkewa kawai nama take son ci.Tukunyar ta bu e ta soma tsamo shi ta na ci amma sam babu ano ba ta jin da insa,tsoro ne ya kamata jin bakinta salaf kamar ba nama take ci ba.Wato ta fahimci naman mutum suke son a doli ta dinga ci,jikinta na rawa ta mi e ta koma aki.Kwalabar da Sarah ta bata ta zo auka amma sam ba ta ganta kan dressing mirror in ba,kamar mahaukaciya haka ta shiga birkice kayan akin ta na nema har ta fidda rai sai kuma ta ganta.Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta na mai bu e kwalbar,wani irin ruwa ne masu masifar haske a ciki masu kamar madubi ta kai hannu ta dangwalo ta soma shafawa a fuskarta.... ```MRS SADAUKI *Book2* My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya ku in karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne . Alkur'anin na tsura wa ido sai na ga wani irin haske na rahama ya lulu e shi wanda kuma hasken ba aramin cutar da wani sashen ruhina zai yi ba. Mine ne wai? Soorab ya tambaya tare da tashi ya nufo ni,na yi saurin ja da baya amma duk da haka ya cabko na saki ara ina dafe gefen kafa ata daidai inda littafin ya ta a ni. Idonsa ya tsura min ko yaftawa bai yi kafin ya ce wane ne kai? shuru dai ban ce komai ba don ban ma fahimtar abin da yake cewa saboda kusa da muka yi sosai ga Alkur'anin har yanzu da hannunsa ya i aje shi. Sarah yaushe kika fara mu'amala da mugayen esprits ? Soorab don Allah ka aje Alkur'anin nan ya na cutar da ni ji nake kamar wuta na ona ni A'a ba ke ba ce Sarah,ba in ruhin jikin ki ne ke cutuwa ya na son wasa da hankalin ki ne ya na gama fa a yasa hannunsa ya matse goshina, ulll! Idona na tsakiya ya bu e taram Soorab yayi murmushi ya ce wato ki ce yarjejeniya kika yi da uwar gijiyar da Ammy ke yi wa tsafi,kin zata haka za ta baki power kan banza? Cutar da ke za ta yi sai kuma ya soma yin karatu har ban san lokacin da na zube gwiwaina a asa ba saboda tsabar wahala. Motsi na soma ji a walwa ta tamkar wani abu na yawo,eh kuma hakan ne dodo ne a ciki wanda yake bani duk wasu bayanai da suka kasance a oye .Idon tsakiyar goshina ne ya soma ara girma ,maciji ne ya fito a galabaice fitowarsa ta yi daidai da fa owar idon a asa shi ma ya soma motsi. Na yi baya a wahalce ina fitar da numfashi,Soorab bai gushe da karanta ayoyin Alkur'ani masu girma ba .Irin yadda macijin da idon ke juyin ra i da azaba za ka auka mutane ne har wani gurnani suke,idon ne ya fara tarwatsewa ya baje macijin kuwa sai da aka yi da gaske shi ma ya one ya zama haya Soorab ya ha e rai ya ce ina kika samu wannan tarkacen? Ba ki san in kika ha a power mai tsarki da wacce take ta tsafi ba sannu a hankali za ta gur ata taki ba ne? Shi yasa kika koma mai tsoro ashe ba kamar can farko da kike da tsiwa ba.Zo nan kika wani ure ni da idon ki na kifi Na turo baki tare da isa wurinsa,hannuna ya kama muka shiga toilet bayan yayi addu'a. Kar ki wani canza min siffar ki zuwa Siren ,wankan tsarki za ki yi na shiga musulunci zan koya miki karatu kuma zancen da Ammy ke cewa za ta taimaki mahaifiyarki ki sani arya take so take ta arasa aikin da shi Mr Shakal ya soma sai da yasa na auki niyyar wankan kafin ya taimaka min na yi ,sannan ya nuna min yadda zan yi alwala. Muna fitowa ya fiddo wata doguwar riga ya bani na saka ya fesa min turare,sannan ya ja mu sallah bayan mun gama ne ya auko Alkur'ani ya ora kan cinyata.Jikina ne ya au kyarma yayi shuru ya na nazarina,ni kuwa ido na zuba masa. Sarah tun ki na arama aka cutar da ke ashe sai kuma ya mi e ya auko wata kwalba zuma ce a ciki haka ya bani na sha sosai sai na ji cikina na yi min ciwo .Jikinsa na shige ina matsar walla ya ce zan fitar miki da duk wani dattin power da aka baki ta tsafi,ruhin ki zai dawo tsarkake ta yadda za mu ya i duk wani gur atacen ruhi na mugunta.Sarah abubuwan da Kaka Anaba ta baki duk don ki zama MATSAFIYA (MRS SADAUKI) ne su ne suka disashe hasken MAITAR IDOnki ba don haka ba ina ma Ammy har za ta yi gigin auko ki ta kawo ki gidanta? Kenan ina da power sosai? Eh sosai in nan ta yadda za ki dinga hani ga duk wani esprits ke ce za ki juya shi yadda kike so ya bani amsa.Na aga kai na kalle shi na ce ka na nufin zan juya Ammy? ya gya a kai ya ce sosai ma bakina na ora kan nasa,mun shiga wata duniya muka tsinkayo muryar Ammy na faman kiran sunanmu. #Province orientale Yadda Bilal ya auke mata wuta duk wunin yau bai kira ta ba,sannan da ya dawo da dare dakyar ya amsa gaisuwar ta girkin ma in ci yayi a arshe ya bar mata gidan .Cike da damuwa ta yi ta zaman jiransa amma bai zo ba,duk uwar yunwar da take ji haka ta samu wuri ta kwanta.Kamar jira ake sai ga ta luntsum a duniyar mafarki,irin mafarkin da ta yi a ranar da Laure ta haihu ga su nan ita da wasu mata wa anda ba ta sani sai Bibalo kawai.Duk kowacce sai jinjina mata take dangane da kyautar da ta bai wa group insu na matsafa wato kyautar an biyun Laure.Wata atuwar tukunya ce saman wuta ,tsawon lokaci ana dafuwa kafin a soma zubawa mutane a ranar nan ma an zubawa Sailuba ta ci sannan kuma ta yi rawa kamar sauran.Yanzu ma ta na shigowa inda ake taron duk suka tarbe ta,Bibalo ta rungume ta tana cewa na zata ba za ki zo ba,ya ne Bilal in ya yarda? Sailuba ta girgiza kai ta ce a'a fushi ma yake da ni Bibalo ta ja ta izuwa wani wuri kafin ta tsinko wani an itaciya ba irin da shi ta ce ungo wannan lokacin da za ki yi masa magana ki saka shi a baki sannan ki sanar da shi to zai yarda Kin tabbata? Sosai zo mu je yau ma mun yi wata sabuwar ba uwa a cikin group inmu haka Sailuba ta bi bayan Bibalo har suka isa wurin tukunyar inda ake raba musu abinci.Su ma zuba musu aka yi Sailuba ta soma ci a yunwace ta na cewa girkin yayi da i sosai dama yunwa nake ji Bibalo ta ce dama ai ni ban cin abincin dare don kawai na more in ba ki oshi ba ki je a ara miki Sailuba ta mi e ta kai wani tsohon kwano aka aro mata ta zauna ta na shirin ci kenan ta ji muryar Bilal .A firgici ta farka ta na kallonsa,shi ma ido ya zuba mata kafin ya ce mafarkin mine ne kike? Shuru ta yi ba ta basa amsa ba,ya furzar da huci ya ce mu je ki ci abinci da dukkan alamu da yunwa kika kwanta shi yasa kike mafarkinsa Shuru Sailuba ta yi ta na tunanin mafarkin da ta yi,tabbas da yunwa ta kwanta amma yanzu sam ba ta jin ta. Ban jin yunwa ta fa a ,da mugun sauri Bilal ya ja baya ya na cewa Sailuba mi kika ci haka arni ke fita daga bakin ki Wani haushi ne ya rufe ta,ta na shirin yin magana ta ji wani abu a cikin hannunta ta na bu e wa sai ta ga abin da Bibalo ta bata ne a mafarki don sakalci kawai ta jefa shi baki tare da cewa Bilal gobe zan fara zuwa taron group in mu To Allah ya kai mu goben sai ki je ya bata amsa fuskarsa sam babu wani annuri ga wata damuwa shimfi e malemale. Sailuba ta lumshe ido ta na son yin tunanin al'amarin amma tamkar wacce aka juyewa kwanya ta kasa tunanin ballantana ta ga aibun abin da take yi.Haka ta kwanta cikin zullumi,ta na jin Bilal na shafarta amma ta yi biris da shi. Washegari Bayan ta gama dukkan ayyukan da take ta yi wanka ta shirya tare da kiran Bibalo ta shaida mata komai.Babu jimawa si ga Bibalon ta zo har ofar gidansu da mota,haka