Sashe 58
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban da" Suuuuuuiiiuuiuuuuu!" Ba abinda take ji a kunnenta, gashi dai idonta na kallonshi amma a zahirin gaskiya ba ganinshi take ba, a tsawace cikin b'acin rai yace" Ke wacece irin macece wai? Me yasa kike min haka Juman? Dan kin jima da gane rauni na a kan ki ne? Sau na wa ina k'ok'arin zama na k'warai a duniyar nan ? Amma ke d'in nan ke kika dakusar da ni, k'iyayya hauka ce? Dan ba kya so na sai a ka ce ke min komai da ranki yake so? Me ye haka wai Juman? Yanzu akan wanene dalili ne zaki hanani fita na ga halin da 'yarmu take ciki? Me yasa ba zaki bani damar aikata aiki k'waya d'aya tak na gari ba kafin mutuwa ta?"
D'agata yayi ya zauna gefenta yana dafe kanshi dake matsanancin ciwo kamar ana buga masa guduma, cikin sanyin murya yake fad'in" Bana son haka Juman, bana so ina muzguna miki, amma dayawancin lokuta ke kika kai ni bango, ban san me ya sa ba?"
Jiki a mace ta tashi zaune tana gyara rigarta, gefen fuskarta ta tab'a inda take jin kamar ya kumbura, cikin kuka mai raunin gaske tace" Baka so na Musail, da kana so na da baka min abubuwan da ka min ba, baka so na ni da Zafeera, Zafreen kad'ai kake so ita data d'auko hallayarka."
A marairaice ya kalleta yace" Juman ina sonku mana, ku fa na wa ne, me yasa ba zaki karanta ko da kad'an daga wani abun alkairi dana aikata a rayuwata ba? Tabbas na san na yi laifuka masu yawa, amma ki...."
Sai kuma ya dafe kanshi ya sunkuyar da shi k'asa yana rintse ido, kallonshi tayi sai kuma ta tab'e baki ta kawar da kanta.
Shi ya kasa cewa komai saboda bala'in da kansa ke mishi, ita kuma ta k'i magana saboda haushinsa da takaici, saida suka d'auki minti ashiri da biyar a haka babu mai k'wak'waran motsi, a hankali ya d'aga kanshi sama yna jan dogon numfashi kafin ya kalleta yace "Juman, na tabbata da zan yi fitar rai a gabanki ba zaki taimaka min da komai ba bare ki damu."
Jinjina kai yayi ya mik'e tsaye yace "Nagode Juman."
Kallonshi tayi da sauri jin yayi magana da wata murya, ganin ya juya zai fita yasa ta saurin fad'in "Godiya a kan me?"
Malalacin murmushi ya mata yace "A kan haifa min ababen soyuwata."
Yana fad'a ne ya juya zai fita sai kuma aka k'wank'wasa k'ofar, da sauri ya k'arasa tare da bud'ewa, Ayam ce ta shigo a wani mugun yanayi a d'imauce, da sauri ya rik'o damatsen hannayenta cike da kulawa yace "Zafeera, lafiya? Me y sameki?"
Murmushi ta k'ak'aro mai kama da kuka tana k'ara cukuikuiye pant d'inta, da gudu Juman ta k'araso ta rik'ota ita ma tana k'are mata kallo, hankali a matuk'ar tashe ta lumshe ido dan ita har ta ga abinda shi bai gani ba ta furta" Illa lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil."
Bud'e ido tayi ta kalleta ta matso hawaye da k'arfi tace" Ayam garin ya ya hka ta faru? Wa ye?"
Pik'i pik'i tayi da ido ta dukar da kanta tana duba jikinta, to me ta gani a nan ita kuma? Me take ma nufi da tambayarta? Jawota tayi zuwa cikin d'akin saida ta kai ta har bakin gado ta zaunar da ita, a lokacin ne Musail ya iya lura da yanda Ayam d'in take shi ma musamman ma tafiyarta.
Da sauri ya dafe kanshi ya k'arasa gaban gadon gefen Ayam din shi a ya zauna, rintse ido yayi sosai yana sake matse kan shi dake sarawa sosai.
Durk'usawa Juman tayi ta kama hannuwanta suna kallon juna tace "Ayam fad'a mana me ya faru da ke?"
Hawaye ne suka fara bin fuskarta kafin tace "Kiyi hak'uri Mah, ba laifina ba ne ni ma, tsautsayi ne."
Jan majina tayi sai Musail daya d'ago da sauri ya dubeta da kulawa yace "Waye Zafeera? A gidan nan ya ke?"
Fashewa tayi da kuka tana kallonshi ba tace komai ba, dafa kafad'arta yayi yace "Ki daure ki fad'a mana kinji, mu iyayenki ne, zamu bi miki hakk'inki ta ko wace hanya."
Jinjina kai Juman tayi tace "Hakane Ayam, ki fad'a mana kinji?"
Girgiza kai tayi cikin kuka tace "A'a Pah, ku barshi kawai na yafe mishi, bana so wani abu marar kyau ya faru tsakaninku, shi ma daga babbar masarauta yake, nasan ba halinsa b..."
D'aga mata hannu sarki Musail yayi alamar tayi shiru, dan har ya gane shaid'anin da yayi aika aikar nan, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauka dan dama tashin hankalin bai wuce ya ji waninsa ne ya karb'e budurcinta ba shi ba (Musail d'in nan fa akwai ayar tambaya kan shi).
Kama hannun Juman yayi suka nufi k'ofa, cikin rad'a yana kallonta yace "Karki d'aga hankalinki a kan wannan, ki dai taimaka mata ta ji dad'in jikinta."
Da mad'aukakin mamaki tace "Me? Kana so ka ce min babu wani matakin da zaka d'auka?"
K'asa k'asa yace "Babu, ki yi abinda na ce."
Cikin d'aga murya tace "Ka fad'i haka mana, saboda dama ba damuwarka ba ce ita d'in, to amma ka sani tana da uwa, ni ma kuma ina da iyaye sannan suna da iko a hannu, wallahi ko zan mutu saina k'watar mata 'yancinta."
Zai yi magana sai kuma ya kalli inda Ayam ke zaune, ganin ta k'ura musu ido ya sa shi jan hannunta suka fita a d'akin, bakin k'ofar suka tsaya inda yace" Wai ke me ya sa baki da hankali ne? Ni ne nan mahaifinta, kuma haka na ce kiyi dole ki yi."
A hassale ta fashe da kuka tace" Musail ka kuwa san me kake magana a kai? 'yarmu fa alamu sun nuna gyad'e aka mata kuma a cikin gidan nan, me yasa zamuyi shiru ba zamu nemi mai laifin sannan mu hukuntasu?"
Girgiza kai yayi ya ja tsaki kawai ya wuce ya barta nan tsaye, share hawayenta tayi ta bud'e k'ofar ta shiga ciki, bata yarda ta kalli Ayam ba ta wuce ban d'aki dan had'a mata ruwan da zata ji dad'in jikinta.
Ayam ma daga zaunen hawaye take yi na abinda ya sameta, da kuma abinda ta gani daga iyayen na ta, rashin jituwar yayi yawa haka, wanda ta san kuma k'iyayyar da mahaifiyarta ke wa mahaifinta ita ce silar komai, a yanzu kam bata ganin akwai wani abu da zatayi da zata siyawa mahaifinta wannan soyayyar da shekaru ashirin da shida suka kasa siya masa, tunda bata san yanayin zamansu ba ta b'angaren kyautatawa.
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*34*
Fitowa tayi daga ban d'akin ta kama wuyan hannunta ba tare data mata magana ba, zafin da ta ji a hannun na ta yasa ta dafa wuyanta, kallonta tayi kamar zata fashe da wani kukan tace "Ayam kin ji fa jikinki zafi, me yasa wai ba zaki fad'a mana wanda ya miki wannan abun ba? Ayam har fa cikin gidan mahaifinki haka ta faru."
A sanyaye sosai cike da kasala tace "Mahhhh! Karki damu kanki mana, ba abinda kike tunani ba ne."
Da kallon mamaki tace "Haba Ayam, ni fa na haifeki da cikina, kallo d'aya na miki nasan wani abu ya faru dake."
Cike da gajiyawa ta d'ora kanta a kafad'ar Juman tace "Mah zaune na ke so na yi."
Janta tayi zuwa ban d'akin tana fad'in "A'a ba zama zakiyi ba, mu je kiyi wanka."
Shagwab'ewa tayi tace "Amma kuma Mah sanyi nake ji."
Ba fara'a a fuskarta tace "Haka zaki hak'ura."
Suna shiga ban d'akin ta nuna mata bahon wankan tace "Cire kayanki ki zauna a ciki."
Cikin dubara ta fara aje pant d'inta da har lokacin yake mak'ale a hannunta gam, a sanyaye ta shiga zame rigar jikinta har ta cireta gaba d'aya, k'arasawa tayi ta d'an taka tudun wajen da bai kai tudun matakala ba sannan ta fara zura k'afarta ta dama.
Da sauri ta cire tana furta "Washhhh!"
Juyawa tayi ta kalli Mah data matso kusanta ta kamata, kakkare jikinta ta fara yi tana fad'in "Mah dama baki fita ba? Please ki fita ki barni, ni fa ba yarinya ba ce."
Ba ta kula da abinda ta ce ba sai kallon k'fafunta da take tace "Shiga ki zauna min."
Cikin d'ari d'ari ta sake zura k'afafun har ta fara k'ok'arin zaunawa a ciki, tana zaunawa ta ji wani fitsari na neman kubto mata saboda zafin da ta ji na ruwan, a firgice ta mik'e tsaye tana shirin yin magana Juman tace "Bana son wasa Ayam, zauna min a ciki."
Cikin kuka tace "Mah zafi wallahi, k'onewa zan yi."
Harara ta dalla mata da Ayam d'in bata tab'a tunanin zata iya yin ta ba sannan tace "Zaki zauna ko sai na jefaki da k'arfi?"
Da sauri ta rintse ido ta fara sunkuyawa a hankali har ta zauna ciki tsumdum, bakin bahon ta rik'e gam gam idonta a rufe duk da haka tana jin suna cika da hawaye, kasa zama tayi wuri d'aya haka ta dinga motsawa tana ta yan dabaru saboda rad'ad'i take ji sosai, sannu sannu kawai ta fara ji zafin ruwan na raguwa saida ta ji ta zauna daidai ba tare data motsa ba.
Lura da haka yasa Juman a dak'ile ta mik'o mata farin towel tace "Tashi ki d'aura wannan."
Karb'a tayi ta mik'e tsaye ta d'aura sannan ta fito, wata k'aramar buta mai ruwan gold ta k'arfe ta nuna mata tace "Sake kama min ruwa a nan."
A sangarce ta kalleta tace "Again?"
Ba alamar wasa tace "Yeah, zuwa safe kuma da kaina zan kaiki asibiti a tabbatar min da lafiyarki."
Numfashi ta sauke ita dai ta duk'a dan kama ruwan, wani sabulu ta mik'o mata na ruwa na kuma tsarki tace "Ki wanke da wannan."
Karb'a tayi ta matsa sabulun a hannunta sannan ta shiga wanke gabanta da kyau, tana idawa ta mik'e ganin Juman ta fita tana fad'in "Sai kiyi wankan tsarki."
*Sarki Musail* na fita daga d'akin kai tsaye b'angaren masaukin bak'in ya nufa, yana zuwa daidai k'ofar d'akin ya k'wank'wasa.