← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 86

Sashe 4

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta kai hannunta ta d'aga doguwar sark'ar gwal d'in dake wuyan sarauniyar, 'yar k'aramar sark'ar dake wuyanta mai bak'in zare da wani k'aramin zagaye kamar ziro, cike da al'ajabi Zafreen tace "Maa, wannan sark'ar ai jabu ce, ina ta asalin?"

Wani masifaffen murd'awa cikin sarauniya yayi inda ta zaro idonta kamar zasu fad'o, a take ta tambayi kan ta "Ya akayi ta gane?"

Dan ko sarki Musail bai tab'a lura da hakan ba, duk dai ma yanzu ya zama bugagge kullum a shaye yake. B'oyayyen numfashi ta sauke tana tunanin abinda zata fad'a mata, dan bata so asirinta ya tonu a yanzun, kafin ta ce wani abu Zafreen ta sake fad'in" Maa dake nake magana fa, ina sark'arki mai daraja take?"

Cikin inda inda tace" Am.. Zafreen, waccen sark'ar ta b'ata shekarar da mukayi tafi da mahaifinki wanda aka mana fashi a hanya, kinsan kuma sark'a ce mai darajar gaske, b'atanta 脿 wuyana zai tashi hankalin 'yan k'asar nan, shiyasa da taimakon malami Dhurani aka had'a min wannan d'in."

Marairaicewa tayi kamar zatayi hawaye tace" Na rok'eki 'yata karki bari sarki ko wani ya ji labarin nan, karki fad'awa kowa kinji."

Sam fuskar Zafreen bai nuna alamun gamsuwa da maganar mahaifiyar ta ta ba, sai kawai ta girgiza kai ta juya ta fice 脿 d'akin, da kallo ta bita saida ta ga b'acewarta kad'ai ta sauke ajiyar zuciya.

*Alhamdulillah*

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *87-62-53-02* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai *Samira*._
01/01/2022 脿 11:30 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*3*

*29/12/2020*

*Larhjadin*

Da gudu ta fito daga motar ta tunkari dattijuwar dake tsaye da alama jiranta take, ihu ta saki tana fad'in "Mommaaaaa."

Da fara'a matar ta tunkareta, amma sarautar Allah kawai sa茂 ta rusuna dake nuna girmamawa ga matashiyar, cak yarinyar ta tsaya ta had'e fuska cikin shagwab'a tace "Momma, ya kike abu haka kamar zaki rusuna min?"

Cikin dubara da wayancewa ta saki murmushi tana mai dafa kafad'arta tace "Haba dai *princezna* (gimbiya), abu ne naji na taka k'afata."

Dariya budurwar tayi ta rumgume maman na ta tana fad'in "Momma na nayi kewarki."

"Ni ma haka." Ta fad'a tana lumshe ido wani dad'i na ratsata sakamakon had'a jikinta da tayi da sanyin idaniyar ta ta, sun jima haka kafin su raba jikinsu, kallonta dattijuwar ta dinga yi daga k'asa har sama.

Dogon wando ne matsatse bak'i sai farar riga mai k'ananan hannu, takalminta flat ne masu d'amara fara, k'aramar jaka ce a kafad'arta bak'a sai hular dake kanta ta sanyi, baya ga haka babu wani abu mai kama da kwalliya ko ado a tare da ita bayan wata siririyar sark'a dake wuyanta mai kalar d'anyan gwal sai wani zagaye kamar ziro.

Kyab'e fuska matar tayi tace "Gimbiya ta, ya naga kin k'ara ramewa? Dubeki fa."

Dariya tayi data bayyanar da 'yan hak'oranta na gaba kamar na b'era tace "Momma kin manta karatu na ne? Ina shekarata ta k'arshe ne, shiyasa na dage nake so na ga na fito a major ta foresti猫re."

Girgiza kai matar tayi tace "K'iriniya irin ta ki sai nema gimbiya."

K'yalk'yakewa tayi da dariya ta dafa kafad'arta tana fad'in "Gimbiya gibimya kullum, wai ni Momma ko dai mijinki sarki ne ban sani ba?"

Yanda tayi maganar cikin zolaya yasa matar yin dariya ita ma sannan tace "Maza ki samesu ku wuce, bana so ki k'ara ja min maganar da zan je bayar da hak'uri."

Turo baki tayi tace "Momma dama kin gaji dani?"

Dogo kuma siririn hancinta ta kama ta ja sosai tare da juyawa da ita suka nufi motar dake tsaye k'ofar gida, cikin kukan sangarta take fad'in "Momma ba zaki barni na ga Papa ba? Please."

Dungure mata kai tayi tace " Ban hanaki yi min yaren da ba namu ba?"

Da yatsunta tayi alamar sakata a bakinta tare da cewa "Nayi shiru, ni na tafi, sai na dawo, ki gaida Papa."

Duk tayi maganar ne tana hawa matakalar motar k'waya uku sannan ta juyo, da mamaki maman tace "Amma ba kin zo ne dan muyi magana ba?"

Dariya tayi tace "Momma zan fad'a miki."

"Yaushe kuma?" Ta fad'a da jimami, dariya ta sake yi tace "Momma zan kiraki idan na koma."

Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba, juyawa tayi zata k'arasa shiga sa茂 kuma ta juyo ta kalli maman na ta, ganin Maman na ta tayi ta sake irin sunkuyawar d'azu tace "Sauka lafiya princezna."

Sam bata yi tunanin komai ba har motar ta su ta fara tafiya, kujerarta dake baya ta wuce ta zauna tare da cire hularta, hakan ya bayyanar da kanta wanda gashi ya fara tohowa, dan dukansu yan matan dake motar kowace kan ta k'wal kwabo ne sakamakon aikin da suke da burin yi.

Wata budurwa ce tace "Hankalinmu zai kwanta yanzu tunda an kawoki gidanku kin ga Momma."

Wani kallo ta watsa mata lokaci d'aya ta d'auke kan ta, tab'e baki budurwar tayi ta d'auke kanta ita ma, tafiya suka yi mai nisan gaske kafin suka isa nesa da garin, wani babban k'ofa wacce aka rubuta sunan makarantar *Skola skoli novych smestnancov* (makarantar horar da sababbin ma'aikata) da yaren slovaque suka tsaya tare da yin oda, jim kad'an aka bud'e musu suka shiga.

Makaranta ce amma kamar gari guda, zaka tabbatar da girmanta ne kawai idan ka ga b'angarorin dake ciki, duk wani mai sha'awar karatun aikin saka kaki to nan yake ziyarta, kuma wanda ke karb'ar horon aikin soja ba zai san da zaman mai karantar horon police ba har sai in k'arshen sati ne da ake basu damar fitowa farfajiya har ma mai buk'ata ya fita waje.

Yanzu ma a b'angaren masu karantar ilimin *eaux et for锚ts* (gandun daji/ruwa da daji) motar ta aje su suka dinga shiga ciki, kowace na ta d'akin ta nufa mai d'auke da gado guda hud'u.

Kan gadonta ta zauna dan tasan yanzu wanka zasu fara dashi, ita kuma ba zata tsaya bin layi ko kuma zaman jira babu kaya a jikinta ba.

D'aya daga cikinsu ce ta shiga wanka sai biyun da suka cire kayansu suka d'aura towel, d'aya daga ciki ne ta kalleta tace " *Ayam*, wai me yasa kullum Mommanki take rusuna miki kamar wata shugabarta? Ko al'adarku ce haka?"

D'aga kai tayi ta kalli *Deeyam* d'in tare da gyara zamanta, saidai ba tace komai ba face k'ura mata ido, a zuciyarta kuma tunani take ita kanta ta fara ankara da haka, sau da dama idan ta lura tayi magana sai Momma ta kawo mata uzirinta.

Ganin ba tayi magana ba kawai yasa Deeyam share zancen tare da kallon gashin Ayam d'in tace "Amma Ayam ba kya tsoron hukumar makaranta ta ganki kin ajiye gashin nan? Za fa su iya korarki dan kin taka musu doka kuma da gangan."
Mik'ewa tayi tsaye tana sauke numfashi, hannu biyu tasa ta tattaro gashin kan na ta ta had'e wuri d'aya sannan ta kalleta tace "Kinga fa jibi ne shagalin k'arin haihuwata, nayi niyya 脿 wannan shekarar ba zan yi bikin k'arin shekarar nan da sulb'eb'en kai ba, dan haka in zaki iya ki je ki fad'a musu na tara gashi."

Dariya Deeyam tayi tace "Amma dai zaki mana babban shagali a wannan shekarar ko?"

Kanne mata ido tayi tace "Dole mana, shekarar mu ta k'arshe ce fa."

*Giobarh*

Kalar fatarshi kawai zata nuna maka lallai shi d'in daga gidan hutu yake, duk da yana da duhun fata amma kuma bak'inshi mai birgewa ne da d'aukar ido, tsiri-tsirin gashin kansa dake ta k'yalli yayi wara-wara alamar ana b'ata lokaci sosai wajen gyarashi.
Chapter 4 · 0% Book details