← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 86

Sashe 19

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A mugun razane kuma a kid'ime cikin tashin hankalin da Zafreen bata tab'a tsammanin fuskanta na ta ga wannan sark'a a wuyan Ayam wacce sark'a ce da ba ko ina ake samunta ba sai a wajen maccen data kasance mata a gurin sarkin Khazira, tabbas ana na bogi amma ta gasken kana ganinta zaka fahimceta, dan dutsen da aka k'era sark'ar da shi daga k'asan ruwa ake samunshi, had'akar lu'u lu'u da murjani ke samar da da dutsen sark'ar, hakan yasa Zafreen jin mugun jiri na neman kayar da ita ya tima a k'asa.

Kamar wacce aka tsoratar ko aka firgita ta juya tana fad'in "Ina! Hakan ba zai faru ba, ina!!!!"

Da gudu ta juya ta nufi hanyar da ake zuwa dan amsa kiran waya, su Laika ma da gudu suka bita suna kiranta, Ayam kam tab'e baki tayi ta gyara sark'arta ta juya a tsanake dan komawa b'angarensu dan ta gaji kam, tunda bai zo ba kuma shi ya sani.

Zafreen na zuwa a gigice ta shiga danna kiran lambar mahaifinta, tan fara kururuwa kam aka d'aga, a matuk'ar rud'e ta shiga fad'in "Pah, pah na ganta, na rantse da abun bauta Ghira na ganta, na ganta sanye da sark'ar Mah, na ganta da ido na."

Cikin fitar hayyacin daya ninka na Zafreen sarki Musail ya amsa da "A ina? Ina kika ganta?"

Saida ta shiga yarfa hannaye tace "A makaranta ne, yanzu haka tana wajen motsa jiki, gudu take, Pah ita ce na rantse."

Kamar zai fasa mata dodon kunne yace "Gamu nan zuwa, yanzu zamu zo Larhjadin d'in, waziri da Adah tun jiya suna nan dama, sun samu wasu bayanai akan ta."

Da sauri tace "Pah indai suna nan su ma ai sun isa, ba sai ka zo ba Pah zamu kawo maka ita."

Jim ya d'anyi sannan yace "Shikenan 'yata, na yarda dake."

Aje wayar ta yi ta juya ta kalli su Laika tace "Ina so na had'u da ita yanzu."

Jinjina kai sukayi suka nufi inda suka barta, amma da basu sameta nan ba sai kawai Laika ta ce su tafi dan su ma lokacin na su darasin yayi, idan sun fito sun had'u da ita.

*A k'ofar* gidansu Ayam gari ya k'arasa wayewa Umad, safiya na yi ya danna k'ararrawar sanarwar dake jikin k'ofar, daga ciki ya ji an ce "Ana zuwa."

Gyara tsayuwa yayi ya k'urawa k'ofar ido yana tunanin fuskar mahaifiyar ce ko ta 'yar zai fara arba da ita dan mace ce tayi magana.

Gaba d'aya k'ofar Habbee ta wangale ta sauke idonta cikin na Umad da shi ma ya saka na shi a cikin na ta, ganin bak'uwar fuska ce sai ta saki murmushi tace "Yaro da me zan taimaka maka?"

Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "...

*Yar uwa kin biya na ki ne? To ki hanzarta dan jin me zai faru, ga Umad k'ofar gidansu Ayam yana neman Zafeera dan d'aukar fansa, ga sarki da mutanenshi ma daf da ita, shin wanene ma Umad d'in nan wai? Sai kin biya na ki zaki san haka.*

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:34 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*11*

Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "Mahma, na zo muyi magana da ke, zan iya shigowa ciki?"

Had'e fara'arta tayi tace "Magana da ni kuma? A kan me?"

D'an d'aga idonshi yayi zuwa saman kanta dake ya fita tsayi ya hangi d'akin, a take kuma ya kalleta yace "Mahma, mai gidan baya ciki ne?"

Murmushi tayi tace "Shi ka ke nema?"

D'aga kai yayi alamar e tare da fad'in "E mahma."

Kaucewa tayi a hanyar tace "Shigo ciki, ya d'an fita zai siyo mana gasasshen bredi ne, yana shigowa yanzu."

K'afafunshi ya shiga zurawa cikin d'akin yana bin bayanta, amma idonshi akan gaba d'aya d'akin yake, komai kallo yake yana so ya ga ko zai ga hoto kafin ma ya ga zahirin, saidai babu komai daya shafi mutum, muryar Habbee ce ta katse shi daga wulk'itawar da yake ta ma idon shi tace "Me zan kawo maka?"

Murmushi yayi yacce "Coffee."

Jinjina kai tayi ta juya ciki, da kallo ya bita kafin ya sake maida idonshi kan komai dake d'akin, yana cikin kallon aka sake danna k'ararrawar k'ofa, da azama ya mik'e da tunanin Utais ne, Habbee kuma har ta fito dan ta bud'e k'ofar, juyawa yayi ya kalleta yace "Karki damu zan bud'e."

Murmushi tayi tace "Nagode."

K'arasawa yayi bakin k'ofar ya kama hannun zai murd'a sai kuma ya lek'a ta yar hudar da aka yi don tsaro ne dama, mutumin daya gani ne yasa shi zaro ido, duk da kayan jikinshi ba na masarauta bane amma ya san shi farin sani, da sauri ya shiga waigawa neman inda zai b'oye, a k'arshe wani labule ya d'aga ya shiga saboda jin an banko k'ofar da k'arfin da yasa Habbee daga madafa fad'in "Waye wai?"

Umad na kallo ta labulen nan har suka shigo tsakiyar d'akin, tunaninshi bai wuce son sanin abinda ya kawosu ba, tsakiyar falon suka shiga suna ta waige waige alamar su ma wani abun suke nema, d'aya daga cikinsu ne ya kalli Habbee dake ta tsatsaresu da ido yace "Ina mijinki yake?"

Cikin fad'a fad'a tace "Me zaku masa? Su waye ku? Me kuke nema a nan?"

K'akk'arfan ne ya d'aga hannunshi sosai ya d'auke fuskarta da mari, a gigice ta dafe kunci tana fashewa da k'ara har ta fad'i k'asa, a tsorace ta kalleshi sanda ya d'ora yatsarshi akan labb'anshi yace "Shiiiiii!"

Hannu yasa ya d'aga rigarshi ya ciro bindiga ya d'ora mata a kai yace "Ina yake?"

Daidai shigowar Utais kenan rik'e da takardar dake nad'e da bredi, sakin kayan yayi suka zube ya ruga a guje yana kiran "Kai! Su waye ku? Me ta muk..."

Bai gama fad'a ba d'ayan ya zuba masa k'ulli a ciki, duk'uwa yayi yana dafe cikinshi kamar zai mutu, tarin lafiyayyar gashin kan shi ya kaa da k'arfi ya jawoshi k'iii saida suka kawoshi daf da inda Habbee take zaune suka jefar, dukansu suka nunawa bindiga wanda yafi kaushin a cikinsu yace "Ina take?"

Kallonsu sukayi a tare Utais ne yace "Wacece?"

Wani wawan naushi ya zuba mishi a baki yace "Karo na k'arshe kenan da zaka nemi raina mana hankali, dan haka daga yanzu zuwa sanda zamu bar nan kasan me zaka fad'a mana."

Habbee fashewa tayi da kuka tace "Na rok'eku ku rabu da shi, ku daina dukansa hakanan."

A tsawace d'ayansu yace "Shiru."

Sake nuna Utais yayi da bakin bindiga yace "Tana ina?"

Lumshe ido Utais yayi ya had'e wasu yawu masu d'aci, bud'e idon yayi ya kallesu yace "Saidai ku kashe ni, amma na yi alk'awarin ba zan fad'a ba, ba zan tab'a cin amanar sarauniyata ba."

Jinjina kai d'ayan yayi ya d'an ja baya kad'an ya d'ana bindigar ya saita akan Habbee yana fad'in "Idan kai a shirye ka ke ka mutu, ban sani ba ko ka shirya rasa matarka ma? Zan k'idaya uku ka ceci matarka."

Da sauri ya kallesu a rud'e yace "A'a na rok'eku, kar ku tab'a ni ku min ko ma menene, kar ku cutar da ita."

Cikin kuka Habbee tace "A'a ka barsu, na yarda su kashe ni indai akan alk'awarin da muka d'aukawa sarauniya ne."

A tsawace yace mata "Shiru, kina da buk'atar kasancewa a raye, ko kin manta kina da mahaifiyar da rayuwarta ta dogara a ta ki ne? Ita kan ta gimbiya ta fi buk'atarki fiye da ni."

A hassale mutumin ya daka musu tsawa ya saka yatsarshi zai danna kunamar bindigar a kan Habbee yana fad'in" Ku mana shir..."

Bai gama fad'a ba alburushi ya tashi kan shi sai fad'uwarshi kawai suka gani da kua sautin alburushin, k'ara Habbee tayi a take Utais ya jawota jikinshi suka duk'e, d'ayan kam da wani irin sauri ya kalli inda harbin ya fito, saidai tuni Umad ya kawo daf da shi, bai ankara ba kawai ya buga mi shi hannun bindigar a hanci ya b'arke da jini, a take kuma ya rik'e hannunshi mai bindigar ya karya wuyan hannun hakan yasa shi sakin k'ara, su Habbee na kallon ikon Allah sai gani sukayi ya kama wuyansa gaba d'aya ya murd'e ba tare daya barsu sun shaida wanda yayi ajalinsu ba ya turasu kiyama.

A matuk'ar tsorace suka shiga kallonshi sai Utais da yayi k'arfin halin tashi tsaye yana kallonsa, nunashi yayi da yatsa jikinshi har b'ari b'ari yake yace "Kai ne? Me ka ke yi anan?"

Gyara tsayuwarshi yayi tare da soka bindigarshi a mazauninta ya kalli Habbee yace "Mahma, ki gafarce ni kar ki fahimce ni ba daidai ba."
Chapter 19 · 0% Book details