← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 86

Sashe 23

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da son waskewa ya d'an zagaya ya matsa daf da shi ya dafa kafad'arshi ganin kamar bai yarda da abinda ya fad'a ba yace "Ka gane ko, ina ga zai fi ka fara ta can d'in, zuwa gobe sai mu koma tare."

Wani arnan kallo Umad ya masa sai kawai ya jinjina kai alamar to sannan yace "Shikenan."

Sallama sukayi inda Umad na d'aukar hanya masaukin daya fara sauka ya k'arasa ya had'a kayanshi, dan yayi niyya yau ba sai gobe ba zai d'ora da neman Ayam, dan sai yake gani kamar Haman ya manta shi ne wajen rashin yarda da kafuwa, duk aminci da yardar dake tsakaninku ba zai saka shi d'auke ido a kan ka ba, bare al'amari na wacce yake da tabbacin za'a iya sadaukar da bilyoyin kud'i don samunta. Yana gama shiryawa saida ya fito ya d'auki hanyar zuwa filin jirgi sannan ya kira canal Jacob dan sanar da shi aikinshi ya k'are, dama hanya aka masa a gwamnatacce dan cika aikinshi, to tunda ya tabbatar da wacce yake nema ai shikenan.

*Bayan awa shida (Giobarh*: yana sauka a k'aton jirgin emirates d'in motoci guda hud'u ne suka zo dan d'aukarsa, sanda suka shiga rusuna masa d'aya daga ciki ya karb'i jakarsa mamaki ya shiga yi na samun tabbacin abinda yake zargi, dan ko mahaifinshi sarki bai fad'a ma zai zo ba, amma ga tarba ta musamman daga masarautarshi.

Limozine d'in da aka bud'e mishi ya shiga ya zauna suka mayar da k'ofar aka rufe suka d'auki hanya, gudu ake sosai dan tafiya ce mai nisan gaske daga filin jirgin zuwa fadar ta su, a d'an lokacin nan kuma tangale hab'arshi yayi yana kallon titi a zahiri a bad'ini kuma tunanin komai daya faru kuma yake faruwa yake, da wannan suka share awa d'aya a hanya kafin motocin su tsaya a k'ofar gidan suna oda.

Masu gadi biyu ne suka shiga jan k'ofar suna bud'eta tsabar girmanta da kuma nauyin da take da shi, danna hancin motocin sukayi a cikin farfajiyar wanda shi kan shi filin gidan wata k'asar ce daban data gaji da kyau da had'uwa.

*K'arshen free page, idan kina da buk'ata garzaya ki biya naki, sai kun zo masoyan asali.*

*Masoya na da suka biya kud'insu dan wannan littafi ina son sanar da ku zaku min alfarma d'aya, zan dinga sakar muku sabon shafi ne sau biyar a rana, saidai bai tsayar da ranakun ba gaskiya, kamar yanda a kowace rana ogana zai iya shigowa gari, hakan kuma na raunana rubutu na na kasa samun kai na, fatan zaku fahimce ni.*

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:35 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*13*

A k'ofar babban b'angaren motocin suka tsaya, da sauri suka firfito suka jeru suna jiran fitowarshi inda d'aya a ciki ya bud'e mishi k'ofa, k'afarsa d'aya ya fara zurowa mai sanye da takalmi kalar maroon k'irar turkey amma ba k'afa ciki ba, karasa fita yayi gaba d'aya cikin sauri ya tunkari shiga ciki suka rufa masa baya, saida suka kai daf da falon suka tsaya sai biyu da suka bi shi zuwa ciki, tunkarar matakalar da yayi yasa shi d'aga musu hannu alamar su dakata kafin ya shiga takawa da sassarfa kamar zai yi gudu.

D'aki na biyu a jerin corridor ya k'wank'wasa, bai jira izini ba ya bud'e ya shige dan yasan wacce ke d'akin ba zata iya bashi izinin ba, cak ya tsaya yana kallon sanyin idaniyar tashi, wani annuri ne ya ziyarci fuskarshi sanda ya d'ora idonshi akan kyakyawar fuskar dattijantakarta, a hankali kuma har sanyayyan murmushi ya bayyana a fuskar shi ba tare da sanin shi duk dan shauk'in ganin *mahaifiyarsa*.

Bai yi k'asa a gwiwa ba tunda yasan ba zata iya motsa ko da k'afarta ba yasa shi saurin k'arasawa gareta, saida ya zagaya b'angaren hagunta sannan ya durk'usa kan gwiwarshi d'aya, hannunshi na hagu yasa yana shafa gashin kan ta yana mayar mata da shi baya, tattausan murmushi yake sakar mata hannun dayan shi kuma ya sak'alashi cikin na ta, a sanyaye ya furta "Fy Mam (mahaifiya ta, a yaren Gallois)."

Farin cikin ganin mahaifiyarshi da kuma tsananin tausayin halin da take ciki yasa shi jin wata k'walla na taruwa masa a gefen idon shi, cike da k'arfin halin son kawar da ita yace " Fy Mam kina lafiya ko?"

Idonta dake rufe ya kalla wanda yasan ba dan bacci take ba da ta amsa masa da ido, k'urawa fuskarta ido yayi cikin muryar jimami da alhini ya sake fad'in "Komai ya kusa zuwa k'arshe fy Mam, na samota dana tafi, kuma zan tabbatar na kawo miki ita har nan, bansan ko nayi kuskure ba, amma dai dole ne sarki Musail ya d'and'ani hukunci, dole ya ji rad'ad'in rashinta yayin da zai hangeta a cikin gidan nan, amma kuma babu yanda zai yi, ko ta zama ajalinsa, ko ta zama silar rugujewar duk wani iko na shi, wannan bai dameni ba, zafi da tashin hankalin da zai shiga na rashinta ma kawai ya isheni."

Sake damk'ar hannunta yayi tare da sako hawayen daya gagara tsayar da su cikin k'unar zuci yace" Sai na d'aukar miki fansa fy Mam, a dalilinshi ne kike kwance ba kya motsa ko da yatsanki, a sanadiyarshi ne mahaifina ya rasa duk wani farin cikinshi, a sanadin shi ne na rasa d'an uwa na..."

D'ora goshin shi yayi a hannunta yana zubar da hawaye, wannan d'umi hawayen dake sauka hannunta ne ya farkar da ita, saidai ido kawai ta zuba masa tana kallon sumar kan shi, saida ya ci kuka mai isarshi ya d'ago kan shi ya zuba idonshi a fuskarta, suna had'a ido ya saki murmushi yana share k'wallan shi yace "Fy Mam, kin tashi ne?"

Ido kawai ta zuba mishi ba tace k'ala ba, murmushi shi dai kawai yake sakar mata, hannunshi na cikin na ta yana ta mammatsawa, banko k'ofar d'akin da aka yi aka shigo yasa shi d'aga idonshi ya kalli k'ofar, kan farin gemun mahaifinshi ya fara sauke idonshi kafin gaba d'aya farar fuskarsa, wani bayyanannan murmushi ya saki ya mik'e tsaye da hanzari ya tunkareshi, shi ma sarki Wudar da farin cikin ganin gudaliyarsa kuma magajinshi yasa shi bud'e hannayenshi yana fad'in "Fyddai (d'ana)."

Da fara'a shi ma ya rumgumi mahaifin na sa yace "Fy nhd (mahaifina)."

Sosai suka rumgume juna kowa na shak'ar k'amshin junansu, cike da so da k'auna sarki Wudar ya d'an bubbuga bayanshi hakan yasa suka d'ago suka kalli junansu, da farin cikin sake had'uwa da sukayi Wudar yace "Yaro na ya kake?"

Da fara'a ya sunkuyar da kai yace "Ina lafiya mahaifina, kamar yanda kake gani."

Jinjina kai yayi yace "Ya akayi ka zo baka sanar dani ba? Baka so na san da zuwanka ne?"

Kallon fuskarshi yayi yace "Amma yanzu ya akayi ka sani?"

Da fara'a ya amsa masa da "Abokinka ne ya sanar da ni, Haman."

D'an girgiza kai yayi tare da k'yabta idonshi alamar sam bai ji dad'i ba, nuna masa mahaifiyarshi yayi yace "Ka ga jikin na ta ko? Har hanzu Umad k'ok'ari nake akan rashin lafiyar mahaifiyarka, izuwa yanzu abun ya daina bani mamaki sai ma tsoro."

Jinjina kai yyi yace "Mam ta kusa samun lafiya Ba, insha'Allah."

Da mamaki sarki Wudar ya kalleshi yace "Me ka fad'a a k'arshen?"

Girgiza kai yayi alamar ba komai, sai kuma ya sunkuyar da kai yace "Ka gafarce ni mahaifi na, ni zan je b'angare na."

Da alamar mamaki a fuskar sarki Wudar ya kalleshi yace "Sosai nake mamakin sababbin halayanka Umad, wai me yake damunka ne?"

Kallon fuskar mahaifin na shi yayi, irin kallon nan na tsaneke kallo na basira, a take kuma ya d'auke idonshi ya mayar k'asa yace "Sarki na, zan sanar da kai komai da zaran mun zauna."

Bubbuga kafad'arshi yayi ya jinjina kai alamar gamsuwa, cikin nutsuwa yace "Ka huta da kyau, zuwa dare zamuyi tafiya."

D'an kallonshi yayi da mamaki sai kuma ya sunkuyar da kai yace "To Ba." Da ido ya masa izini da zai iya tafiya, a ladabce ya rab'ashi ya fita a d'akin, hadiman dake bakin k'ofar ne suka rusuna masa alamar gaisuwa, bai kula da su ba sai wucewa inda zai sadashi da na shi b'angaren.

A kasalance ya k'arasa had'add'en b'angaren shi, cike da gajiyar tafiya ya shige b'alle mab'allansa amma kuma idonshi a lumshe yana tunanin _"Ina take? Shin zai iya samunta a cikin gidan nan kuwa?"_

Ajiyar zuciya ya sauke ya bud'e idonshi tare da jefa rigarshi kan gado ya nufi ban d'akin shi yana tunanin tabbas idan suka zauna zai fad'awa mahaifinshi ya fa jima da canza addininshi.
Chapter 23 · 0% Book details