Sashe 85
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
馃槀Zo ka ga Ayam ta yi sabon uba, tun yanzu yake ganin tab'ara, gashi shi ma mutum ne mai barkwanci sosai da kuma son d'an wanda kake so, hakan yasa yake biye mata a waya su sha hira har da tsare tsaren bikinsu suke, wata rana kuma har ya dinga tsokanarta da cewa yaushe za ta haihu wai? Ko tana so tai ta ganinshi a tuzuru ne ? Haihuwarta ta masa shamaki d zama ango.
*Sati d'aya* cir ta kwashe tana zubar da wannan ruwan zak'i, a ranar da suka tsaya tana murna bata jin komai yanzu zata shirya ta tafi turakar mijinta, sai dai ina nak'uda ce gangariya ta sakota a gaba, da gaggawa Kossam da jakadiya da likitarsu mace suka rufu a kanta, cikin ikon Allaah saida ta kwashe awa uku tana nak'uda kafin Allah ya amince d'anta ya sanyo kai zuwa duniya.
Masha Allah masarautun biyu babu wanda bai shaida an yi sabon magaji ba, sai gashi hatta da gwamnati ta san da haihuwar Ayam saboda ita ake jira ta haihu dama sannan shugaban k'asar ya angwace, tunda aka dinga ganin hoton yaron akan bpnshi na WhatsApp da Instagram da sauransu yan jaridu suka bibiyi labarin, daga nan suka shiga yayatawa su ma suna fatan alkairi.
A satin nan d'aya da ya gabata haka Juman data zo take gyara yarta take mata wanka na musamman, saida Ayam ta ji a jikinta a iya hakama aka tsaya taji dad'in jikinta kuma zata birge mai gidanta.
Ranar suna an ci an sha an tara bak'i bila adadi, anyi murna sosai da shagalin wannan rana kafin daga bisani yaro ya ci sunan *Abdul Waheed*, yaro mai shiga rai wanda yayi kama da Musail, hakan yasa yayi kyau gashi b'ul bul kamar ba d'an wata bakwai ba.
*Bayan wata takwas*
Zaune take a kan kujerar dake d'akin tana wayarta, yar dariya tayi a nutse tace "Abba na, gaskiya idan Mah ta haihu sai na biku har can, kun wani tafiyarku Atlanta kunyi zamanku."
Dariya yayi shi ma yace "Karki damu 'yata ta kaina, ai jirgi na tanada da zai d'auko min ke da kuma abokina (Abdul Waheed)."
Dariyar jin dad'i tayi tace "Yawwa Abbana, kuma ka ga..."
Kafin ta kai k'arshe aka bud'o k'ofar d'akin na ta, sanin ko waye yasa tace "Abba zan sake kira ka bani Mah, yanzu gaba d'aya shareni take bata son muna magana."
Dariya yayi shi ma yace "Kunya take ji saboda tana da ciki."
Murmushi tayi tare da aje wayar ta juyo ta kalli mai shigowar, jallabiya ce jikinshi bak'a da hula a kan shi, sai Abdul Waheed dake d'auke a kafad'arshi cikin kayanshi na kanti masu kyau, tubarkallah ba zaka ce d'an wata bakwai ba ne, a haka ma dan sanda zai yi hak'ori yayi amai da zaho ne duk suka ramar da shi, amma yanzu har ya maido jikinshi gashi har ya fara tatata.
Yana zuwa d'oro mata shi yayi a k'afafu ya kai hannunshi cikin rigarta ya ciro nononta, yaron na gani kam yayi ram da shi ya fara tsutsa, rufe ido tayi tana jin zafin tsutsar da yake saboda nonuwan sun cika mak'il sai zuba suke.
Zaune yayi daf da ita a hannun kujerar ya k'urawa yaron ido dake tsutsar nonon idonshi rufe, kallonta yayi yace "Uwar yaron nan baki da tausayi wani lokacin, tun safe da kika kai min yaron nan ban kuma ganinki ba, ke wai ba kya tunaninshi ne?"
Turo baki tayi tace "To ai ina so ne ya ga yanda kake gudanar da mulkinka dan yayi koyi da kai."
A hassale yace "Sai kuma na ce miki ina buk'atar haka ni? Ko ya koya ai kya bari har yayi wayo ko?"
Marairaicewa tayi tace "Shikenan ka yi ta min fad'a saboda na yi abinda ya dace, ai dai ranar da aka nad'aka mulkin nan kayi alk'awarin ba zaka hassala a kai na ba, amma shi ne...har da min tsawa yanzu."
Hawayen k'arya ta fara sharewa hakan yasa ya jawo kanta a k'irjinshi yana fad'in" Shikenan to yi hak'uri, gani nayi yanzu ba kya kula wannan yaron, jiya ma fa Mah ta fad'a min wuni yayi wurinta bai sha nono ba, me yasa zaki k'i bashi abincinshi yasha ya k'oshi?"
D'aga kanta tayi ta kalleshi sai ta mak'ale masa ido d'aya, da alamar raha yace" Akwai magana kenan?"
D'aga gira tayi alamar e, jinjina kai yayi yace" To gama bashi yasha sai muje ki ga wani abun mamaki, amma tukuici na shine ki fad'a min me ke faruwa."
Jinjina kai tayi tace" Na yarda."
*Bayan minti arba'in*
Hannayenta take ta lalubawa kamar makauniya saboda rufe mata ido da yayi da wani farin k'yalle, a hankali ya kwance mata d'aurin na fuska, a hankali ta fara bud'a idonta har ta saukesu fes a kan wani ni'iltaccen lambu, bayan korayen itatuwan data sauke idonta babbar zakanyar nan ce ta biyu ta zuba idonta a kan ta, wani farin ciki ne ya lullub'eta har ta furta "Wow!"
Bud'a ido tayi sosai tana kallon gurin, a b'angarenta ne ya killace wani gurin aka nomashi da shuke shuke irin na jeji, sannan aka zuba nau'in dabbobi, zakanya, biri, barewa, rak'umin daji, dorina, aku, d'awisu da sauransu, nau'in tsintsaye kala kala masu kyawun gaske.
Juyowa tayi ta kalleshi tace "Yallab'ai..."
Juyawa tayi ta kalli zakanyar nan tace "A ina ka samota?"
Dariya kawai yake saboda ganin farin cikin da take, rumgumeshi tayi sosai ta sumbaci wuyanshi tace "Nagode sosai mijina, ina alfahari da kai."
Cikin kunne ya rad'a mata "A bani tukuicina."
D'agowa tayi daga jkinshi suna kallon juna, hannunshi na dama ta kama a hankali har ta d'ora a kan mararta, sannan ta kalli k'wayar idonsa tace "Abdul Waheed, zai samu k'ane ko k'anwa."
Da mamaki ya kalleta yace "Da gaske? Kina nufin ciki ne da ke? Amma..."
Dariya ce ta kubce masa ya kalli cikin na ta ya kuma kallonta yace "Amma kuma shi ne kike farin ciki? Duk da kinsan Abdul Waheed bai ko shekara ba, sannan kin sha wahala wajen haihuwarsa."
Langab'e kai tayi tace "To me ye a ciki? Ba na ka bane? Wahalarka ce ? Zan iya mijina, zan iya da yardar Allah, ko da shi ma ina haihuwarsa zan sake d'aukar wani, na yi maka alk'awarin ba zan gaza ba ko da bautarka ce zata kasheni."
Wata wawuyar rumguma ya mata tare da bata wani zazzafan sumba mai haukata k'walwa da gaggar jiki... 馃グ馃
*Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka nuna min k'arshen littafin nan lafiya, kamar jiya ne aka fara gashi yau an kawo k'arshen sa da amincewarka, Allah nagode maka, Allah ka k'ara mana lafiya da aron rai.*
_Hak'ik'a VIP grps kun nuna min k'auna, kun bi ni a novel d'ina na kyauta sannan kuka bi ni a novel d'ina na kud'i, kun min hallaci kuma kun nuna ku d'in masoya ne ba masoyan baka ba, hakan yasa a kullum nake kiranku da *yan amana*, ku d'in na daban ne a zuciyar Samira, Allah ya bar k'auna a tsakaninmu. Yanzu ma ga wani sabo nan na kud'i, na san zaku fara mamaki dalilin da yasa na ke son fara na kud'i? Dailin shi ne ina jin dad'in ganin wanda suke ikrarin suna tare da ni na kuma ga sun saka kud'insu sun siya saboda ni, hakan kuma na zama alkairi a gare ni, ina mai muku albishir da labarin *MALLAKINA CE* zai baku mamaki da sakaku nishad'i, dan na tabbatar zai fi *JIHADI* citta haka kuma zai fi *MATAR MUTUM* zak'i da saka walwala, abinda na ke so daku kawai shi ne ku biya kud'inku ku samu labarin, sannan alfarmar da zaku min ta biyu ita xe ku tayani tallata labarin dan k'ara samun masoyan asali._
*D'AND'ANO*
A nutse kamar yanda ma fi aksarin masu sunan *Abbakar Sadiq* suke kasancewa ya shigo falon da sallama, cikin haiba da k'asaita ya dunfareta, tunda ta ji bai jira an amsa sallamar ba, bai kuma kalli kowa dake falon ba sai ita ya tabbatar mata da wata a k'asa, amma sai ta nutsu tana kallon dogayen k'afafunshi masu d'auke da zara zaren yatsu har saida yayi daf da ita ya rage kad'an yayi saura k'afarshi ta tab'a k'afarta da ke mik'e.
Da wani irin sauri ta tank'washe k'afafunta ta ja baya sannan ta mik'e tare da sakin littafinta dake kan cinyarta tana karatu, rusunawa yayi tare da kai hannu da niyyar cakumar gashinta data bari a waje ba d'an kwali, sai muryar mahaifinshi wanda tun shigowarshi yana shirin amsa sallamarshi amma ya ga ba wannan ne a gabanshi ba sai ya dakata yana kallo ya ga me zai yi.
A razane yace "Kai! Lafiyarka k'alau kuwa?"
Da sauri ya janye hannunshi tare da d'agowa ya juya, sam bai yi tsammanin mahaifin na d'akin ba, ashe ba shi kad'ai ba ma har da mahaifiyarshi na zaune da kuma Goggon shi, cikin rashin jin dad'i ya dawo baya ya tsaya kusa da mahaifin na shi dake zaune kan kujera, kakkafeshi da ido Abba yayi yace "Da me ka yi niyyar yi Sadiq?"
Murmushi ya saki ya girgiza kai, tsaf Umma dake kallonshi ta fahimci da matsala, wato murmushin nan ne mai kama da kuka da yake yi idan ranshi ya b'ace, shi kuma gashi miskilin tsiya bai cika nuna damuwarshi ba, mutum ne mai koyi da fad'ar Manzon Allah (S.A.W), yana had'e fushinshi ko da kuwa zai iya d'aukar mataki, Abba kuma da bai fahimta ba d'orawa yayi da "Ban yarda da wannan girgiza kan ba, za ka fad'a min ko kuwa?"
D'aga kanshi yayi ya kalli mahaifin na shi, ba tare daya d'auke murmushin nan a fuskarshi ba yana kallon fuskarshi a ladabce yace "Abba, yarinyar can nake so na koyawa hankali, ina so na ji me ye tsakani na da ita da ke b'ata min suna? Me take nufi da ni da take min haka? Me kuma take nufi da abinda ta fad'a?"
Da sauri Abba ya kalli *Sajeeda* dake tsaye da rigarta t-chirt da zanen atamfa, ta d'auki littafinta ta ri'ke tana kallonsu ita ma sai zare ido take.
Mahaifiyarta da tun da ta ga ta wuntsila ta tashi tasan bata da gaskiya, harara ta cilla mata tace" Me kika masa?"