Sashe 47
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Waye shi Mah?" Ta fad'a a sanyaye, d'an yak'e ta mata kafin tace "Ayam Bukhatir d'an uwana ne, mahaifina shi ne gaba da mahaifinsa, ni kad'ai ce 'yar da suka haifa mace bayan shekarun da suka share a tare babu haihuwa, mahaifin Bukhatir mutumin kirki ne wanda mulkin yayansa baya gabansa, saidai Bukhatir tun yana k'arami yake sha'awar mulki, sanda suka haifeni sai ya yarda lallai idan na girma zan iya hawa kujerar mahaifina, saboda kuwa mu a wajenmu mace ma tana yin mulki sai idan bata buk'ata, bayan wani lokaci Bukhatir ya zo min da tayin soyayyarsa, amma ban karb'a ba saboda bai min ba, bana sha'awar mulki kuma bana son mai tsananin son mulki."
Da mamaki Ayam tace" To Mah e yasa ya saceni ya kaini gidansa? Guduwa fa na yi bai sani ba, sanda na fahimci babu hankalin kowa a kai na na wa hadiman daya had'ani da su dabara na shige boot d'in motar bak'in da suka zo masa a lokacin."
Girgiza kai tayi tace" A gaskiya ban sani ba, ban san dalilin da yasa ya saceki ba,saidai nasan lokacin da mahaifinki ya nemi aurena sun samu matsala har sukayi musayar yawu, watak'ila ko akan hakan yake son rama wani abu da aka masa."
A hankali tace" To amma Mah, idan har kunyi soyayya irin haka da mahaifina, me yasa ya manta da komai ya jefaki a magark'ama saboda ni?"
Dariya Juman tayi har saida hak'oranta sirara masu kama dana Ayam d'in suka bayyana, girgiza kai tayi tace" Ayam kenan, yarinya ce ke har yanzu."
Da mamaki tace" Kamar ya Mah, ni fa na girma."
Ta fad'a tana kumburo baki, dariya ta sake yi tace" Ayam ba haka abun yake ba, a shekara ta 1985 sarakunan gargajiya sunyi taro na musamman dan sake hab'aka zumunci da kawar da bambamce bambamce a tsakanin k'asashen, sarkin Egypt wato mahaifina, da sarkin Khazira wato mahaifinki, da kuma sauran sarakuna daga ciki har da sarki Wudar na Giobarh, duka sun hallara a wannan babban taron wanda mahaifina shi ne mai alhakin sauke bak'in, ma'ana a k'asarmu aka gudanar da taron, kwana uku aka d'auka ana wasanni kala daban daban, a na ci a na sha cikin farin ciki da annashuwa, b'angare d'aya kuma sarakuna na gudanar da abinda ya kawosu."
Numfasawa tayi ta d'an gyara k'afarta data tank'washe sannan ta ci gaba da fad'in" A kwana ukun da akayi na kamu da soyayyar wani d'an baiwa, kinsan me yasa na kirashi da d'an baiwa? Saboda shine zakin daya fara sace zuciyata, da kallo d'aya ya birgeni ya kuma shiga zuciyata, lokacin da nake jin dad'in satar kallonsa ina tunanin hanyar da zan fad'a masa abinda ke zuciyata kafin su bar k'asar, sai ya turo da k'aramin k'aninsa mai shekara shida a duniya ya fad'a min wai shi ma yan so na."
Damk'e hannun Ayam tayi sosai tana jijjigawa cike da farin ciki tace" Kin kuwa san irin farin cikin da na kwana ina yi a ranar? Na ji kamar duniya aka bani da komai dake cikinta, saidai kash! Ban tab'a tunanin wannan bak'in taro ne a gareni ba saida Musail ya shigo rayuwata, ki gafarceni idan kin ji ba dad'i Ayam saboda soyayyar d'a da uba, amma dai tabbas ban ji dad'i ba."
A sanyaye Ayam tace" Me ya faru Mah?"
Girgiza mata kai tayi tace" A'a Ayam, bana so daga had'uwarmu na zauna na yi ta fad'a miki mugayen halayen mutanen dake zagaye da ke."
Rik'o hannunta tayi tace" Please Mah, ki daure ki fad'a min komai, na fad'a miki mutanen da ban sani ba suna kawo min farmaki ta hanyar rikita min k'wak'walwa, ina so na san komai daga gareki, hakan shi ne zai cire min kokonto na akan kowa da komai."
Girgiza kai tayi tana sako da hawaye a idonta tace" Ba zan iya fad'a miki wannan ba Ayam, ki gafarce ni."
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tace" To shikenan na ji, amma ki fad'a min waye wanda kika so a zuciyarki? Sannan ki fad'a min me ya hana aurenku?"
Murmushi tayi tace" Ayam ai idan na fad'a miki abinda ya hana aurenmu an gudu ba'a tsira ba kenan, dan abinda ya hana auren na mu shi ne abinda bana son fad'a miki."
Jinjina kai ta sake yi tace" To na ji, waye shi?"
Saida ta saki sanyayyan murmushi tace" Sunansa *Urab*, babban d'an sarki Wudar."
Zazzaro ido tayi tace" Sarki Wudar Mah?"
Jinjina kai tayi tace" E, d'an sarki Wudar."
Da mamaki a fuskarta tace" Hakan na nufin yaya ne ga yallab'ai Umad? Dama 'ya'yan sarki biyu ne?"
Gyad'a mata kai tayi tace" E, su biyu, Umad d'in ai shine k'aramin k'aninsa da nake fad'a miki."
Juyar da kanta tayi gefe a ladabce tace" Kenan yallab'ai Umad sosai ya sanni ba sanin shanun talla ba? Kenan tabbas saboda ni ya je makarantar nan? Kuma mahaifinsa ya san wacece ni, amma kuma duk da haka yake cewa yana son..."
Shirun da tayi yasa Juman saurin fad'in" Yake son me? Kin had'u dasu dukansu? Ta ya ya?"
Girgiza kai tayi dan bata san me hakan zai janyo ba kafin tace" Ba komai Mah, na zauna tare da su na kwana biyu."
Tsaf ta kwashe abinda ya faru ta fad'a mata, sai daga bisani kuma ta kalleta a tsanake tace" Mah, to ina shi yayan yallab'ai d'in yake? Ko gidansu dana zauna ban ji ko da labarinshi ba."
Kallonta tayi sosai ita ma a tsanake tace" Ya rasu shekara ashirin da hud'u da suka gabata."
Dafe k'irji tayi tamkar mahaifinta aka ce ya mutu tace" Me?"
Jinjina mata kai tayi alamar e, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "Amma ta ya Mah?"
Girgiza mata kai tayi tace "Kinga yanzu dai manta da wannan, bana so ki sa kanki a damuwa, yanzu bani labari game dake?"
"Kamar me kenan Mah?" Ta fad'a kamar mai rad'a, jan hancinta tayi tace "Kamar k'awayenki, samarinki, karatunki, matsayin addininki a gareki."
Bushewa tayi da dariya tace "Mah, a b'angaren karatu na dai kam zan iya miki albishir da ce wa tun dana fara daga ajin farko zuwa inda nake yanzu, indai za'ayi jarabawa to ni ke zuwa farko, k'ok'ari na ma yasa har idon gwamnati ya zo kai na suka dinga d'aukar nauyina."
Rausayawa tayi ta ci gaba da fad'in" Kawaye kuma ni kam ban da tsayayya, duk k'awayen makaranta ne, da zaran mun rabu to shikenan ni da su sai ko kan hanya idan an had'u."
Cikin jin kunya tace" samari kuma...ban tab'a yi ba Mah, ko na wasa."
Jin tayi shiru yasa Juman fad'in" To addininki fa? Me ye matsayinsa a gunki?"
Waina idonta tayi tace"...
*In shaa Allah sai litinin kuma*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:39 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*27*
Waina idonta tayi tace "Mah, babu wani addini da nake cikinshi a baya, dan abinda su Mah (Habbee) ke bautawa ina ganin hakan kamar b'atan basira, a gani na ba ta yanda zan sassak'a ice da hannu na sannan na ce gareshi zan nemi biyan buk'atoci na, a k'arshe ma sai ta kai da kud'i kad'an zaka iya siyanshi a kasuwar sabah sannan ka kai cikin gidanka, sai nake ganin hakan gaskiya bai dace da mutum mai hankali da tunani ba, duk da ban rayu da su rayuwa mai tsayi ba saboda makarantar kwana dana dinga yi, amma dai a haka suna min fad'an na samawa rayuwata madogara, dan rayuwa babu addini tamkar rayuwa ne babu alk'ibla, amma kullum sai na fad'a musu zan yi idan har na samu addinin daya dace, dan kullum a jikina da kuma hangena nake samun yak'ini tabbas akwai wani buwayi gagara misali wanda ya cancanci dukanin mai rai da numfashi yayi bautarsa gareshi, and...a k'arshe dai na samu ta dalilin yallab'ai Umad, yana bautawa ubangijin daya dace, gareshi ni ma na karb'a, saidai yanayi yasa babu abinda ya koyar dani game da addinin, amma kakata ta koyar dani wankan tsarki, sannan ta fara min bayani akan rukunan musulunci guda biyar."
Cike da farin ciki marar misaltuwa Juman ta rumgumota tace" Wow! Masha Allah, a gaskiya na ji dad'in haka sosai, sai kuma yanzu na fahimci kuskuren da na yi saboda rufewar da ido na sukayi na son ganin na ceci rayuwar ki, sam na manta da madogararki, na manta nayi tunani akan jigon rayuwarki, zan nemi gafarar ubangiji na kuskure na, sannan daga yanzu zan fara d'oraki daga inda kika tsaya."
Cikin jin dad'i ita ma tace" Nagode Mah."
Da sauri kuma tace" Dakata, dakata, na ji kin ce kakarki? Wace kakarki kenan?"
K'urawa fuskarta ido tayi tace" Mahaifiyarki, sarauniyar Egypt."
Zaro ido tayi tace" Ina kika had'u da su Ayam? Iyaye na fa kika ce?"
Jinjina kai tayi tace" Yallab'ai Umad ne ya kai ni wajensu."
Da mamaki tace" Umad? Wai me yake nema ne?"
Girgiza kai tayi tace" Ban sani ba ni ma Mah, amma ni yanzu babu ruwana da shi, dan yau da zan taho na shiga d'akinshi sai na samu wasu abubuwa da ke nuni da kamar wani ne ke shirya mana wani abu, ko kuma dai ana aiki a kan mu."
Jim tayi tana tunani kafi' daga bisani tace" To ko dai shi ma..."
Sai kuma tayi shiru, da sauri Ayam tace" Shi ma me? Mah ki fad'a min idan kinsan wani abu a kan shi."
Girgiza kai tayi idonta na kallon k'asa tace" Um um! Ba lallai abinda nake tunani ba ya zama gaskiya."
Cikin zumud'i tace" Duk da haka Mah fad'a min."
Kallonta tayi tace" Kin gane ko? Zuciyata ce na ji ta raya min wasu abubuwa a game da yawan maganarsa da na ji kinyi, uwa uba kuma kika ce ya had'aki da iyayena, ina tunanin to ko dai shi ma ya shiga aiki irin na yayansa Urab ne?"
Kallon tuhuma Ayam ta mata tace" Mah, tambayarki fa nayi kuma ke ma kin tambayeni, wane aiki kenan?"
Cikin rashin tabbas tace" Jami'in sirri ne, a waccen lokacin jami'in sirri ne dake binciken manyan laifuka na k'asa."