Sashe 31
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mik'ewa Dhurani yayi ya bi shi suka fita inda waziri ya ji haushin hakan, ya so aje da shi ya ji me ya kawosu me kuma za'a tattauna, hakan yasa shi jan tsaki ya fara safa da marwa dan ba zai iya zama ba har sai ya jie aka tattauna.
*Giobarh*
Duk da ta jima bata kwanta ba amma sai ga shi k'arfe 07:00 tana bugawa ta farka saboda sabon tashi, saida ta bud'a idon ta ne ta fahimci inda ta kwana, a gajiye kuma a kasalance ta yaye rufar ta sauka a gadon, gaban madubi ta k'arasa tayi tsaye tana kallon kanta da tunanin me zatayi ? Gudu zata fara da shi? Ko kuma gyaran makwancin data tashi? A sanyaye ta fad'a ban d'aki ta fara da wanke bakinta da fitsari sannan ta fito, gurin kaya ta fara dubawa dan ta ga ko zata samu k'ananan kaya na motsa jiki, saidai duka kaya ne manya a ciki irin wanda ta gani jikin matar nan ta jiya (Joyran).
Rufewa tayi ta koma kusa da tagar gurin, bud'ewa labulen tayi hakan yasa hasken safiyar shigowa d'akin, ta madubin ta dinga kallon tarin shukokin wanda suka mata kyau take kuma ayyana lallai zasuyi k'amshi gurin kuma zai yi sanyi.
Da sauri ta saki labulen ta nufi k'ofa dan fita ta shak'i wannan daddad'an oxygen d'in, tana bud'e k'ofar ta fara takawa, fitowarta tayi daidai da bud'a d'akin sarauniya Kossam da wata hadimar tayi d'auke da farantin abincinta, a ladabce ta gaishe da Ayam d'in ta amsa, fuskarta a sake tace "Dama da mutum ne a nan?"
Da girmamawa tace "E ranki shi dad'e, ai d'akin sarauniya ne."
D'aga girarta tayi sama tace "Oh ! Zan iya shiga ciki?"
A ldabce tace "E to ranki shi dad'e zaki iya."
Hannu ta kai ta bud'e k'ofar ita ce a gaba hadimar na bayanta, ganin matar kwance yasa Ayam kallon hadimar tace "Bata da lafiya ne?"
"E, ai ta jima kwance a haka." Ta fad'a sanda take aje farantin hannunta, da tausayi Ayam ta kalli Kossam da idonta ke rufe tace "Me yake damunta ne?"
Girgiza kai tayi tace "A gaskiya ban sani ba, shekara uku da fara aikina a nan, nima a haka na sameta."
Da mamaki ta waro ido tace "Shekara uku? To ita shekara nawa ta d'auka a haka?"
Cike da jimami tace "A yanda na ji suna fad'a shekara ashirin kenan."
Da k'arfi tace "What? Oh my God."
Ta fad'a tana k'arasawa ga Kossam, zaune tayi bakin gadon ta rik'o hannunta, kamar ta tsikareta da allura sai kawai ta tsam ta bud'a idonta ta zuba akan Ayam d'in, wani tattausan murmushi Ayam ta sauke ta kalli hadimar tace "Ta farka, tana magana ne?"
Girgiza kai tayi tace "A'a ranki shi dad'e."
Kallon Kossam ta sake yi, sanyayyan murmushi ta sakar mata a karo na biyu ta sake jimk'e hannunta, cikin taushin murya tace "Kina ji a ranki kamar ki ce wacece ni ko?"
K'urawa fuskarta ido tayi tana son ta ga ko zata amsa lata da ido, sai kawai ta ji ta d'an jimk'i hannunta, kallon hannayen na su tayi sai kula ta sake kallonta tace "Kin gaji da kwanciyar nan haka ko?"
Sake jimk'e hannunta tayi, da sauri ta sake kallon hannayen na su, k'ura mata ido tayi tace "Kina so kiyi magana ne?"
Sake damk'e hannunta tayi, jinjina kai Ayam tayi tce "Zaki yi magana, zaki samu lafiya nan kusa ke ma."
Mik'ewa tayi tsaye ta kalli hadimar tace "Taimaka min mu gyara mata jikinta ta ci abinci."
Zaro ido tayi hadimar tace "A'a ranki shi dad'e, ai babu mai alhakin bata ko da ruwa ne sai mai girma Joyran."
A yatsine ta kalleta zatayi magana sai kuma ta ji Kossam ta sake rik'e hannunga gam a cikin na ta kamar za'a rabasu, kallonta tayi da mamaki ta kalli hannayen na su, nazartarta tayi sosai ta shiga karantar yanayinta, sai kawai ta kalli hadimar tace "Wacece haka kuma?"
Tausasa murya tayi tace "K'anwar sarauniya ce, ita ke kula da ita tsawon lokaci."
Mik'ewa tayi daga rank'wafawar tace "Kuma dole sai ita ce zata iya kula da ita, babu wani wanda zai iya saka hannunsa da sunan taimako?"
A tsawace tace "Malama kama min ita."
Da sauri ta matsa suka kamata ta dinga nunawa Ayam d'in yanda suke taimaka mata, har baki saida ta wanke mata da mai ta tsefe mata kai sannan tace ma hadimar "Samo mata kayan sakawa."
Da sauri hadimar dake mamakin iko na wannan yarinya ita ma tace "Ai kayanta suna d'aya d'akin, mai girma Joyran ce tasa aka mayar da su can."
A dak'ile fuska a had'e Ayam tace "Ai cewa na yi ki d'auko min, ba wai ki fad'a min inda suke ba."
Da sauri ta juya ta fita ta shiga d'akin da aka sauke Ayam d'in, ita kuma abincin ta d'auka ta fara ba wa Kossam wacce k'arara zaka fahimci fuskarta bata cikin yanayin nan na dumkum data saba.
Duk da ta ji an bud'e k'ofar bai sa ta juyo ba dan tunanin ta hadimar ce, amma sai ji tayi an ce "Uban wa ya baki damar bata abinci?"
A gadarance kamar wacce ta tashi da ciwon wuya haka ta juyo ta kalli Joyran wacce tashin hankali ya bayyana a gareta k'arara, d'auke kan ta tayi ka rantse bata san da mutum a wurin ba tace "Kin ci sa'a d'aya an ce yar uwar madam ce ke, ba dan haka ba da na ce *uban ki*."
Kossam kan ta saida mamaki ya bayyana a fuskarta, uwa uba kuma hadimar nan data shigo d'auke da kayan da Ayam d'in ta buk'ata, haka ma Joyran kusan jiri ta ji zai d'ebeta, yanda ta zazzaro ido ta k'ura mata su kamar wacce ke kallon gawa na motsi, sam mantawa tayi da a inda take me kuma take yi saida ta tsinkayi muryar Ayam a kunnenta tana fad'in "Ki daure ki k'ara kad'an madam, please."
Da sauri ta zabura kamar wacce aka mara ta k'arasa shigowa d'akin, cikin tashin hankali da neman bala'i ta bige farantin abincin tana fad'in "Ke har kin isa? Wacece ke da zak..."
D'aga mata hannu Ayam tayi ta d'ora yatsa a labb'anta tace "Shiiiii!"
Kallon fuskar Joyran d'in tayi tace "Haka kawai na tsani tsawa, na tsani a d'aga min murya musamman a k'ok'on kai na, na rlk'oki kar ki jawowa kan ki mummunar safiya ta hanyar tak'alata rikici, ina so na kafa kyakyawan tarihi a gidan nan kafin na barshi."
Juyawa tayi ta kalli hadimar tace "Kawo kayan ki taimaka min a saka mata."
A tsorace cikeda girmama lamarinta hadimar ta k'araso jikinta har rawa yake ta aje kayan kan gado, a tsawace Joy ta kalli hadimar tace "Ke! Idan baki bar nan ba sai na tozartaki."
Da kallo Ayam ta bi hadimar data fita a rikice ta rasa me zatayi, zagayawa tayi ta d'auki kayan ta warware ta tako zata koma inda take, cikin jin haushi Joy ta fizge kayan ta jefar a k'asa tace "Fita a nan malama, sannan ki ji da kyau."
Tayi maganar tana nuna Ayam da yatsa, d'orawa tayi da "Daga yau sai yau karko sake shigowa d'akin nan bare ki k'araso gareta, babu ruwanki da abinda ya shafeta, idan kuma kika sake to ki sani ki ma zaki tsinci kanki a mugun hali."
A take, a bazata, kamar saukar aradu Ayam ta rulgume hannaye tana fad'in "Kamar yanda kika jefata kenan?"
Wani mummunan fad'uwa ne gabanta yayi ta rarako ido ta kalleta, take wani gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta zuwa wuya, tsatsareta tayi da ido ta sake gyara tsyuwarta tace "Ko kuma zaki jefani fiye da halin da kika sakata ne duk tsawon shekarun nan?"
Kame kame ta fara tana jujjuya kai tace "Ke ke..me kike...fad'a ne wai haka ? Baki da hankali da alama."
Tana fad'a ta rab'ata zata fita a d'akin, ta kai daf da k'ofa kuma sarki Musail ya shigo daidai da Ayam tace "Ina da hankali, amma ki sani a cikin haukana zan bankad'o sirrin da kika jima kina b'oyewa ta hanyar wasar kura da rayuwar mutuniyar kirki."
Rud'ewa Joy tayi ta kalli sarki Musail dake binsu da kallon tuhuma yana son sanin me ke faruwa, fashewa tayi da kukan makirci tana fad'in" Wannan ma ai tozartani kike yi, yar uwata ce fa, ya kike tunanin da hannu na a cikin rashin lafiyarta?"
Shigowa yayi yana kallon Ayam yace" Gimbiya Zafeera, me yake faruwa ne? Tana neman b'ata miki rai ne?"
Kallonshi Joy tayi da mamaki wato bai ma damu da damuwarta ba bare kukan da take, figaggiyar ma yake tambayar ko ana neman b'ata mata rai ne?
Ayam kam murmushin yak'e tayi tace" A'a ranka shi dad'e, ba komai muna magana ne."
Kallon Joy yayi yace" Ki koma b'angaren ki, sannan ki kiyaye b'acin ranta, dan zan iya yin komai a kan ta."
Kallon shi Joy tayi ta k'ara kallonshi sau ba adadi, sai kawai ta juya ta fita dan bata san me zata fad'a ba, tana fita kuma Umad na shigowa har ma yana gaisheta amma sai ya fahimci bata cikin hayyacinta, yana shigowa ciki ya zuba idonshi akan ta, duk da rigar bata fito da jikinta ba face k'afafunta da kuma fuska sai tafukan hannu, amma sai ya ji ya tsani tsayuwarta haka kuma a gaban mahaifinshi.
Bai kula da sarki Wudar dake tsaye ba haka mahaifiyarshi da idonta ke kan shi, fuskarsa a had'e ya kalleta yace "Malama ki je d'akinki ana kai miki kaya yanzu."
Abun al'ajabi da mamaki daya kusan saka sarki Wudar suman tsaye shi ne yanda Ayam ta jinjina kai alamar to ta kuma kama hanya ta fice, sai ya ji ya fara kokonto ko dai ba ita bace, dan wacce aka fad'a fa komai matsayinka ita ce zata baka umarni kuma kayi jikinka na b'ari, hasalima ita waccen idonta kawai sun isa su saka mai aurenta durk'usawa kan gwiwoyinshi ya tambayi me take da buk'ata.