Sashe 17
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ladabce yace "Baba ina neman wata mata da miji ne, kuma an tabbatar min da kina da alak'a da su."
Da mamaki tace "Su wa kenan? Kuma wa ya fad'a maka haka?"
Murmushi yayi yace "Habbee da Utais."
A take jikinta ya d'auki kyarma tsabar tsoro da fargaba, neman sunkuyewa tayi daga tsayen da take, cikin in'ina da tashin hankali tace "Kai kuwa wa ya fad'a maka na san su? Su waye ma su d'in?"
Dariya yayi wacce ta fitoda kyanshi ya mik'e tsaye, cike da isa yace "Baba gashi kin fara d'orani a mizani, tambayarki ta farko ita ta nuna lallai kin san su, tambayarki ta biyu kuma ta nuna ba gaskiya kika fad'a ba."
Gyara tsayuwa yayi yace "Shin Baba zaki iya fad'a min inda zan same su? Ko kuma sai na..."
Bindigar k'ugunshi ya fito da ita yana shafawa, hakan ya k'ara rud'ar da ita sai ta rikice ta fashe da kuka, durk'ushewa tayi k'asa tana rok'onshi "Ka yi hak'uri zan fad'a maka, amma ka min alk'awarin ba zaka cutar da 'yata ba."
Da tsananin mamaki yace "Wacece' yar ta ki? Habbee?"
Jinjina kai tayi alamar e, jinjina kai yayi yana murmushin mugunta a fan shi yace "Lallai gimbiya Juman, wato kafin ta b'atar da 'yarta saida ta bi ta goge duk wani sawu da za'a bi dan kamata."
Kallonta yayi yace "Ina jinki fad'a min? Babu abinda zai same ta."
Mik'ewa tayi tana share hawaye tace "Larhjadin, bayan kasuwar *Buffar*, gida mai lamba 115."
Dad'in daya kama shi ne yasa shi rumgume tsohuwar ya sumbaci kuncinta, ko ba komai zai samu hutu da nutsuwa idan ya kammala aikin nan, sakinta yayi ya juya cikin sauri ya fita yana fad'in "Nagode Baba."
Wayarshi ya ciro a aljihu ya kira lambar Umad, sai dai bai sameshi ba dan lokacin suna jeji, duk da haka bai hak'ura saida yayi ta jarabawa, a k'arshe dai wani masauki ya samu mai kyau ya kama d'aki dan ya jira wayewar garin gobe tunda har magriba ta wuce.
*Larhjadin*
Keb'entacciyar asibitin makarantar Umad ya kai kan shi sakamakon yakushin da zakin nan ya masa, cikin k'warewa da nagartattun kayan aiki aka dubashi tare da yi masa allurar kashe duk wani dafi, kuma dama sam baya jin ciwon yakushin kamar yanda yake jin bala'in ciwo a jikinshi inda zakin nan ya daka masa k'afafunshi, lallai ya yarda k'afafun zaki zasu iya kashe mutum ma.
*09:30* Ayam ta shigo d'akin da aka kwantar da shi, dan bata san me ke faruwa ba saida Sabrine suka fad'a mata, su ma dan sun tafi karb'an magani ne na zazzab'i, kayan bacci ne a jikinta amma ta d'ora rigar sanyi a kai wacce zaka d'auka ta mata yawa ne, amma haka tsari da zubin rigar yake.
Saida ta je ta tsaya gaban gadon kdonshi rufe alamar bacci yake, rumgume hannayenta tayi tana kallonshi, ta jima tsaye tana k'are masa kallo tana doka murmushi, daga bisani kuma hannunta ta d'ora akan hannunshi dake kan k'irjinshi.
Kamar wacce ta daddab'ashi a take yaji wani yanayi a cikin baccinshi, tsam ya bud'e idonshi ya sauke akan fuskarta, da sauri ta d'auke hannunta tace "Am.. Sannu, ya jikinka?"
Muskutawa yayi ya tashi zaune da kyau yana kallon fuskarta, ba tare da yanayin wasa ba yace da ita "Me ya kawoki nan?"
Kamar marar gaskiya tace "Na zo duba jikinka."
Kallon tuhuma ya mata yace "Kin zo duba jikina ne amma kuma kike shafani haka?"
Baki bud'e tace "Lahhh! Ni fa kawai dubaka na zo na yi."
"Saboda kinsan dalilinki nake kwance a nan kenan?" Ya fad'a yana tsareta da ido.
Kawar da kan ta tayi ta turo baki a ran ta tace "Masifaffe."
Wani irin kallo ya mata kamar ya karanta me ta fad'a a fuskarta yace "Me kika fad'a?"
Da sauri ta kalleshi tace "Yallab'ai na ce ba, ni kam me yasa ka cika masifa dayawa ne? Ko sau d'aya ka jaraba yin wuni d'aya tak ba tare da b'acin rai ko had'e fuska ba mana, murmushi zai maka kyau sosai."
A hankali ya juyar da kan shi kan d'an teburin masu jinya inda ya d'ora bindigarsa, d'ora hannunsa yayi a kan bindigar ya kalleta cike da gadara yace" Zaki bar nan ko sai na fasa miki baki?"
Zaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace" Yallab'ai haushi na kake ji ne saboda na nuna maka zaki?"
Gyara zama yayi yace" Ke! Ke ce ma kika nuna min shi kenan?"
D'auke kan ta tayi daga gareshi tace" Kusan haka mana, ai na ga kai kuna had'uwa da shi gasar tsere kuka fara."
Me Umad zaiyi ba k'yalk'yalewa da dariya ba, sai ga shi da rik'e ciki yana dariya har da hawaye a gefen idonshi, kallonshi take har ta kai ta tab'e baki ta juya zata fita dan bata son dariya mai yawa, cikin k'yak'yala dariya yace" Ina kuma zaki je?"
Cikin sangarta tace" Ba korata kayi ba."
Jingina kan shi yayi a gadon yana tsagaita dariyar yace" Ban tab'a dariya irin haka ba tunda na ke Ayam, haka ma babu wanda ya tab'a kwantar da ni a gadon asibiti sai zakinki."
Murmushi tayi tace" Ba wani nan, jarumatarka ce ta kawo ka gadon asibiti."
Da sauri kuma sai tace" Wai ma me ye dalilin da yasa ka tari zakin nan ne? Kana tsoron kar ya illata ni ne?"
K'wayar idonta ya kalla yace" Ji nayi ba zan bari wani abu ya sameki ba, hakan zai sa na d'auki kaina a matsayin mai laifi na har abada."
Dariya tayi tace" Shiny shiy."
Kallon daya mata na alamar tambaya yasa ta cewa" Nagode to."
Juyawa tayi zata tafi tace" Saida safe."
"Karb'i." Ya fad'a yana mik'o mata wayarshi, karb'a tayi ta kalla da alamar tambaya, cikin sakin fuska yace "Ta mutu ne, ki saka min caji a d'akinku, likitan ya ce dole a nan zan kwana, kuma abin cajina yana d'aki."
A ladabce ta amsa ta juya zata fita, muryarshi ta sake ji yace "Nawa ne kwanan watan haihuwarki?"
Juyowa tayi tana murmushi tace "Yanzu haka 12:00 nake jira tayi na cika shekarata ashirin."
Murmushi ya mata yace "Wace shekara?"
Kai tsaye tace "Dubu biyu da biyu."
K'ura mata ido yayi sai ya rasa bakin magana har ta fita, saida ta fice ya fad'a a fan shi "Anya kuwa ba ita bace?"
*To fa yar uwa, ga wasar na d'aukar zafi gashi mun kusa zuwa k'arshen free page, dan haka ki hanzarta ki biya na ki dan samun damar kwamushe na ki karatun a nutse.*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:33 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._
_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._
_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._
Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.
_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*10*
Ko da ta saka wayar sai bata ga tayi alamar ta d'auka ba, ta jima zaune tana son ta ga wayar ta nuna mata tana d'aukar cajin, Deeyam da suke zaune kan gado suna jiran 12:00 ta yi ne tace mata "Dan Allah ki rabu da wayar nan ki zo, mu ji me kike shiryawa?"
Cike da damuwa tace "Wayar nan ce ta k'i d'auka fa."
Sabrine ce tace "Ki kunnata mana ta yiwu ta d'auka."
Jinjina kai tayi ta danna wayar dan kunnawa, Deeyam ce tace "E lallai, irin wannan damuwa haka, da alama fa akwai k'amshin wani abu tsakaninki da malam Umad."
Ganin wayar ta kama kuma lallai ta fara d'aukar cajin yasa ta mik'ewa ta nufosu tana tab'e baki tace "Kinji wani banzan tunani kuma, malamin na wa?"
Tsaki tayi ta zauna tana fad'in "Ba zan iya had'a hanya da mai saka uniform ba, dama dai shi d'in joker ne ko kuma mai aikin gidan zoo, zai fi armashi."
Bushewa sukayi da dariya sai Deeyam da tace "Ke kuma ki rasa wanda kike son yin rayuwa da shi sai wanda bai kai komai ba."
Sabrine ce tace "Ba ma wannan ba, me yasa take son auren irin mutumin nan?"
Zuba mata ido sukayi, numfashi ta sauke sannan ta kalkesu dukansu tana murmushi tace "Saboda ina so na rayuwa kusa da dabbobi, ina son ganinsu a kewaye da ni."
Gyara zama tayi tace "Ba wannan ba, yanzu me kuka shirya min ne na ga kuna ta b'oyo d'azu har da korata a d'akin nan."
Da sauri dukansu suka ce "Ba komai."
Da kallon tuhuma ta bisu tace "Kun tabbata?"
"E." Suka fad'a a tare, tab'e baki tayi ta mik'e ta nufi gadonta ta kwanta tana fad'in "Da 12:00 tayi ku tasheni."