← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 86

Sashe 69

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya kalli Haman sannan ya kalli mahaifiyarshi yace "Mah, dama tana da d'an uwa da ban sani ba?"

Tab'e baki mahaifiyarshi tayi tace "Ban sani ba nima sai yanzu, ai ba ni na had'a aurenka da ita ba, mahifinka ne kuma baya raye."

Da mamaki yace "Amma ai Pah ya fad'a min kafin ya rasu cewa na rik'eta amana ni kad'aita gareta tunda iyayenta suka rasu."

A sanyaye Zeyfi tace "Ya fad'a maka hakane saboda haka d'in ne, Haman tun yana yaro ya bar gida saboda basa shiri da mahaifinmu, kullum cikin fad'a suke akan sab'anin ra'ayi, dan haka wata rana ya ce zai bar gida su manta da shi, cikin hushi mahaifinmu ya ce ya fi ruwa gudu, sannan shi ma ya sa a ranshi kamar bai tab'a haihuwar d'a namiji ba, wannan dalilin yasa nake ni kad'aita, saidai ni ban yada zumuncin dake tsakani na da d'an uwana ba, muna had'uwa a kai a kai sannan muna waya ma, saidai mahaifinmu ne sam ya k'i hak'ura, amma mahaifiyarmu ma sukan gaisa da shi ta waya, har ta rasu tana binsa da addu'ar alkairi, sab'anin mahaifinmu da ya rasu yana hushi da shi."

Musail ne ya kalli Umad da kulawa yace" ka yi maganar d'an uwanka, Umad fansa kake son d'auka har yanzu?"

D'aga ido yayi ya kalleshi yace" A gaskiya yallab'ai na shiga aikin bincike ne saboda kawai na samu hujjar da zan gurfanar da kai a gaban kotu na kashe min d'an uwana, amma yanzu...da na fara sabawa da Ayam kafin na san wacece ita, bana jin zan iya yin wani abu na k'i ko wanda zai cutar da kai, sai dai kawai ina so 'a san dalilin da ya sa ka kashe min d'an uwana, shin saboda ka auri matar da take son sa ne?"

Girgiza kai Musail yayi yace" Umad ba ni na kashe maka d' an uwa ba, hasalima ban da hannu a cikin kashe shi, kawai tarkon mak'iya na fad'a kuma sun yi nasara."

Da mamaki duk suke kallon kafin sarki Abdallah yace" Kana so ka ce duk hatsaniyar da aka tayar a ranar baka da hannu a ciki?"

Girgiza kai yayi ya kalli Umad yace" Ka tuna labarin dana fara baku d'azu? Sanda na je fada wajen Dhurani, to ai bayan maganar Zafeera na samu suna tabttaunawa kan yanda suka tsara wannan farmakin, lokacin da na buk'aci auren Juman ban samu ba na shiga cikin damuwa da b'acin rai, hakan yasa na shawarci Dhurani da Khatar, nan suka zugani suna nuna min bai kamata na nemi wani abu na rasa ba, sai Khatar ya ce na bar komai a hannunsa zai d'auki mataki, ba tare da sanin abinda zai aikata ba kawai na bashi umarnin yayi duk abinda zai sa Juman ta zama ta wa, to a nan ne suka tashi hatsaniya wanda a cikin wannan hatsaniyar suka yi nasarar kashe Urab, kuma a yanda na ji suna fad'a a ranar Khatar ya y hakan ne saboda cika burin wata masoyiyarshi."

Shiru ya yi inda Umad ya kalleshi yace" Masoyiyarshi kuma? Wa kenan?"

Kallon Umad d'in dake nuni zai fad'i abu marar dad'i sannan yace" Ban san cikakken labarin ba, amma idan ka samu k'anwar mahaifiyarka za ta sanar da kai komai."

Zaro ido yayi yace" Joyran?"

Jinjina masa kai yayi yana kallonshi shi ma, wuri wuri ya fara da ido yana rarrabasu, ba zai ce k'arya ba ce kai tsaye tunda har ua gane tana neman da mahaifinsa, saidai me ye ribarta a cikin aikata hakan? Ta yi ne dan ta samu mahaifinshi? Ko kuma dan ta mulki gidan kamar yanda ta yi kafin zuwan Ayam ta samarwa gidan 'yanci?

Zunbur ya mik'e yana laluba wayarsa a aljihu, da sauri ya fice a falon ya barsu da bin shi da kallo, saida ya b'ace ma ganinsu sarki Abdallah ya kalli Bukhatir yace "Zamu dakatar da nad'aka matsayin sarki har sai mun tabbatar da baka da laifi."

Ajiyar zuciya Musail ya sauke ya kalli sarki yace "Yallab'ai, ina rok'onku da ku yafe min abisa abubuwan da suka faru, sannan zan so ku huta yanzu, zuwa dare zamu tattauna akan wata magana mai mahimmanci."

Kallon Juman yayi dake gefenshi sannan yace "Abinda ya shafi tsakani na da ita, da kuma tsakani na da Ayam."

A sanyaye sarki Abdallah ya gyad'a sannan yace "Ba damuwa komai ya wuce, saidai zuwan nan na mu kamar yanda na fad'a shagalin bikin Ayam ne ya kawo mu, dan haka za'a fara shagalin nan daga gobe, dole k'asar nan ta shaida ana bikin 'yar gata, ya ga sarki Musail sannan jikanya ga sarkin Egypt."

Murmushi Musail yayi yace" Duk yanda kuka yi d'aya ne, Allah nuna mana."

Da mamaki sarauniya Bilkees tace" Wai ko dai ka musulunta ne kai ma?"

Sunkuyar da kai yayi irin a gaban surukan nan ya shafa kanshi kawai bai ce komai ba, mahaifiyar Bukhatir ce ta d'ora da basu hak'uri akan abinda Bukhatir d'in yayi sannan ta nema masa afuwa da fad'in shi kad'ai ne babba daya rage musu, kar su rabasu da shi, hannu bibbiyu sarki Musail da Abdallah suka karb'i k'orafinta kafin zaman na su ya k'are.

Masaukin bak'i aka kai su sai sarki Abdallah da aka keb'e musu wuri na musaman sannan aka shiga had'a musu girki na musamman da karin kumallo.

*Alhamdulillah.*
01/01/2022 脿 11:43 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*40*

Umad a fita daga nan d'akinshi ya nufa, iya abinda zai buk'ata kawai ya d'auka na daga kud'i da passeport d'inshi da kuma babbar wayarsa, fitowa yayi ya sa dreban gidan ya kai shi filin jirgi, yana shiga ciki dan samun izinin tafiya sai ga Joyran na jan k'aramar jakarta da sauri, da mamaki ya kuma dubawa da kyau dan ya tabbatar ita ce ya gani? Ko kula dai tsabar son had'uwa da ita yanzun ne yasa yake ma wasu matan kallonta?

Har ta d'an gitta ta gabanshi ta wuce sai k'amshin turarenta mai k'arfin gaske ya shaida masa tabbas ita ce dai wacce zaka tafi yanzu dominta, to amma me ya kawota nan? Kafin ya samu amsar ya taho sukwane yace "Aunty."

Bata juyo ba saboda tunanin wa zai kirata da haka a nan d'in, saida ya matsa daf da ita yace "Aunty Joy."

Da sauri ta juyo saboda d'aukar muryarshi da kuma tabbatarwa da ita dai a ke, suna had'a ido duk da hular dake kanta (hana sallah) da bak'in gilashi k'ato data saka saida ta ji gabanta ya fad'i har ta furta a k'asan mak'oshi "Umad kuma?"

Bai yi mamakin ganinta a wannan lokacin ba, saidai mamakin da ya ke shi ne hala bata san gogan na ta ya bar duniya ba?

Da mamaki da kuma rawar murya tace "Amm..Umad, me...kuma ka ke y...a nan? Ina nufin me ya kawo ka nan?"

Murmushi ya sakar mata tare da sunkuyawa yace "Ina kwana auntyna."

Wani murmushi ta saki wanda kai tsaye daga zuciyarta ya fito sakamakon ganin ya gaisheta kamar yanda yake yi a da, kafin zuwa shed'aniyar nan ta lalata mata komai, damtsenshi ta dafa tace "Lafiya lau Umad, baka amsa min tambayata."

Kallon k'wayar idonta yayi sannan yace "Aunty mun zo shak'atawa ne tare da abokaina, yanzu ma wani malaminmu ne ya zai zo saboda zamuyi yawan bud'a ido da shi, shiyasa na zo nan."

Dariya tayi tace "Masha Allah, Umad kai dai baka son zama wuri d'aya."

Wani malalacin murmushi ya mata bai ce komai na, rik'o jakarta yayi yana kallon fuskarta yace "Aunty ke fa? Me ya kawoki Khazira?"

Cikin kame kame tace "Uhmm..ka gane, ni ma dai na zo had'uwa da wata k'awata ne da mukayi karatu tare, tayi aure kuma ban samu na zo ba saboda hidimar kula da aunty (Kossam), shine yanzu na zo na mata murna."

Jinjina kai yayi yace "Yayi kyau hakan, amma kafin nan aunty mu je na kaiki masaukinmu, dan kinga bai kamata ki d'ora mata nauyi ba ko?"

Da sauri tace "A'a a'a Umad, ai mun yi da ita zan sauka a gidanta, ka ga ba zata ji dad'i ba, kuma m ai zata turo drebanta ne ya d'aukeni."

Cewa yayi "Duk da haka aunty na, mu je mu jira dreban, idan ya zo sai ya saukemu a masaukin."

Yanda yayi gaba da jakarta yasa bata da wani zab'i sai bin bayanshi, gasu tsaye mutane na ta barin wajen amma su suna nan, tana son sanin ta yanda zata ribace shi ya bar wajen sannan ta shige taxi, amma ya gagara hakan, hatta ruwa da ta ce ya kawo mata da jakar ta ta ya tafi ya siyo ya dawo, k'arshe dai kallonta yayi yace "Aunty na, anya kuwa dreban nan zai zo?"

Dariyar yak'e tayi tace "To gashi dai shiru, amma zai zo, zai zo na sani."

Girgiza kai yayi tare da tare taxi yace "Ba zai zo aunty, idan har tana ganinki da daraja ba zata yarda ta kasa turo mai d'aukarki kafin saukar jirginki ba, ni kuma ba zan tafi na bar nan ba na bar ki a tsaye."

Tura jakarta yayi a boot ya bud'e mata gidan baya yace "Shiga aunty."

Kamar zata fashe da kuka ta kalleshi amma haka ta shiga a dole saboda tana jin nauyin yi masa gardama, shiga tayi ta zauna ya rufe sannan ya shiga mazaunin gaba dreban taxi ya ja su zuwa titin da Umad d'in ya fad'a.

Da k'aramar wayarshi yake ta latse latse har suka yi nisa, Joy kam daga baya kamar zata fashe saboda takaici, k'eyarshi kawai take zabgawa harara kamar ta kashe shi, ga haushin da uwarshi ta k'unsa mata yau d'in, kawai ta sa hadimai na ta mata wani shirye shirye, data tambayeta ko lafiya ta ce zatayi tafiya ne, data tambaya zuwa ina sai cewa tayi "Bai dameki ba."
Chapter 69 · 0% Book details