← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 86

Sashe 74

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karb'a yayi ya bud'e murfin ya fesa mata a jiki, lumshe ido dukansu sukayi saboda tasirin turaren, sai dukansu suka daure ta hanyar bud'e idonsu kamar babu wani abu da ya faru.

Aje kwalbar ta yi sannan ta d'auki zoben azurfa ta mik'awa Ayam tace" Ki saka mishi a yatsar data miki."

A sanyaye ta amsa tana kallonshi shi ma kuma kallonta yake, hannunshi na hagu ya mik'a mata wanda yake sanye da wani zoben a yatsar kusa da k'arama, kallon yatsun na shi tayi da kyau, a hankali ta kai yatsunta biyu ta cire mi shi wannan zoben sannan ta saka mishi na hannunta, kallonta yayi sosai murya kasa k'asa yace "Wannan fa mai daraja ne."

Ba tare data boye muryarta ba ta amsa mishi a yaren Italy tace "Shi ma mai darajar ne."

Tana gama fad'a ta kalli iyayensu da suma ke kallonsu suna murmushi duk da basu ji me ta ce ba ita, amma zoben na shi d ta saka a yatsarta babba ya k'ara basu sha'awa da dariya, wanda shi ma kuma hakan ya masa dad'i.

Da haka Juman ta dinga gabatar da al'adarta har ta ida sannan suka ba wa bak'i damar zaunawa a mazaunansu dan su ci abinci, sosai d'akin taron yayi shiru dayawa saboda kowa mai ji da kan sa ne, bayan k'arar cokula da takalmin hadimai dake yawon raba abinci da kowane teburi babu wata hayaniyar, sai magana k'asa k'asa kawai da hirar mutane ke tashi.

Ganin hankalin mutane baya kansu yasa Ayam yunk'urawa tare da fad'in "Ya Allah." Ta mik'e, takawa tayi zata sauka daga matakalar d'aya yace "Ina za ki je?"

Juyowa tayi ta turo bakinta gaba tana jujjuyashi tace "To ai ban san an d'ora dokar hana d'aya daga cikinmu tashi a nan ba."

Tana fad'a ta juya ta ci gaba da tafiyar ba tare da ta ji daga gareshi ba, da kallo ya bita yana murmushin gefen labb'a, tafin hannunshi yasa ya kama gemunshi dake ta k'yalli yana wasa da shi a ranshi ya ayyana" Rigima ko? To ai na bayar da hak'uri, kuma ma ai halalina ne."

Wani murmushin ya kuma saki ya bi d'an k'ugunta da kallo, cije leb'en k'asa yayi ya d'an kawar da idonshi kad'an daga kanta yana tuno yar gajeruwar had'uwarsu da ita.

Sake maida idonshi yayi kan ta dan baya jin zai iya kawar da gani gareta na sakan biyu, saidai abinda ya gani yasa ya zaro ido har ya furta "Iyeeeh!"

Bai ankara da ya mik'e tsaye ba saida ya ji ya d'aga kafarsa ya taka k'asa, da sauri ya shiga takawa da gaggawa ya isa gareta, yana zuwa yay karaf ya karb'e kofin kwalbar mai shak'e da ice cream dan bak'in wanda take daf da kai wa bakinta da d'an cokalin k'arami.

Da sauri ta kalleshi suna had'a ido ta kyab'e fuska tace "Sha zan yi fa, kai ma ka d'auki na ka mana."

Hannunta ya rik'e gam a cikin na shi ya d'ora kofin kan wani tebur sannan ya jata zuwa wani corridor da babu kowa sai masu wucewa.

Neman fizgewa take saida ya kai ta inda yake da buk'ata kad'ai ya dakata tare da mannata da bangon, saida ya mata runfa da k'irjinshi kamar zai fad'a mata sannan ya k'urawa fuskarta ido, hakan ya haifar da kusanci sosai a tsakaninsu ta yanda numfashinsu ke gauraya, k'asa ta sauke idonta tana wasa da hannayenta wanda bai ko bata damar had'esu wuri d'aya ba, cikin narkakkiyar murya a sanyaye yace "Kar ki sha sanyi kin ji...*Sajeeda*."

D'aga idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi saurin sadda kanta k'asa, a hankali yasa yatsanshi ya tallabo hab'arta ya tilasta mata kallon fuskarshi, k'asa tayi da idonta sosai yanda sam bata kallonshi, daf da fuskarta ya sake matsawa yace" Me ye?"

A hankali ta girgiza kai cikin gargadar murya kamar zata b'alle da kuka tace" Ka...wai dai...na ji..ka kira...fassarar suna na ne da yarenku."

Mamaki ne ya bayyana a fuskarshi yace" Kenan kinsan Ayam yana nufin Sajeeda ne?"

A hankali cikin dubara ta d'aga kai tare da fad'in" E."

Gyara tsayuwarshi yayi sosai ya sake babbaketa ta yanda ba zata motsa ba yace" Kenan ni ma kinsan fassarar na wa sunan?"

Shiru tayi bata amsa mishi ba sai k'ok'arin kawar da kanta da take, sake cewa yayi" Uhum! Ina jinki."

Kallon k'wayar idon shi tayi da sauri tace" *Faruk* mana, na sani ai."

Murmusawa yayi tare da sake tallabo hab'arta yace" To e ye na hassalar? Ki bani amsa mana da girmamawa."

Cikin fad'a ta ture hannunshi tace" Ni ka matsa zan wuce."

Har zata rab'ashi ta wuce ya rik'o hannunta hakan yasa ta tsaya cak, juyawa tayi suka kalli juna, cike da sigar tsokana yace" Ba kya tsoron abinda zan miki idan aka ware mana d'aki ne?"

Da mamaki ta kalleshi tace" Ware mana d'aki kuma? Haka ka ke tunani?"

Gyara tsayuwarta tayi tace" Yallab'ai, ka ga dai ai ina jin kunyarka ko? Kuma ina ganin kimarka da darajarka, to me yasa ba ka ji kunyar abinda ka yi ba?"

Cike da danne dariyarshi duba da yanda take maganar yace" Amma ai na baki hak'uri ko? Kuma na ce zan dinga fara bayar da hak'urin kafin na yi yanzu."

Hawayen data rik'e tun sanda ya matse mata wuri ne ta ji sun taho mata masu zafin gaske, nunashi tayi da yatsa tace" Dama can da nufi ka yi na farko? To ka sani ni ma n san 'yancin kai na kuma zan k'waci.'yancina."

Yatsar da take nunashi da ita ya jawo da k'arfi hakan yasa ta fad'o jikinshi bata shirya ba, matseta yayi a jikinshi sosai ya kuma had'ata da bangon nan, k'ure fuskarta yayi da kallo har ya had'a hancinsu wuri d'aya, cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace "...

*Nagode sosai yan uwa da uzurinku gare ni, Alhamdulillah mun gama sabga lafiya.*

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:45 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*43*

Cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace "Za ki hak'ura ne ko kuwa?"

Sake sunkuyar da kanta tayi tace "Um um."

Hannunshi d'aya da ya katangeta ya d'auke yayi saman wuyanta da shi, sannu sannu ya fara kai hannun k'asan rigarta har ya shigar da shi ciki yana k'ok'arin tab'a k'irjinta d'ora tayi ram da shi ta rik'e tana kallonshi kamar ya bata tsoro.

Gimtse murmushin da ya so saki yayi sannan ya d'aga girarsa d'aya wanda hakan ke k'ara masa kyau, cikin had'e fuska yace "Me ye?"

Kamar doluwa tayi da fuskarta ta hanyar kyab'eta tace "Kai zan tambaya ai, me ye haka?"

Sannu a hankali ya matsar da fuskarshi saitin wuyanta har ya kai bakinshi kan fatar wuyan na ta, d'ora labb'anshi yayi tare da bud'esu yanda lemar labb'anshi ya dira kan fatar ta ta wacce ta d'auki d'umi na gyaran da ta sha, luf ya lumshe idonshi ya fizgi wani numfashi ya sauke shi da k'arfi, sai kuma ya sake rufe idon sosai ya fara tsutsar wuyanta sannu a hankali yana shak'ar wani daddad'a kuma sanyayyen k'amshi dake fitowa a sirrince daga jikinta.

Yanda ta rik'e hannunshi haka ta kasa sakin hannun, gaba d'aya komai na ta ya tsaya saboda bak'on al'amarin da ya zo mata da shi, tunda suka samu kusancin nan sosai sai ta ja dogon numfashi ya kuma mata gardama wajen dawo da shi ta sauke, tattausan labb'anshi da suka tab'a fatarta yasa ta jin wani irin ni'imtaccen d'umin daya samo asali daga yawun bakinshi, duk da jikinta na fitar da wani sassauk'an d'umi, amma da ta ji na bakinshi sai ta ji kamar ita a cikin k'ank'ara take.

Lumshe idonta tayi ba tare data san tayi ba ma sai ita ka ta langab'ar da kanta ta d'ora kan na shi kan dake tsakanin wuyanta, gimtse bakinta tayi saboda jin k'arfi da yaji tana son fito da wani sanyayyan numfashi mai kama da kuka, ga bak'on abun da take ji gaba d'aya illahirin jikinta, kamar ana mata tafiyar tsutsa sai wani yam yam ake mata, ga wani zut zut da take ji a k'asanta kamar tana neman wani abu ido rufe.

Sumbatar wuyanta ya ci gaba da yi har saida ya zo daf da bakinta, sai ya d'ora labb'anshi kamar za tsotsa sai kuma ya d'an dakata, yayi haka kamar sau uku sai kawai ya had'e bakinshi da na ta wuri d'aya ya fara tsutsa a hankali.

Shiru ta masa bata hanashi ba haka kuma bata kama masa ba, sannu sannu jikinta ya fara mutuwa har ta saki hannunshi dake sama kusan wuyanta daf da k'irjinta har yanzu, yana jin ta saki hannun ya fara yin k'asa da shi har ya kawo kan mamanta da suke cikin bras wacce bata da ciko.
Chapter 74 · 0% Book details