Sashe 18
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba ma sai kin fad'a ba." Cewar Deeyam, dan suna son bata mamaki kamar yanda ita ma take basu idan irin wannan ranar ta zo musu, Ayam k'awa ce da kowa zai yi fatan samu, zata tsaya maka idan buk'atar hakan ta tashi, idan kana da kad'aicin yan uwa ita ta kan maye maka wannan gurbin, idan kuma maraici kake fama da shi zata mantar da kai shi, duk abinda take da tana baka ba tare d tunanin yawanshi ko darajarshi ba, haka kuma zata iya tare maka duk bala'in dake neman tunkaroka iya k'arfinta, kamar dai yanda tayi a kan Sabrine tsakaninta da Zafreen.
*12:57* ta d'an fara juya kan ta tana motsawa kamar zata farka, sam mafarkin da take yi bata jin dad'inshi, yatsina fuska take yi duk da a cikin bacci take, a can k'asan mak'oshi cikin bacci take fad'in "Ku daina, ku daina azabtar da ita, ku daina."
12:00 a daidai kunnenta suka taru su uku suka d'aga murya wajen fad'in "Barka da zagayowar ranar haihuwa."
A mugun zabure ta tashi zaune da k'arfi tana zazzaro ido a tsorace, Deeyam ce tace "Ke mu ne fa."
Kallonta tayi kamar bak'uwar hallita a hankali ta fara saisaita nutsuwarta, shafa kan ta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace "Oh, thanks."
Wani k'aton cake suka aje mata gabanta suka fara tafawa suna mata wak'ar murnar k'ara shekara, bushe wutar tayi sannan ta yanka cake d'in, a bkin Deeyam ta fara sakawa sannan ta saka a bakin Sabrine da d'ai k'awar ta su, dukansu ma yankawa sukayi suka saka mata a baki sannan suka dangwala suka shafa mata a fuska, daga haka suka haukace inda suka dinga d'ibar cake din suna shafawa junansu suna ta dariya suna tsalle akan gadon cikin nishad'i, dan iya daren garesu kawai da zasu iya yin wannan farin cikin, idan ba haka ba babu lokaci zuwa wayewar garin.
Wata babbar kwalba Deeyam ta d'auko ta lemu mai tsadar gaske sai ka ce barasa, saida ta girgizashi sannan ta bud'e duk ya pallatsar musu a jiki, kowa kofin tangaran ya mik'a ta zuba mi shi, suna tsaka da sha suka ji vibration na waya, a tare suka juya hakan yasa Sabrine cewa "Tun d'azu fa ake kiran wayar nan."
Deeyam yace tace "Watak'ila kiran ujila ne, ko wani abu mai mahimmanci."
Lek'a wayar Ayam tayi ta ga lambar an rubuta sunan *Ffrind* (aboki) da yaren Gallois, d'auke kanta tayi tace "Ku manta kawai, abokinsa ne."
Mantawar sukayi kamar yanda ta ce, saidai tuni aka sake kiran hakan ya katse musu shagalinsu, Deeyam ce tace "Ayam me zai hana ki kashe wayar nan, idan ba haka fa ba zamu huta ba."
D'an k'aramin tsaki tayi tace "Haba, malam ka kira sau d'aya ka ji ba'a d'aga ba kayi na biyu har da na uku, me zai hana ka shafawa mutane lafiya?"
Sabrine ce tayi saurin fad'in "A'a fa Deeyam, ni ina ga da d'agawa mukayi ko kuma dai ta je ta kai masa wayar, ki tuna fa akwai ujila a rayuwa, muka sani matarshi ce ko kuma mahaifiya ko mahaifi."
Cike da gatse Ayam tace "Ke ki je mana tunda ke ce matarsa d'in."
Murmushi tayi tace "Babu inda zan je in fad'a miki, ke zaki je tunda ke ya bawa wayarsa."
Deeyam ma cewa tayi "Gaskiya ne, ki je ki kai masa to."
Tsaki tayi ta kalli jikinta sai kuma ta kallesu, sauka tayi daga kan gadon ta d'auki wayar ta nufi hanyar fita, Deeyam ce tace "Akwai sanyi fa a waje, ki saka rigar sanyi mana."
"An k'i."Ta fad'a kai tsaye tana ficewa a d'akin, da kallo suka bi d'an k'ugunta da baya juyawa saidai dake tana da k'ira ba zaka gane komai ba.
Likitar dake daf da k'ofar shigowa ma'ana sai ka bi ta kan ta zaka wuce tana ganin Ayam ta murje idonta daga baccin dake son d'aukarta daga zaune, ba alamar girmamawa tace "Ke ina zaki je yanzu a daren nan?"
Kallonta Ayam tayi tace "Zan je gurin yallab'ai ne."
"Me zaki je yi?" Ta fad'a a gatsalce, gyara tsayuwa tayi tace "Dama kina zaune a nan ne dan tambayar abinda zai shigar da kowa nan?"
Mik'ewa tayi tsaye cikin hassala tace "Ke bana son shashanci banza, ya zama dole na san me zai shigar da ke ciki, idan ba haka ba kuma ki koma."
Matsowa tayi ta tsaya gabanta cikin gadara ta rumgume hannayenta, zuba mata ido tayi kamar zata had'iyeta tace "Kika ce saidai na koma?"
Haka kawai tsigar jikinta ta tashi ta ji ta kasa jurar kallonta, samun kan ta tayi da rusuna kan ta tace "Kinyi sa'a yau bana jin bala'i, da..."
Kasa k'arasawa tayi sai kawai ta kalli k'irjin Ayam tace "Shiga kawai."
Sama da k'asa Ayam ta galla mata harara ta wuce, tana shiga zaune ta sameshi yana kurb'an coffee a farin kofin tangaran.
Bud'a k'ofar da tayi ce ta ja hankalinshi zuwa kan ta, yanda ya so yi mata kallo d'aya sai abun ya ci tura ya kuma gagara, bai d'auke idonshi daga kan samb'ala samb'alan cinyoyinta ba wanda suke a cikin fari kuma gajeran wando iya cinyoyinta, haka ma rigarta fara ce mai siraran hannaye, kan ta kuma yanzu babu komai a kai face launin gashinta mai kalar maroon da d'an ratsin yellow yellow.
Gabanshi ta tsaya cike da shak'iyanci sakamakon lura da kallon da yake mata tace "Wato na maka kyau ko? Saboda ka ganni a hakane? Ai dama ni d'in kyakyawa ce."
Cikin jin kunya da takaicin kan shi ya duk'ar da kai yana fad'in "Me ya kawoki kuma? Ko dai kin gagara bacci ne a dalili na?"
Yatsina fuska tayi tace "Tabb'! Akan me ni kuwa zaka dameni?"
Ziiii! D'in da wayarsa dake hannunta tayi yasa ta mik'o masa tace "Uhum ka gani, wannan abokin na ka ne ya addabi mutane, a gakiya mutumin nan da ina da wani iko a hannu na dana sa an d'aure min shi, haba mutum sai takurar tsiya."
Duk tana maganar shi kuma yana kallon bakinta ne, saida ta dasa aya ya karb'i wayar ya duba sunan, kallonta yayi yace" Nagode to zaki iya tafiya, amma ki sani zan tuna miki wata rana."
Da mamaki tace" Me zaka tuna min?"
Girgiza kai yayi alamar ba komai, sannan ya lumshe mata ido ya bud'e alamar tafi, baki ta bud'e da matsanancin mamaki tace" Kai! Ni zaka kora da ido? Na rantse babu inda zan je sai ka min magana da baki, kaji ka kamar wani sarkin gaba d'aya k'asar Texanda."
Wani malalacin murmushi yayi yace" Kenan dole sai nayi magana da baki?"
D'aga kafad'a tayi tace" Haka kawai na ji bai min ba da ka min magana da ido."
Girgiza kai yayi saboda fara hawa masa kai da tayi ya nuna mata k'ofa yace" To ta fi."
Zura dogayen k'afafunta ta fara yi ta masa bye bye tace" Saida safe."
Saida ta kai daf da k'ofa zata fita yana k'are mata kallo yace" Barka da zagayowar ranar haihuwarki."
Juyowa tayi da fara'arta tace" Merci beaucoup."
Juyawa tayi ta fita a d'akin saidai kafin ta rufe kofar ta sake kallon shi, murmushi ta sakar masa tace" Halinka ya had'u yallab'ai, kai mutumin kirki ne."
Rufe k'ofar tayi ta fice shi kuma bai san sanda ya saki k'ayataccen murmushi ba har saida ya ji an sake kiran wayar, yana d'agawa cikin jin haushi Haman yace" Haba Umad, me ye haka dan Allah? Ya zanyi ta kiranka akan abu muhimmin amma baka d'aga min waya? Tun yamma fa nake kira."
Cikin rashin jin dad'in rashin kyautawa yace" Kayi hak'uri Haman, wallahi na samu wani d'an had'ari ne sakamakon shigarmu jeji, amma da sauk'i yanzu."
Cikin kulawa har ya manta da b'acin ranshi yace" Subhanallah, me ya sameka Umad? Kana ina yanzu?"
Girgiza kai yayi ya aje kofin hannunshi yace" Ba komai karka damu, na ji sauk'i yanzu ai, fad'a min ya ake ciki daga wajenka?"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace" Umad munyi nasara da yardar Allah, adreshin unguwa da lambar gidan da gimbiya Zafeera take duk yana k'wak'walwata."
Da k'arfi ya sauka daga kan gadon yace" Da gaske Haman? Ka samu? Ina take?"
Cikin farin ciki yace" E na samu, kuma abun farin cikin tana cikin garin da kai ma yanzu kake kamar dai yanda kayi hasashe tun farko."
Cike da k'aguwa da zumudi da farin ciki yace" Da gaske Haman? A ina take? Ban adreshin?"
Murmushi yayi yace" Na yi tunanin haka dama, na so zuwa garin yau amma na ga zanyi dare."
A k'age yace" Haman ba wannan na tambayeka ba, ina ne adreshin da zan sameta? Zan yi sammako na je na had'u da su."
Dariya Haman yayi yace "Bayan kassuwar Buffar, gida mai lamba 115, amma Umad..."
Bai barshi ya k'arasa ba yace "Nagode Haman, zan kiraka zuwa safe."
K'it! Ya yanke kiran ya shiga tattara komai na shi dake wurin ya fita a d'akin, likitar na masa magana amma ko kulata bai yi ba saida ya bar asibitin kwana kwanan.
*01/01/2021*
Tun gari bai gama wayewa ba d'aliban suka duk'ufa wajen gudu a filin makarantar, sun yi har sun fara gajiya amma yallab'ai Umad babu shi babu dalilinshi, cikin hakane Zafreen da tawagarta suka biyo ta filin zasu wuce.
Da gangan Zafreen ta bi ta inda Ayam ke gudu, Ayam kam na ganinta a cikin gudunta ta nemi kauce mata, amma dake neman fitina take da d'aukar fansa sai kawai ta tareta gadan gadan ta bankad'eta.
Fad'uwa ta nemi yi hakan yasa tayi baya tana tangal tangal, amma ikon Allah sai Ayam ta jawo hannun Zafreen hakan yasa suka fad'i tare k'asa.
A tare suka saki k'ara inda Zafreen ke kan Ayam d'aro-d'aro, da sauri su Laika suka kamo Zafreen ta mik'e tsaye, Ayam ma mik'ewa tayi tana kallon Zafreen d'in, hannunta na dama ta d'ora kan sark'arta tana k'ok'arin mayar da ita cikin rigarta dake riga biyu ce jikinta, d'aya ta sanyi mai zip a gaba sai k'aramar daga ciki.