Sashe 33
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mad'aukakin mamaki ta kalleshi tace" Wudar, dama zaka iya hukunta ni?"
Da mamaki Umad ya kalleta jin ta ambace shi da sunanshi wanda bai tab'a jin haka ba, Haman da ke neman haukacewa daga zaune shi ma tsatsaresu kawai yake da ido yana neman dalilin da zai tashe shi a wurin nan kafin yarinyar nan ta masa *bankad'a*, dan ya kula daga cikin dalilin da yasa kowa ke nemanta akwai son fallasa abinda ke b'oye, tunda gashi har ta zak'ulo sirrin daya b'oye shekara da shekaru.
Sarki Wudar kam ranshi b'ace yace "Ko waye a duniyar nan zan hukunta shi indai akan matata ce uwar d'ana k'wallin k'wal a duniya."
Malaacin murmushi tayi ta kalli Ayam sama da k'asa tace "Har wannan ma zaka iya hukuntata akan Kossam?"
Wani abu Umad ya ji ya soki zuciyarshi da yasa shi wurga mata wani kakkausan kallo, Ayam kam mik'ewa tayi tsaye ta kalleta ta kalli sarki Wudar tace "Me kike nufi da abinda kika fad'a?"
A wulak'ance Joy ta gyara zamanta tace "Ina nufin..."
Tsawar da sarki ya daka mata tasa ta yin shiru ta kalleshi tana hararenshi, kallon su Umad yayi da Ayam yace "Ku jira a waje kun ji."
A hassale Umad ya mik'e ya fita Haman da Ayam kuma su'a bayanshi, suna fita Haman kam bai yarda ya tsaya dan shi ma a tsorace yake, motarshi ya shiga ya tayar ya bar gidan, Umad na tsaye yana hangenshi har ya fita a gidan, bayanshi Ayam ta tsaya tace" Me nake yi a masarautarku?"
A hankali ya juyo ya kalleta, kawae da kai yayi a gadarance yace "A yanzu dai kam ban sani ba ni ma, tabbas mahaifina ma yana cikin masu nemanki, sai dai bansan me ye manufarsa a kan ki ba, mu jira lokaci kad'an kamar yanda ya fad'a mu ga me zai bayyana mana."
Da mamaki a fuskarta tace "Ko da manufarsa zata iya saka rayuwata a had'ari kana nufin mu zuba ido har sai zai aiwatar zamu sani?"
Jinjina kai yayi ya juya mata baya yace "Kusan haka?"
Cikin jin haushi ta koma ta gabanshi ta fuskance shi bakinta d'auke da masifa da niyyar tace "Wai kai wanene? Me kake ji da shi? Kai bana son iskanci ka ji ko, ka d'auke ni a nan ka mayar da ni garina."
Amma kuma yana saka k'ananan idonshi masu sirkin ja a cikin na ta sai kawai ta sunkuyar da kan ta muryarta a tausashe sosai tace "Kana yi kamar baka damu da rayuwata ba yallab'ai, idan hakane to ka maidani garinmu."
Wata dariyar rainin hankali ya mata yace "Damuwa da rayuwarki? Oho na gane! Wato so kike nima kamar sauran marasa aikin yi, na dinga binki sau da k'afa ina washe miki baki, ina nuna miki babu kowa sai ke ko? To ba zai yiwu ba, ni ba sakarai bane."
Da sauri ta kalli fuskarshi tace "Sakarci? Hakan wai shi ne sakarci? Yanzu idan da ni k'anwarka ce zaka yarda kana kallo mutanen da ban sani ba suna neman juya min rayuwata? Ko kuma da soyayua muke da kai zaka yarda a rabamu ne? Da kuma ni matarka ce fa a ce z..."
A mugun tsawace yace "Shiru malama."
Zabura tayi tare da rintse ido gam ta k'ame wuri d'aya, k'urawa fuskarta ido yayi yanayin firgicin data nuna sai ya ji kamar yayi ta kallonta, sanyayyan murmushi ya saki a b'oye a zahiri kuma ya had'e fuska yace "Abinda na fad'a miki jiya ma baki yarda da ni ba, ya kike so na yi kenan?"
A take ta bud'a idonta tace "Ka kaini wajen iyaye na to."
A shek'e ya kalleta yace "Wane daga ciki?"
Kallonshi tayi da fari da mamakin tambayar, sai kuma ta kawar da kai tace "Iyayena, wanda suka raine ni har na girma."
Shi ma kawar da kan yayi yace "Suna cikin tsaro a inda suke, rayuwarsu na cikin had'ari, ba zan iya nuna miki su ba."
Da mamaki tace "Me ya sa rayuwarsu a had'arin? Me suka aikata?"
Kallon fuskarta yayi ya saki murmushi mai ciwo, kamo sark'ar wuyanta yayi yace "Ina kika samu wannan?"
Kallon hannunshi tayi dake rik'e da sark'ar tace "Iyaye na suka bani."
"Tun yaushe?" Ya tambaya yana tsareta da ido, ba alamar tabbaci a tare da ita tace "Ban sani ba nima, na ganta a wuyana ko da nayi wayo."
Murmushi yayi yace "Wannan sark'ar a ranar da aka haifeki aka saka miki ita, Ayam karki dameni da son ganin marik'anki a yanzu, duk tambayoyin da kike da muradin yi musu kina da amsoshinsu idan kika aje hankalinki, ki nutsu ki fara tariyar alak'arki da su, dan su basu d'aukeki a 'yar da suka haifa ba sai yar da sarauniyarsu ta haifa, ma'ana gimbiyarsu."
Matsawa yayi daf da ita ya saki sark'ar yace" Kina son ganin abun mamaki a rayuwa?"
Idonta ta zuba cikin na shi tace" Ina son abubuwan mamaki a rayuwa, idan ban k'aru da ilimi ba na kan samu alfanu a tare da hakan."
Jinjina kai yayi yace" Idan kowa yayi bacci zan tasheki sai mu je wani wuri."
Da mamaki tace" Me yasa sai kowa yayi bacci? Me yasa baka son kulani a gaban mutane?"
Juyawa yayi yana fad'in" Saboda tsaro ne." Da kallo ta bishi har ya shiga wani b'angaren da take tunanin na shi ne.
A ciki kuma suna fita a hassale sarki Wudar ya rik'o hannun Joy yace" Me kike so ki tabbatar a haka? Me ye na k'ok'arin fad'a musu abinda ba yanzu na ke da niyyar fallasa shi ba."
Jujjuya masa baki tayi ta fizge hannunta tace" Wannan kuma kai ka jiyo, amma ka sani inhar zaka dinga nuna ban da mahimmanci yanzu a gareka to abinda zai dinga faruwa kenan."
Nunata yayi kamar zai tsone mata ido yace" Ki sani ke baki isa ki lalata min shirina akan Zafeera ba, kina gani akan idonki zan aureta kuma babu yanda zakiyi."
Rai b'ace tace" To ko ka shirya hujojjin da zasu kareka daga zargi da jifan mutane, dan tabbas zasu san meye alak'ata da kai, sannan su san bayani a game da sabon yarimansu dake hanyar shigow duniyar."
Tab'e baki yayi yace" Ki sani zaki burmawa cikinki wuk'a ne, na farko ke ce zaune a gidana, na biyu babu wanda ya tab'a gani na a b'angaren ki musamman da dare, na uku kowa dake gidan nan ya shaida irin shigar da kike yi, sannan ki tuna wani abu! Gimbiya Zafeera ta fara bayyana mana wani abun wanda shi ma zai iya sake jefaki bakin al'ummata."
Yana fad'a ya juya ya bi ta k'ofar da zat sadashi da fadarshi dan gudanar da mulkinshi.
*Khazira*
Sarki Musail na shigowa suka had'a ido da Bukhatir, cak ya tsaya ya furta "Bukhatir?"
Mik'ewa Bukhatir yayi yana murmushin munafurci yace "Ranka shi dad'e, barka da shigowa."
Takawa sarki Musail yayi yana k'arasa shiga ciki yana fad'in "Bukhatir, me ya kawoka gida na? Me kake yi a nan? Dama kai ne bak'on da ya zo?"
Dhurani ne ya kalli sarki Musail yace "Shugaba me yake faruwa? Ka san shi ne dama?"
Kallon Dhurani kawai yayi bai ce komai ba ya sake matsawa kusa da Bikhatir, a kausashe yace "Me ya kawoka nan Bukhatir?"
A ladabce dan ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace "...
*Kuyi hak'uri da wannan, na so ya fi haka wallahi.*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*19*
A ladabce dan san ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace "Sarki na, mhe zai hana ka zauna sai mu tattauna."
A wulak'ance sarki Musail ya nuna kan shi yace "Da wa? Da ni? Ai har abada, ka manta rabuwarmu da kai ne?"
Murmushi Bikhatir yayi ya sake yin k'asa da kan shi yan tuna rabuwarsu ta k'arshe wacce basu sake had'uwar ba sai yau kuma yanzu, shekarun da suka gabata a baya gaba da gaba kuma ido cikin ido Bukhatir ya kalli sarki Musail yace _" Na yarda kayi nasara a kai na a kan ta, ban damu ba ko dan kana da mulki a hannunka ne kayi nasara a kai na, amma ka sani daga yanzu ni da kai gaba ce a tsakaninmu dan ka rabani da matar da nake da burin ta zama ta wa, shi kan shi wanda take so a matsayin abokin gaba na dinga kallonshi, kuma a kowace wucewar rana neman hanyar da zan kassarashi nake, na yi farin cikin mutuwarsa fiye da tunaninka, amma yanzu mutuwarka ita ce abar harina."_
Sanyayyar murmushi ya kuma sako dan sai yanzu kalaman suka bashi dariya ma, sarki Musail ma murmushin yayi yace" Da alama ka tuna, dan haka ka gaggauta barin nan kafin na sa a cire maka kai, komata ka shigo."
Dhurani ne ya sunkuya daf da kunnenshi yace" Ina ga fa zai fi mu saurare shi, haka kawai ba zai zo ba idan babi dalili mai k'arfi."
Kallon shi yayi yace" Malami ina so ka sani duk wani abu da zai min barazana da rayuwata babu ni babu shi, ka fi kowa sanin haka."
Kallonsu Bukhatir yayi yace" A gafarce ni ranka shi dad'e, maganar dake tafe da ni mai mahimmanci ce, magana ce akan gimbiya Zafeera, na san zaka so jin inda take? Tare da kuma wa take?"
Girgiza kai sarki yayi yace" Ta ya zan iya yarda da kai?"
Nuna masa k'ofa yayi yace" Gimbiya Zafreen, ai ta dawo cikin k'oshin lafiya, ko bata fad'a maka tare suke da yar uwarta a can ba a hannu na?"
Shiru sarki Musail yayi yana kallon fuskar Bukhatir, ya jima haka alamar yana ta tunani kafin ya jinjina kai ya taka a tsanake, wata k'ofa wacce wanda mai kallo zai yi tunanin ban d'aki ce ya bud'e ya nunawa Bukhatir yace" Akwai buk'atar muyi sirri?"
Da girmamawa yace" Me zai hana."