Sashe 54
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sake murtuke fuska sarki Musail yayi ganin sai matarshi ya sakar ma fuska amma shi ya maidashi kamar wani sakarai ma, jinjina kai yayi a b'oye sannan ya kalli Haman yace "Sannu da zuwa."
Rusunawa yayi ace "Barka yallab'ai."
Muryar Juman ce ta dawo dasu da ta kalli Umad tace "Sannu ko?"
Jinjina kai yayi a ladabce yace "Sannu ranki shi dad'e."
Yatsina fuska sarki Musail yayi yace "Mu je mu ci abinci."
A sanyaye Ayam ta mak'ale kafad'a tace "Ni dai na k'oshi."
Juman ma sama da k'asa ta kalleshi tace "Ni ma haka."
Hannun Ayam ta kama zasu bar wuri ta kalli Umad tace "A ci lafiya."
Hanyar masaukin Ayam suka nufa inda sarki Musail ya bisu da kallo, a ciki yayi k'wafa alamar zku sani sannan ya nufi wajen cin abincin ba wai dan yana buk'ata ba sai dan bak'inshi.
Rankayawa sukayi kan teburin Umad na ta k'ok'arin b'amb'are hannunshi cikin na Zafreen amma ta rik'e gam, har saida suka isa duk suka zazzauna, tsaye ya so yi dan sake k'ara fahimtar komai na gida da takon kowa, amma sai Zafreen ta zaunar da shi da k'arfi har saida Musail ya kalleta yace "Ke!"
Sai kuma ya d'auke kai yana girgiza kan shi, haka aka zuzzuba abincin kowa ya fara ci.
Cokalansu kad'ai ke k'ara a wurin, cikin siririyar murya Zafreen ta kalli sarki Musail tace "Pah, kasan na jima ina fad'a maka ban samu wanda ya dace dani ba a garin nan?"
Zuba mata ido yayi shi dai bai ce komai ba, d'orawa tayi da "To yanzu na samu, wannan ne."
Ta k'arashe tana nuna Umad da ka rantse baya jin yaren ta, duk da dai d'in gaskiya bai cika jin yaren slovaque ba, amma dai yana ji jefi jefi saboda yanayin aikinshi da shige shige da kuma sa kai.
Haman a dake ji jefi jefi da Khatar da kuma Adah duk kallonta sukayi dan Dhurani tafiyarshi yayi bai tsaya ba, sarki Musail ma kallonta yake yi kamar ya wanka mata mari, haushin hakan yasa bai ce k'ala ba sai Haman daya kalla a nutse yace "Me ye sunanka?"
A ladabce ya amsa da "Ranka shi dad'e sunana Haman."
Jinjina kai yayi irin na dattawa yace "Haman Abraham Joshua kenan?"
Gyad'a kai yayi alamar e, lumshe ido yayi alamar gamsuwa, a tsanake ya sake furta "Me ye aikinka? Kuma a ina ka fara sanin Zafeera? Me kuma ya sa kake son aurenta?"
Cikin d'ar d'ar Haman yace "Yallab'ai na kammala karatu na, inda nake da burin mahaifina ya sama min aiki a babbar ma'aikata, Zafeera kuma mun fara had'uwa ne a Giobarh, saidai ban mata magana ba a saida na fara sanin wacece ita, ina kuma so ne na aureta dan ina sonta."
Wani hamshak'in murmushi sarki Musail ya saki yace" Bayan son da kake mata, sai kuma wane dalili?"
A hankali ya karkata ya saci kallon Umad da shi ma ke kallonsu ko abincin baya ci, sai kuma ya kalli sarki Musail yace" Saboda yar babban gida ce, ita ce ta dace ni."
Sauk'akk'en murmushi ya saki ya d'an fara tsakurar abincin yana fad'in" Mu ci abinci yanzu, nan da awa biyu zan had'aku da ita dan ku tattauna, idan kun fahimci junanku mahaifinka na zuwa nan ranar d'aura muku aure za'a saka."
Wani k'ayataccen murmushi Umad ya saki a ranshi ya ayyana" Lallai ma, ku gama duk shirin ku, na wa ne zai yi aiki a k'arshe."
Haka suka ci gaba da cin abincin da tattaunawa tsakanin Haman d'in da sarki Musail, bayan su babu wanda ya saka musu baki banda Zafreen dake ta k'ok'arin d'aukar hankalin Umad d'in tana ta washe masa baki.
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*31*
Wajen Ayam kuma d'aki suke ita da Juman inda ta tambayeta a tsanake "Mah, a game da lamarin ruwan garin nan, yau nayi magana da wasu daga cikin talakawa sun fad'a min komai, ya zanyi na taimakesu akan haka?"
A tsanake ita ma tace "Ayam ai maganar ruwan nan kasuwanci ya shiga cikinshi, duk da gwamnati na iya yin ta, bana jin zaki iya wani abu tunda baki da abu biyu."
Da alamar tambaya ta kalleta tace "Kamar ya Mah?"
Numfashi ta sauke tace "Na d'aya baki da kud'i, na biyu baki da iko."
Da mamaki tace "Idan ina da su kenan zan iya taimakon al'umma?"
Jinjina kai tayi tace "Tabbas, idan kina da kud'i zaki iya taimaka musu, idan kina da iko zaki mallaki dayawa daga cikin masu fad'a a ji."
Shiru tayi tare da fad'awa kogin tunani, sai ta ga bata da wad'annan abubuwan, da sauri ta rik'o hannun Juman tace "Mah, ke fa? Ai kina da iko saboda ke ce sarauniyar k'asar nan, kuma nasan kina da kud'i ma."
Murmushi tayi ta girgiza kai tace "Bana da ko d'aya yanzu Ayam, sanda mahaifinki ya jefani kurkuku ya datse min asusun bankina, gaba d'aya masarautar nan yanzu ba zan iya saka baki a abinda ya shafeta ba."
Da mamaki a fuskarta tace "Saboda me Mah? Na d'auka yanzu ai kin fito."
Sake fad'ad'a murmushi tayi tace "Ayam kenan, kafin ya fito da ni saida aka fad'a min na wucen gadi ne."
Cike da alhini a fuskarta tace "Mah...na kasa yarda Pah duk yake wad'annan abubuwan, har yanzu bana jin wani iri a jikina idan na ganshi."
Lak'ace hancinta tayi tace "Saboda yana mahaifinki ne mana, soyayyar dake tsakaninku ba zata bari tsoro yayi tasiri a kan ki ba."
Ajiyar zuciya ta sauke bata sake cewa komai ba, haka ita ma Juman ba tayi magana ba, saidai dukansu da abinda suke tattaunawa a zuk'atansu.
*08:30* Na dare ta fito cikin wasu had'add'un kaya na masarauta wanda suke jan k'asa har da babban mayafin da aka d'ora mata a kai amma ya sauka a baya, karo na farko a rayuwarta da aka shafa mata jan baki kalar leb'enta pink, bayan yau kam bata tab'a sakawa ba, tana dai shafa man leb'e amma ba jan baki ba.
Sanyayyan k'amshinta ne ya fara sanar da su tana zuwa, suna juyawa a tare da sauri Haman ya mik'e tsaye dan sak sarauniyar Khazira idonsa suka gane masa, hakan yasa shi saurin mik'ewa da girmmawa yana neman gaisheta.
A b'oye Umad ya ja rigarsa ya d'an motsa labb'ansa yanda ba kowa zai gane ba yace "Kula fa, kar ka kwafsa."
D'an gyara tsayuwarshi yayi ya saisaita kanshi ya dakata daga hard'ewar da yake shirin yi ya rusuna mata, da k'ayataccen murmushi ta k'araso a nutse zauna tare da nuna masa zai iya zama, zaune sukayi a tare inda ta d'an k'yallara idonta ta kalli Umad.
D'auke kai tayi ta kalli hadiman da suka rakota, a nutse kamar wata sarauniya ta furta "Zaku iya tafiya."
Saida suka rusuna kafin suka nufi hanyar fita, saida ta ji sun rufe k'ofar sannan ta kalli Umad dake tsaye bayan Haman k'ik'am, sauke k'arar data d'ora kan d'aya tayi ta gyara zamnta cikin yanayinta data saba tace "Me ye haka yallab'ai? Duk wannan shirin na miye? Me ye wani neman aure na da kuma mai tsaro?"
Haman kam mik'ewa yayi ya koma kusa da Umad yace "Zai miki bayani, duk shirin sa ne wannan."
Kamar a rashin sani ta mik'e tsaye tare da wurgawa Umad wata harara, takawa tayi har zuwa inda suke tsaye, da yatsa ta shiga masa k'wak'waran kashedin "Ka ga yallab'ai bana so, bana son wannan bibiyar da kake min, idan har gaske ne rayuwata na cikin had'ari, to ka barni na mutu bai dameka, amma ka sani idan har wani abu ya samu mahaifina a zuwan nan na ku, wallahi Allah sai ka gane kurenka."
Jujjuya d'an k'aramin bakinta tayi ta juya ta barsu tsaye baki sake da mamaki, bugo k'ofar da tayi bayan fitarta ne yasa Umad sakin wani lallausan murmushi yana girgiza, wai shi ta kalla duk da matsayinshi a gareta, da kuma matsayin da Allah ya masa kasancewarsa mai jiran gado, bata duba kasantuwarshi na malaminta ba ta kalleshi ta nunashi da yatsa sannan ta ce wai *zai gane kurensa*.
Shafa sumar kanshi yayi ya zauna kan kujera yana furta "Zakanya, ni ne zan gane kure na?"
Jinjina kai yayi yace "Zan gani."
Da sauri Haman ma ya zauna yana fad'in "Ka ga Umad dan Allah ka fad'a min me ye shirin ka? Ni wannan shirun da ka min ina bin uamrninka bana son shi wallahi."
Kallonshi yayi fuska a had'e yace "Zan fad'a maka, ka k'ara hak'uri kawai."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan zan jira."
Tana komawa d'aki ta samu Juman ta shiga fad'a tana fad'in "Mah ni wannan kayan sun isheni, cirewa zanyi."
Dariya tayi tace "Zaki fara sabawa da zaran kin zama sarauniya."
Kallonta tayi kamar zatayi kuka tace "Haba Mah, ki daina fad'a mana."
Jinjina mata kai tayi tace "Na ga wannan ranar Ayam, na ga haka a mafarkina, saidai nasan ba lallai mafarki ya zama gaske ba."
K'ala ba tace ba saida ta cire kayan nan ta d'auki wata sassauk'ar riga a cikin wanda aka kawo mata ta bacci ta saka, warware gajeran gashinta tayi wanda har yanzu yake tohowa ta sakeshi dan ya sha iska, kan gadon ta kwanta ta kalli Juman tace" Mah, yau na farko a rayuwata ina so na kwana tare da ke kaina a kan k'irjinki."
Dariya tayi tace" Baki da matsala gimbiyata, ni ma zan so hka duba da yau zan yi bacci a nutse hankalina kwance."
Da mamaki tace" Saboda me Mah?"
Cikin rad'a da fara'a a fuskarta tace" Saboda Umad na gidan nan, ganinshi ya bani k'arfin gwiwa, duba da shekarun dana fara had'uwa da shi da kuma yanzu."
Girgiza kai tayi ta buga hannunta akan cinya alamar" Haba mana Mah."
K'yalk'yalewa tayi da dariya tace" Da gaske nake fad'a miki."
Turo baki tayi tace" Ni da yanzu mana fad'a masa ya daina bibiyata, ni sam ban wani yarda da shi ba."
Kallon tuhuma ta mata tace" To da kike jin haka a game da shi, me ya hana ki fad'awa mahaifinki?"