Sashe 35
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi yayi ya rik'o hannunta cikin na shi, fad'uwar da gabanta yayi ne yasa ta saurin saka idonta akan fuskarshi, kakkausan kallo ne ta masa dake nuni da me hakan ke nufi? D'an motsa hannunta tayi alamar tana so ta k'wace, amma sai ta ji kam ya rik'eta sosai, jan ta yayi zuwa bakin gadon suka zauna, sam ta k'i d'auke idonta a kan fuskarshi yayin da shi kuma ya kasa kallonta saboda kallon da take masa, idonshi na kallon cinyoyinta duk da cikin riga suke ya shiga fad'in "Gimbiyata, ina so ne na fad'a miki wani abu, sai dai ina jin tsoro."
Mutsu-mutsu ta dinga yi da hannunta saida ta k'wace kafin ta d'an kawar da kan ta tace "Ina jinka yallab'ai, fad'a min ko menene."
Gyara zamanshi yayi ta hanyar matse mata wuri, da sauri ta ja baya ta sake jefa masa kallon bansan iskanci tare da yatsina fuska tace "A'a yallab'ai, wai me ye hakane?"
Fuskarshi d'auke da murmushi yace "Kina ji ko? Ban san ko wani ya fad'a miki tarihinki ba..."
Da sauri ta jinjina kao tana sake matsawa baya tace "E e, an fad'a min, amma ban yarda ba, watak'ila kai zaka fad'a min gaskiya."
Tsurawa fuskarta ido yayi yace "Kinsan komai game da ahalinki kenan?"
Girgiza kai tayi tace "Ta ya zan san komai a game da su? Bayan ko kamanninsu ban sani ba."
A nutse ya sake kallonta yace "Kinsan bayanin b'atanki?"
A shashance tace "E, yallab'ai Umad ne ya fad'a min wai mahaifiyata ce ta bayar da ni dan ta kareni."
Da alamar tambaya a fuskarshi yace "Umad? Dama kun yi magana da shi ne?"
Tuna kalaman Umad da tayi cewa saboda tsaro yake nesa nesa da ita yasa ta saurin fad'in "A'a ai d'azu ne da ka ce mu jira a waje, mun fara maganar sai kuma na nuna masa ban fahimci komai ba kawai."
Jinkina kai yayi alamar gamsuwa yace "Kin tabbatar ya fad'a miki mahaifiyarki ta ceci rayuwarki daga masu son cutar dake ne?"
A gatsine tace "Haka ya fad'a, amma ni ina ganin me ye dalilin da zai sa a rabu da ni tun jinjira? Shin masu son cutar da ni d'in suna tare da ni ne a lokacin da take ganin rayuwa a cikinsu zai sa ni cikin had'ari?"
"Tabbas." Ya fad'a yana kallonta, da mamaki ita ma ta kalleshi tace "Kamar ya?"
Fuskantarta yayi da kyau yace "Gimbiya Zafeera, a lokacin masu son kasheki dayawa ne, saidai wanda ya fi su had'ari kuma babban cikinsu shi ne, sarki Musail, wato *mahaifinki*."
Irin kallon nan na galala ta masa kamar wacce bata hayyacinta, duk da labarin sabin iyayenta ba wai ta yarda ba ne, amma dai sai ta ji abinda ya alak'anta mahaifinta da shi ya mata ciwo yana kuma neman zautar da ita, zunbur ta mik'e tsaye tace" No! No! No... No...Hakan ba zai faru ba."
Cikin d'aga murya tana nunashi da yatsa tace" Yallab'ai ku gaggauta dakatar da labarin k'anzan kuregen nan na ku, kuna neman ku haukata da wannan banzayen labaran, kun manta ni d'in yarinya ce? Shekaru na ba zasu d'auki wannan k'arairayin na ku ba, please yallab'ai ku daina na rok'eku."
Had'e hannaye tayi alamar rok'o tace" Na rok'eka ka mayar da ni garinmu, ka taimaka ka kaini wajen iyayena ina son ganinsu."
Mik'ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace"...
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*20*
Mik'ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace "Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci kad'an zan tabbatar miki da haka."
Girgiza kai tayi kamar zata fashe da kuka tace "Yallab'ai ni kawai ina so na koma rayuwata ta baya, wannan labaran da kuke bani zasu iya saka zuciyata tarwatsewa, ta ya mahaifin daya kawoni duniya kamar yanda kuka fad'a kuma zai nemi kasheni?"
A nutse yana tsare fuskarta da ido yace "Saboda ci gaban mulkinshi ne, gimbiya Zafeera tarihin magabata ya nuna ke ce zaki kawo sauyi a k'asar nan baki d'aya, ba kuma zaki kawo wannan sauyin ba har sai mahaifinki baya kan karagar mulkinshi, to da haka ki fad'a min ta ya zai barki bayan ya tabbatar zaki kawo k'arshen mulkinsa?"
Dafe kanta tayi da hannu wasu hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, cikin nutsuwa da sanyayyar murya tace" Da a ce zan kasance yar wannan sarkin da gaske kamar yanda kuke fad'a min, tabbas da na hak'ura da kawo sauyin nan dan kawar da duk wata hatsaniya tsakanin 'ya da ubanta, da zan yi k'ok'ari na ga ran mahaifin nan bai b'ace ba bare har na taimakawa son zuciyarsa wajen yunk'urin kasheni."
Murmushi yayi yace" Haka kike gani, shiyasa na ce ki bani d'an lokaci dan tabbatar miki."
D'auke hannunta tayi ta kalleshi a marairaice tace" Yallab'ai zaka iya barina ni kad'ai?"
Cike da tabbaci yace" Me zai hana gimbiyata? Na barki lafiya."
Juyawa yayi ya fita inda ta bishi da kallo har ya fice, a hankali ta lumshe idonta wasu hawayen suka sake gangaro mata, bud'e idonta tayi ta k'arasa gaban tagar ta bud'e labule, inuwar yammacin da shukokin da suka k'awata gidan yasa ta jin son kad'aicewa da kuma samun kyakyawan yanayin nan, sakin labulen tayi da sauri ta shiga takawa ta fita a d'akin.
Kallon fadawa da hadiman take ganin duk wanda suka had'e sai ya sunkuya ya gaisheta a yarensu na Gallois, har ta fita farfajiyar suna gaisheta, zagayawa tayi ta b'angaren hagunta ta k'arasa kusa da shukokin, wani dogon numfashi ta ja idonta a rufe sannan ta sauke numfashin tana mai bud'e idonta akan koreyan shukokin, sanyin mai d'auke da ni'imtacciyar iska sosai ya mata dad'i, rumgume hannayenta tayi tana sake sauke numfashi.
Sannu sannu ta fara shiga duniyar tunani har tayi nisa, a haka kuma tana takawa zuwa ga shukokin, saida ta d'aga k'afarta ta tsallake d'an dakalin da aka zagaye shukokin, shiga tayi ciki tana taka k'ananun ciyayin a rashin sani har ta taka mab'allin pampon dake ba wa shukokin ruwa a duk sanda lokacin ba su ruwan yayi, tana takawa sai kuwa tsinin takalminta ya dannu wasu k'ananun k'arafu na suka bud'e suka shiga feshin ruwa suna juyawa ta ko ina.
Zuwan abun bazata da kuma yanda ruwan ke fita kamar ruwan panpo na sama yasa ta zabura ta waro idonta, da sauri ta kalli k'asa dan tasan tabbas ita ce ta taka, tana ganin wurin ta sunkuya da niyyar kashewa, sai kawai ta ji daga bayanta wani bafaden yace "Ranki shi dad'e ki barshi zan kula da komai."
Mik'ewa tayi ta fito ta shiga takawa da sauri tana tattaro rigarta tana matse dan har ta jik'e da ruwa, lokaci d'aya kuma tana mayar da gashinta baya tana matseshi shi ma.
Duk abinda ke faruwa tsaf a idonshi yana hangenta daga sashinta ta saman bene, da fari kam dariya ce ta kubce mishi, amma ganin zata koma inda ta fito tana matse kaya sai ya k'urawa duk wani namiji dake wurin ido yana son ya tabbatar da inda idonsu suke kallo, shin sun tsareta da ido sakamakon jik'ewar kayanta suna k'are mata kallo? Ko kuma dai hankalinsu na kan aikinsu kamar yanda suka saba? Saida ya ga shigewarta kad'ai sai kawai ya ji wata nutsuwa ta d'an sauko masa, ko ba komai yasan dai zata canza kayan jikinta.
A wani ikonce ya d'auke kan shi daga gurin yana had'e fuska ya mayar kan k'aramar na'urar dake hannunshi yana ta binciken abinda yake k'ara son tabbatarwa, dan shakkun da yake da akan Haman da wanda Ayam ta k'ara masa a kai yasa ya ji bai yarda da kowa ba hatta ita kan ta hukumar ta su bincike kan miyagun laifuka da hana ta'addanci.
Ko da ta koma d'aki wanka tayi gaba d'aya sai ta canza kayanta, yanzu kam riga da wando ne saidai basu da maraba da irin kayan yan Pakistan, dan har da mayafinsu su ma wanda ta rasa wa ya siyo mata kayan nan haka masu rufe jiki? K'arshe dai mayafin a kafad'unta ta daidaita ta d'orashi sannan ta fito a d'akin dan zaman haka kurum isarta yake, gashi ita ko gudu na tayi bare sauran motsa jiki.
Masu gadin dake tsaron k'ofar d'akin sarauniya wanda yau ne aka sakasu saboda alfarmar data nema gurin sarki Wudar d'in ta kalla tace "Zan iya shiga ciki?"
Jinjina kai d'aya yayi yace "Bayan shugabanmu sarki Wudar da yarima Umad, ke ce ta ukun da aka yarje mana mu barki ki shiga ciki, sai kuma jakadiyarta mai kula da ita."
D'an murmushi tayi a hankali suka bud'e mata k'ofar ta shiga, yanda dai take da tabbacin zata sameta haka ta samu, kwance amma kuma idonta bud'e alamar ba bacci take ba, murmushi ta d'ora a fuskarta tana k'arasawa kusa da ita d fad'in "Sannu da hutawa madam."
Zaune tayi bakin gadon daf da ita ta kamo hannunta kamar yanda tayi da safe ta rik'e jim, tsurawa fuskarta ido tayi tace "Kina da buk'atar wani abu ne?"
Kamar d'azu da safe sai kawai ta damk'e hannunta alamar e, jim Ayam tayi alamar tunani sannan tace "Abinci?"
Sarauniya Kossam k'ura mata ido tayi bata damk'e hannunta ba alamar a'a kenan, d'orawa tayi da fad'in "Ruwa?"
Shi ma dai shiru tayi, d'orawa tayi da "Zaki shiga toilet?"
Ganin dai ba amsa sai tayi saurin fad'in "Kin gaji da kwanciyar?"
Matsa hannunta tayi alamar e, murmushi ta fad'ad'a tace "Na gane, bara na samu wanda zai taimaka min sai mu fitar da ke waje."
Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa."
Fita tayi a d'akin sai kuma tayi katarin had'ewa da wata hadimar, dakatawa tayi tace "Na ce ba, ina za'a samu kujera irin ta masu jinya?"
Jim tayi alamar tunani sai kuma tace "Ina jin akwai a d'akin ajiye kaya, da ana d'ora sarauniya a kai idan za'a kaita d'akin gashi."
Jinjina kai tayi tace "Ok, ki kawo min."
Jinjina kai ita ma tayi a ladabce dan dukansu an nuna musu mahimmancinta sannan tace "To ranki shi dad'e."
Juyawa tayi zata koma ciki tace "Idan kin d'auko ki kawo min d'akin madam."
Da mamaki tace "Madam?"