Sashe 82
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta d'ago kanta saboda ta fahimci muryar da ta ji, muryar da ita ta fara ji a duniya a kunnenta kafin ta mahaifiyarta, muryar da ta jima tana d'aukin ganin mai dauke da muryar, hannu ta kai da sauri zata yaye labulen yayar Kossam ta rik'e hannunta tace "Ba gimbiya kike ba yanzu, ke sarauniyar Giobarh ce."
D'auke hannayenta tayi ta saukesu k'asa, a sanyaye ta kalli matar tace "Wannan fa uwata ce, ta ya za'a hanani ganinta saboda Allah ya bani wani matsayi? Ba zan iya ba, zan d'aga na ga fuskarta dana jima ina mararin gani ko da hakan sab'awa dokarku ne."
Da sauri ta d'aga mayafin fuskarta ta fito suka had'a ido da Habbee, wani murmushi ta saki mai kama da kuka wanda yasa Habbee sunkuyar da kanta kamar zata durk'ushe tace" Ki gafarceni uwar gijiyata, ka da ki zubar da hawaye ta dalili na."
Da k'arfi Ayam ta jawota jikinta suka rumgume juna, kuka ta saki sosai tana fad'in" Na sha wahala tun bayan rabuwarmu da ku, an caza min kai na sosai Mah, an wujijjigani da labaran gaskiya wanda a gareni k'arya ne da farko kafin na yarda da su, Mah ! Me yasa ko sau d'aya baku fad'a min ba? Me yasa ba ku sake zuwa gareni ba? Me yasa Mah? Ina Aba?"
Habbee dai a d'arare take neman yakicewa daga jikinta, a sanyaye tace" Ki yi hak'uri sarauniyata, idan kina da buk'ata zan sanar da ke komai daya fara tun daga haihuwarki."
Jinjina kai tayi ta d'ago ta kalleta tace" Ina Aba?"
Nuna mata hanya tayi tace" Yana fada wajen nad'in sarauta."
Yayar Kossam ce tace" Mu je sarauniya Ayam, can muka nufa yanzu."
Jinjina kai tayi da zumud'i ta sauko da mayafinta wanda ke nuni da matar sarki ta fi k'arfin ganin idon kowane mutan gari suka nufi fadar data cika tamk'am da dattawa da masu ruwa da tsaki.
*A yi hak'uri ba yawa, saboda hidima ne.*
*Alhamdulillah.*
01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*49*
Suna isa fadar ba ta iya gane komai ba, sai dai tana d'aukin ganin marik'inta Utais, amma sam bata samu damar ganinshi ba har saida suka sadata da damdamalin da Umad yake tsaye cikin wata shiga ta alfarma, kayan sun masa kyau sun kuma mayar da shi babban mutum, duk da dishi dishi take gani amma a haka ta iya gane shi ne tsaye a gabanta, har kuma ta hangi yana sakar mata lallausan murmushi.
Dattijon daya tsaya gabansu tare da kambu a hannunshi yasa suka kalleshi a tare, a hankali Umad ya rusuna gwiwarshi d'aya a k'asa hakan ya ba dattijon damar saka mishi kambun a kan shi, sannan ya mik'o hannunshi na hagu ya saka masa zoben azurfa mai kyau da girma, wata k'aramar takobi ya mik'a masa ya karb'a da hannu biyu, take wurin ya kaure da hayaniya da shewar shikenan ya zama sarki.
A hankali ya mik'e tsaye yana sunkuyar da kanshi, wasu zafafan k'walla ne suka d'aso masa a kumatu, a sanyaye a k'asan zuciyarshi ya furta "Shikenan, shikenan nauyi ya hau kaina, madadin matata k'waya da'aya tak, yanzu nauyin dubbanin al'umma ne a kai, Allah ka ga zuciyata, na rok'eka ka bani ikon rik'e nauyin nan da adalci a tsakanin mutane na, Allah ka jib'anci lamurana dana mutane na baki d'ayanmu, Allah ka dafa min komai ya zama mai sauk'i a gareni..."
Taffin da aka saka sanda aka saka ma Ayam wani kyakyawan zobe a hannunta da kuma kambun da bai kai girman na shi ba ya dawo dashi daga addu'ar da yake, kallonta yayi ita ma sai kallon zoben take tana jin wani nauyi na hawa kanta, fuskantarta yayi da kyau ya rik'o damatsunta ya juyota gareshi suna kallon juna.
A hankali yanda ko na kusa da su bai ji me ya fad'a ba yace "Ki yi hak'uri Ayam."
Lumshe ido tayi tace "Me yasa baka fad'a min hakan ko da a waya ba?"
A raunane yace "Ban sani ba ni ma Ayam, sai yau d'in nan da kika zo gareni, kiyi hak'uri."
D'an murmushi tayi tace "Ka daina bani hak'uri."
Kallon zoben hannunta ta sake yi sannan ta kalleshi tace "Hakan na nufin na zama matar sarki yallab'ai Umad? Hakan ya tabbatar min da ni ma nauyi ya hau kai na kenan?"
Jinjina kai yayi a nutse yanda ba kowa ya fahimci hakan ba yace "Hakane, da fatan zaki tayani d'aukar nauyin nan Ayam? Ina rokonki da ki kasance a gefena, hakan zai k'aramin k'arfin gwiwar aiwatar da mulkina a tsanake, ki zama mai tausaya min, hakan zai sa na zama mai tausayawa al'ummata, ki agaje ni Ayam, hakan zai saka ni farin ciki har na zama mai fara'a ga mutane na, ki tattaleni ki zama mai sama min nutsuwa a sanda kaina ya d'au zafi saboda girman nauyin dake kai na, hakan zai sa na zama adalin sarki ga jama'ata, na rok'eki."
Ya fad'a yana had'a hannayenshi biyu alamar rok'o, da sauri ta rik'e hannayentshi duka biyun tana fad'in" Zan yi, zan yi sarki na, shugabana, farin cikina, kima da darajata, duk kai ne silar dana samesu, zan yi maka komai daka buk'ata, In shaa Allah, fatana Allah ya bani ikon rik'e wannan nauye nauyen, sannan ka zama mai kawar da kai daga kuraraina, ka zama mai tausasa min yayin da na b'ata maka, ka zama mai jink'ai na a sanda na kasa, ka zama adalin sarki a gareni yayin yanke min hukunci, ka zama uba ga wannan marainiyar, ka zama mai sassauci ga laifukana, hakan zai bani azamar kyautata maka."
Da fara'a a fuskarshi ya amsa da" Zan yi, zan yi sarauniyata, In shaa Allah."
Da murmushi a fuskarta ita ma tace" Na ji dad'i, kuma In Shaa Allah kamar yanda na kasance mata ta farko a gareka, zan k'ok'arta wajen ganin na zama makarantar farko mai inganci a gareka."
D'an girgiza mata kai yayi cikin rad'a sosai yace" Matata ta farko, kuma matata ta k'arshe In Shaa Allah."
Girgiza kai tayi ita ma tace" Bayan Mah ta fad'a min addinin islam ya yarjewa maza musulmi auren mace biyu, uku, hud'u, idan ba zaku iya adalci bane aka umarce ku da d'aya ko kuma abinda damarku ta mallaka."
Janye hannunshi d'aya yayi daga na ta ya lak'aci hancinta yace" To ai saboda ba zan iya adalcin bane nake son k'are rayuwata da ke, ba zan iya had'aki da wata ba sarauniyata, sarauniyar zuciyata."
Kallonshi tayi tar tana gimtse dariyarta tace" Ba wani nan, bayan ma d'aukar fansa ce ta had'ani da kai."
Dariya ce ta sub'uce masa bai yi zato ba, jawota yayi jikinshi suka rumgume juna cike da shauk'in juna, hakan yasa fadar d'aukar tafi da hayaniya ana mai jin dad'in ganin haka.
A wannan wunin basu samu tsagaitawa ba bare su huta, bak'i ta ko ina suka dinga halartar walimar da aka shirya ta zuwan sarauniya da kuma nad'in sarautar, sai gashi hatta da sarakunan wasu k'asar suna zuwa dan tayasu murna da addu'ar alkairi.
Ayam ta gaji iya gajiya, gashi duk abinda zata kai bakinta sai da taka tsantsan saboda komai za ta yi sai a ce ita fa yanzu sarauniya ce, bata ma bud'e fuskar ba saboda tsaro bare kuma ta samu damar cika cikinta, gashi tana da buk'atar ta ci ta k'oshi iya iyawarta, amma an k'i bata damar haka.
Ta galabaita sosai tana cikin jin haushin yanda aka kasa barinta shak'at jakadiyar sabon sarki ta shigo falon ta sanar da jakadiyarta mai martaba na son ganin sarauniya yanzu yanzu.
Da sauri ta mik'e ta bi bayan jakadiyar da tunanin tana shiga ta fashe da kuka tace yunwa zata kasheta, saidai suna shiga nan ma wasu bak'in ne, tawagar ma'aikatarsu ne suka yi tattaki dan tayashi murna da ita kanta, dan haka ya kirata dan su gaisa.
Ganinsu duk sai ya sage mata gwiwa ta k'arasa a nutse ta zauna, gaisawa sukayi sosai da girmamata saboda d'aukakar da Allah ya mata, dan in za'a bi salsala ne to gaba da baya ita d'in ba abar banzatarwa ba ce, ba dan tak'i karb'a ba da shi kanshi Umad zai zama k'asa da ita ne saboda kujerarta ke gaba da tashi.
Addu'o'i suka musu kafin su mik'e da niyyar zuwa wajen da sauran bak'in suke, da kallo ta bisu har suka fice ta ga an rufo k'ofar, mik'ewa tayi tsaye ta jaye rufin fuskarta hakan yasa kwalliyarta bayyana, kallonta yayi yana murmushi zai fad'a mata kalma mai dad'i, sai gani yayi ta zube k'asa tayi zaman yan bori ta fashe da kuka iya k'arfinta tana dafe cikinta da fad'in "Wayyo! Mah ke! Mahhh ! Shikenan mutuwa zan yi ni wallahi."
Da sauri ya zaburo ya zo gareta ya durk'usa yana rik'o hannunta yace "Me ya faru ne sarauniyata? Me ya sa ki kuka?"
Tsit tayi ta kalleshi ta turo baki kamar zata tsinkashi tace "To ba yunwa nake ji ba, tunda na zo ban ci na k'oshi ba, komai zai yi sai a wani ce sarauniya sarauniya, ni na gaji ba zan iya ba gaskiya, kawai ka ban abinci na ci na k'oshi."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi, a sanyaye ya furta "Yunwa ce matsalar?"
D'aga kai tayi tace "E."
Shafa kuncinta yayi yace "To kwantar da hankalinki, matar sarki ai ta fi k'arfin yunwa ta kasheta sai dai k'oshi."
Hannunshi daya d'ora kan kuncinta ta kamo da hannu biyu, lumshe ido tayi ta saka yatsunshi biyu a cikin bakinta, wani d'ummmm ! Ya ji ni'imtaccen d'umi ba mai cutarwa ba, bai san sanda ya furta" Ahhhhhhhhh."