← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 86

Sashe 63

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin takaici ta kalli Haman da shi ma mamakin yanda Umad d'in ke mata yake, cike da masifa Ayam ta nuna shi da hannu tace "Wai a haka ne za ka aure ni? Kana ganin abinda ya ke min amma ba za ka d'auki mataki ba."

A fusace ta d'auke kai daga kallonshi ta furta "Banza kawai."

A tare suka zaro ido, Haman kam sai ya ji ta muzantashi, amma ya zai yi tunda yar Musail ce, Umad kam shafa sajenshi yayi sannan ya kuma tsareta da ido yace "Me za ki ci?"

Harara ta wurga masa tace "Ban sani ba."

Wani shak'iyin murmushi ya saki ya juyo ya kalli Juman kamar gunki da kuma Haman da ya d'an had'e fuska yace "Ku d'an ba mu guri sarauniyata, zan sa ta yi magana."

Jinjina kai Juman tayi tace "Shikenan."

Kallon Ayam tayi tace "Kar ki yi taurin kai kin ji, ki fad'a ma sa abinda ki ke so."

Da sauri ta kalleta tace "Mah, Mah kar ki fita, jira ni to..."

Ta yi maganar ta na sauko k'afafunta za ta fita ita ma, hannu ya sa ya dangwarar da ita ta koma zaune, a hassae ta kalleshi za ta yi magana, amma ganin ba ita ya ke kallo ba sai ta yi shiru tana hararanshi.

Ya na ganin fitarsu ya juyo kan ta tare da zaunawa gefenta, fuska a had'e yace "Me za ki ci?"

Kallonshi tayi idonta taf da k'walla tace "U...mad, ka san dai idan na maka Allah ya isa za ta bi ka ko?"

Zuba idonshi yayi cikin na ta kamar zai yi dariya, sai kuma ya gyar zamanshi da kyau saboda hango irin abinda zai mata yanzun, cike da isa yace "Na sani, amma ba zan bari ki yi ba, idan ma kin yi babu abinda za ta min."

Da alamar tambaya tace "Haka ka ce?"

Da ido ya mata alamar um! Rumgume hannaye ta yi a k'irji tace "Shikenan ka je na bar ka da..."

Shak'o rigarta ya yi da k'arfi hakan yasa ta kawo masa karo goshinsu ya had'e, kafin ta san dalilin da ya sa ya yi haka sai kuma ta ji d'umi a cikin bakinta, dan idonta rufewa sukayi sanda goshinsu ya kauru.

Tsutsar da aka mata a baki ne ya tabbatar mata da lallai fa bakinshi ne a na ta bakin, hannayenta biyu ta d'ora a k'irjinshi sannan ta sa k'arfi dan ta tureshi, gam ta ji ya sake nane mata ya lik'e, zaro ido tayi ta fara tureshi da k'arfi tana "Um..umum..umm..."

Irin tsutsar da ya ke mata kamar ta gayya dan sai ya yi kamar zai cire hak'orinta, sai kuma ya cabki harshenta ya na lalubar mata dadashi, saida ta ji leb'enta na zafi alamar azaba ta saki jikinta gaba d'aya ta bud'e idonta da ta lumshe, sharrr hawaye suka sauko a kuncinta, bud'e idonshi yayi da suka rikid'e suka zama ja sai rufewa suke k'arfi da yaji, ido cikin ido suka had'a ido hakan yasa ta kuma lumshe idonta ta masa alamar ka yi hak'uri yallab'ai.

Samun kanshi yayi da saisaita tsutsar da ya ke mata, a hankali a hankali ya fara mata yanzu har saida ita kan ta ta fara jin tasirin abun a jikinta yanda ta sakar masa bakin ta daina k'ok'arin k'wacewa, sannan ta lumshe idonta ruf tana sauke numfashi daga k'asan mak'oshinta.

Lis ya mata wanda hakan duk ya galabaitar da su, yana sakin bakinta mik'ewa yayi ya shiga takawa da mugun sauri zai bar d'akin har had'a k'afa yake, ita ma idonta a rufe ta jingina a gadon dan haka bata san ya fita ba, numfashi take saukewa sannu sannu har ta jawo pillow ta rumgume tayi shiru.

Wurin ranar asibiti su ka yi shitare da Juman da sarki Musail dake yawan lek'owa, sallah kad'ai take sauka daga gadon tayi ta koma ta zauna, abinda kuma Juman ba ta sani ba shi ne, sarki Musail da kanshi ya shiga madafa ya bayar da umarnin a dafa musu abinci sannan jakadiyarsa ta tsaya kan girkin, tare da alk'awarin idan aka samu matsala tabbas zai ganawa mutum azaba, amma sanda aka kawo abincin dukansu d'ari d'ari suke da abincin, saida ya d'auki cokali ya sa a bakinshi ya ci ta tabbatar ya had'e sannan kad'ai ta zuba ta fara ci, saida ta cinye da tsawon minti biyar kafin ta zuba ta ba wa Ayam.

Dariya yayi kawai yana girgiza kan shi sannan ya fice, sai yamma sosai aka sallameta inda suka koma masarauta a mota.

*Da dare*

A d'akin Ayam Juman ta kwanta bayan Ayam d'in ta yi wanka ta saka kayan bacci masu laushi, lafiya lau suka kwanta kuma gida ya yi shiru alamar ko wa ya kwanta dan ya huta ma ran shi.

*03:00* wata mummunar k'arar fashewar tukunyar gas ta sa duka mutanen gida farkawa a kid'ime, kuma daga d'akin abinci wannan abu ya fara, saidai a lokacin da turmutsutsun mutane ya fara cika gidan, sai kuma wutar ke dad'a yad'uwa a sauran sassa daban, a cikin haka kuma aka ji wata k'ara mai kama da jiniyar motar asibiti ta karad'e gidan wacce ke nuna lallai wasu sun karya tsaron gidan sun hauro ciki, sai kowa ya k'ara rikicewa ana ta neman mafaka inda mazan suka shiga neman makamai dan kare kansu da iyalensu da kuma sarkinsu.

Wad'anda ke cikin falon k'arar harbin bindiga suka ji daga waje alamar fa yak'i ne ke faruwa, kafin ka ce me an fara turo k'ofar falon, duk matan ihu suka saka suna b'uya mazan kuma suka sake rik'e makamansu a hannu suna jiran kar ta kwana.

Ana bud'e k'ofar aka shiga harba bindogogi ana ba da wuta ba kakk'autawa, sai ga mutanen nan ne dake rufe da fuskokinsu da bak'ak'en kaya sun shigo sun fi su ashirin.

Da azama suka shiga falon tre da da tsayawa waje d'aya, wanda ke gabansu da ya nuna shi ne shugaban tafiyar ne yace "Ku duba mana ko ina dan mu samota, ku yi aiki da jiki."

Da azama suka shiga sassarfa suna fad'awa duk wani wuri da suka san d'aki ne, jim kad'an suke dawowa suna sanar da shi babu kowa a d'akin, hakan yasa ya kalli matan da suka rakub'e dan duk sun harbe mazan yace" Ke zo nan."

Jiki na rawa wacce ya kira ta rarrafo ta durk'ushe gabanshi, cikin kakkausan murya yace" Ina Gimbiya Zafeera?"

Jiki na kakkarwa tace" Ban...ban...sani...ba"

Wani mahaukacin mari ya wanka mata a tsawace yace "Za ki fad'a min ko sai na kasheki?"

Ya fad'a yana nunata da bakin bindiga, fashewa tayi da kuka jiki na sake b'ari ta nuna masa kusurwar tace "Ta can ne."

Juyawa yayi ya kalli yaran da suka dawo masa yace "Mu je."

Tunkarar k'ofar suka yi duk da bindigoginsu a hannu, daga gefensu d'aya daga cikin yaran Umad yayi kukan kura ya naushe shi a baki, lokaci d'aya ya kama hannunshi mai bindigar ya murd'e tare da d'ora hannunshi daidai kunamar bindigar, kafin ya ankara ya saki alburushi ga d'aya mutumin dake gefen wannan, Haman da shi ma suka fito tare yana rik'e da bindigarshi da azama ya tashi kan yaran biyu hakan ya rage sai shugaban na su.

Umad ya saitashi da bakin bindiga kenan sai kuma wasu yaran suka fito wad'anda suka bazu neman Ayam, hakan yasa shi da Haman suka b'uya a k'asan matakalar da zata kai ka d'akin Juman, wuta suka dinga ba wa junansu aka dinga ba ta kashi, cikin taimakon ubangiji duk suka kashe yaran inda shugaban ya k'arasa shigewa wajensu Ayam.

Fitowa sukayi daga malafarsu suna kallon juna Umad yace "Ka gane, wad'annan mata ka tsaya tare da su, zan je na ji da wan...ahhhhhhh."

K'ara ya saki sakamakon harbinsa da wani ya yi a bayanshi ga kafad'a, da wani irin salo da k'warewa Haman ya saita kan mutumin ya tasheshi a aiki.

Da sauri ya kalli Umad daya rufe ido hannunshi na jini yace" Umad, kana lafiya?"

Matse bakinshi yayi sosai ya daure duk da rad'ad'in da yake ji ya bud'a ido ya kalleshi yace" Lafiya lau na ke, zan je na duba kar ya cutar da ita."

Cike da damuwa Haman yace" Ba za ka iya ba Umad, ka bari ni na je."

A hassale Umad ya kalleshi yace"...

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*37*

A hassale yace "Zan iya mana, zan iya, zan iya."

Da gudu ya juya ya nufi hanyar d'akin na ta, Haman kuma k'arasawa yayi kusa da hadiman nan da suka lab'e bayan kujeru.

Daga waje kuma har yanzu sara da suka ake da harbi tsakanin dakarun sarki Musail da maharan nan, inda cikin k'warewa duk su ka yi nasarar kashe maharan sannan rabin su suka tunkari b'angaren sarki Musail, wasun su kuma suka shigo falon dan ba wa sarki da iyalinshi kariya.

Kasancewar Adah wanda ya san sarki Musail farin sani ne, sai ga shi cikin tawagar wad'anda suka shiga falon da kiyyar kare iyalinshi, yanda Haman ya saitasu da bakin bindiga yasa Adah saurin d'aga hannayenshi yace "Kar ka yi harbi, mu ne."

D'auke bindigar yayi sannan ya matso kusa da su yana fad'in "Wannan harin fa? Daga ina haka?"

Da sauri Adah yace "Ba wannan lokacin, dole mu gaggauta ba wa iyalin mai martaba kariya kafin su cimma su."

Sama ya tunkara zai hau tare da mabiyanshi sai Haman yace "Ina ga suna d'akin gimbiya Zafeera."

Juyowa Adah yayi ya kalleshi sai kuma ya kalli wani yace "Ku biyu ku je d'akin gimbiya Zafreen, ku tabbatar babu abinda ya sameta, akwa mab'oya ta sirri a d'akin, ku yi k'ok'arin dubata a ko ina."

Da gudu gudu suka nufi inda ya fad'a musu suna kuma rik'e makamansu a hannu, shi kuma tare da wasu suka nufi d'akin Ayam d'in dan ba ta kariya.
Chapter 63 · 0% Book details