← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 86

Sashe 50

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rusunawa yayi yace" Godiya nake ranka shi dad'e, sai na ji daga gareka."

Jinjina kai kawai yayi bai ce komai ba, mik'ewa yayi a ladabce yace" Na barka lafiya sarki na, a huta lafiya."

Sake jinjina kai yayi yana kallo har ya fita daga falon bak'in na shi, a take ya tsunduma kogin tunani akan shawarar Bukhatir d'in.

*Khazira*

A wajen su Ayam lokaci mai tsayi suka d'auka suna karatu, Juman ce kad'ai ta tsagaita saboda lokacin sallah zuhur, tana duba agogo ta kalli Ayam tace "Yanzu tashi mu yi sallah, ba laifi mun sha karatu, fatana dai idan mu ka idar ki fad'a min ko da rabin abinda na sanar da ke ne."

Jinjina kai tayi tana murmushi sannan suka mik'e, ban d'akin Ayam d'in suka shiga tare, tsayawa Juman tayi bakin k'ofa tace "Ki fara d'aura alwalar na gani komai yayi daidai."

Da "To." Ta amsa ta cire kallabinta data yana ta fara da wanke hannayenta da bismillah, a tsanake take kallonta tana gabatar da komai yanda ta koyar da ita, amma abun mamaki sai ga shi Ayam tayi komai yanda ta koya mata, za ma ka rantse da Allah ita ce ke koya mata, saboda yanda take wanke komai da kyau har zuwa inda aka ce d'in, ba wannan ya fi bata mamaki ba saida ta ga ta idar ta mik'e tsaye ta karanta addu'ar da ake karantawa bayan idar da alwalar ta d'aga hannu ta furta.

_"Ashhadu an la'ilaha illallah-wahdahu la sharika lahu-wa ashhadu anna Muhammad rasulillah."_

_"Allahuma-ja'alni mina-tawwabina-waja'alni minalmutad'ahirina."_
_"Subhanaka-lahuma wa bi hamdika, ashhadu an la'ilaha illa anta, astagfiruka wa atubu ilaikh."_

Tana juyowa suka had'a ido ta mata murmushi tace" Mah na yi komai daidai?"

Da farin ciki tace" Ayam, ai daidan ma mak'ura ki ka yi, ta ya ki ka iya rik'e komai da na fad'a miki lokaci guda haka?"

Numfashi ta sauke tace" Mah, idan har akwai wata baiwa dana yarda ina da ita, to wannan ce ubangiji ya bani, a iya sani na ba'a tab'a maimaita min abu sau biyu ba."

Dariya tayi ta jin dad'i sannan tace" Na ji dad'in haka, saboda haka ma zan had'aki da malami ku fara karatu daga daren yau, kafin nan da d'an lokaci ke ma ki fara koyarwa."

Dariya tayi ita har hak'oranta suka fito waje kafin ta nufi wajen gado ita kuma ta k'arasa shiga ban d'akin dan yin alwalar ita ma.

Tana idar da alwalar ta fito ta samu Ayam zaune tana jiranta, ganinta yasa ta mik'e tana gyara kallabinta, kallonta tayi da kyau tace "Mu je d'akina sai na baki hijab ki saka, kafin jibi ke ma zan sa a kawo miki."

Da "To." Ta amsa suka fita a d'akin na Ayam suka nufi d'akin Juman d'in, hanyar da Juman ta biyo d'azu suka sake bi ta nan, a daidai corridorn da ba'a cika bi ba suka samu hadimai guda biyu suna sallah duk sun yane kawunansu da kallabin, yanda basuyi tsammanin zuwan wani ba a lokacin yasa da k'arfi suka juyo a tare sun ma manta da sallah suke.

Da sauri Juman ta musu alama da hannu tace "Ku ci gaba."

Durk'usawa sukayi k'asa kawunansu sadde suna sauke ajiyar zuciya, ko ba komai sun san zasu tsira da rayukansu, tunda ita kan ta a b'oye take sallah a sanin da suka mata.

Da mamaki Ayam tace "Ku kuma me ye haka? Kuna ganawa da wanda ya hallici ita kanta uwae gijiyar ta ku, shi ne zaku wani tsaya rusuna mata?"

Murmushi Juman tayi jin abinda Ayam d'in ta fad'a tace "Ba wai gaisheni suka tsaya yi ba, sun tsorata ne saboda basu san wa ke tahowa ba."

Da sabon mamaki tace "Kamar ya? Tsoro kuma a cikin bautawa ubangiji?"

Jinjina kai tayi ta kama hannunta suka nufi d'aki tana fad'in "Saboda a nan ba'a barin musulmi yayi ibadarsa yanda ya dace."

Cak ta tsaya tare da d'an murza hannunta dake cikin hannun Juman har tayi nasarar raba hannayensu, idonta ne suka d'auki launi ja tsabar b'acin rai da takaici tace "Mah, idan sarki ba musulmi bane, me zai sa ya hana talakawanshi 'yancinsu? Wannan ai tauye' yanci ne ko a dokar k'asar nan, bare kuma a addinance."

Girgiza kai tayi tace "A gaskiya Mah ba zan juri ganin haka ba, yanda kowane mai ji yana da addini yake bautarsa babu takura, ban ga dalilin da zai sa musulmi ma yayi bauta da takura ba, dan haka duka wani mai kad'aita Allah dake cikin gidan nan ya fito zamuyi sallah tare."

Juyawa tayi da sauri ta kalli hadiman tace" Duk wanda kuka san addininmu d'aya da shi ku tara mana su a farfajiya."

Da sauri Juman tace" A'a Ayam, kar ki fara da abinda zai saka rayuwarki a had'ari."

Murmushi tayi tana kallonta tace" Mah, tun fa cikina na gudan tsoka nake cikin had'ari, bana jin kiramin had'ari a yanzu zai iya tsorata ni, dan da shi na girma."

Bin bayan hadiman tayi da suka fita haka Juman ta bi bayanta jiki a mace tana mai k'arfafa zuciyarta cewa ba zata barta ita kad'ai ba.

Tsaye tayi farfajiyar ita da Juman yayin da hadiman maza da mata suka dinga b'ullowa daga kusurwa daban daban, cikin k'ank'anin lokaci sai ga hadimai gabanta guda goma sha takwas, kallonsu tayi da kyau tace "Dukanku kuna da alwala?"

Da "E ranki shi dad'e." Suka amsa mata, jinjina kai tayi ta kalli wasu dogarai biyu maza tace "Ku samo mana babban carpet."

Da gudu suka juya suka nufi wani b'angare, jim kad'an suka dawo sun d'auko babban carpet guda sun tallabo, suna zuwa suka bud'eshi aka shinfid'a a nan, duba taron mutanen tayi da suke kallon ikon Allah har yanzu suna tambayar kawunansu me zai faru tace" A cikinku wa zai ja mu sallah azahar?"

Kowa zaro ido yayi suka shiga kallon kallo, hakan yasa babu wanda yayi jarumtar nuna kanshi saboda tsoron me zai biyo baya, numfashi ta sauke ta kalli mazan dake gefe d'aya tace" Dukanku babu mai jarumtar da zai iya ne? Ko kuma mahaliccin na ku ne baku iya ganawa da shi ba?"

Shiru wurin ya d'auka sai kawuna da suka sadda k'asa, d'orawa tayi da" In dai har taron maza kamar ku za'a rasa wanda zai jagoranci dayawa zuwa ga ubangijin talikai, to ina ganin dukaninmu babu anfanin rayuwarmu, dan ni dai a wuri mutuwa da kima ya fi rayuwa da tsor."

Shiru tayi na dak'ik'u, jim kad'an kam wani matashi d'aya daga cikin masu bawa shukoki ruwa ya d'aga hannu yace" Ni zanyi jagorancin gimbiya, ko da hakan zai sa na rasa raina."

Da jin dad'i sosai ta kalleshi tace" Addininmu bai yarda mu jefa rayuwarmu had'ari ba, amma wajen kare mutumci, addininmu, dukiyarmu, iyalinmu, addini ya bamu dama mu yi komai, dan haka mu daina b'oye addininmu alhalin wanda basa da addinin ma suke bayyana na su."

Ai kam gaba ya shiga inda dukan hadiman suka shiga daidaita sahunsu, mazan na gaba sai kuma tazarar da aka saka tsakaninsu da mata ta kusan k'afa shida zuwa bakwai, sallah suka fara a nutse inda duka matan kalluban kansu ne suka yane kansu da shi.

Sannu sannu hadimai da sauran dogaran gidan suka fara taruwa kallonsu, al'ajabi suke na ganin sabon abun, dan wasu basu tab'a gani ba ko da a b'oyen, saidai babu wanda yake jin zai iya tambayar wye silar wannan taro, dan kuwa kowa yasan bak'uwarsu ce, tunda haka bata tab'a faruwa ba har sarauniyarsu bata da wannan k'arfin halin.

Raka'arsu ta k'arshe ce sarki Musail ya fito daga k'ofarda zata sadashi da fadarshi, ganin wannan taro yasa shi tsayawa yana kallonsu, hankalinshi tashe yake kallonsu yana zazzare ido, bubbuga sandarshi ya dinga yi ya rasa me ma zai fad'a, musamman jin yanda gidan yayi shiru, su kuma masu sallar suka duk'ar da kawunansu ka rantse basa numfashi tsabar girmamawa, lallai ya tabbatar wanda suke bauta a gareshi na da mahimmanci a garesu, suna girmamashi kuma suna jin kunyarshi tare da k'ask'antar da kansu zuwa gareshi.

Juyawa yayi ya kalli sarki yak'i Adah dake bayanshi yace "Ka taho min da gimbiya Zafeera idan sun gama."

Da sauri ya juya ya nufi shiga fadar, da mamaki Adah ya kalleshi yace "Idan ma ta gama ya ce? Lallai yarinyar nan barazana ce barinta a raye."

Gyara tsayuwarshi yayi dan ya jirata kamar yanda ya ce, ya kai minti biyar a tsaye kafin ya ga sun fara tashi suna barin wuri ya k'arasa, a ladabce ya tsaya kusa da ita yace "Ranki shi dad'e gimbiya, mai martaba sarki na yana son ganinki yanzu yanzu?"

Jinjina kai tayi ta mik'e a hankali hakan yasa Juman ma mik'ewa da sauri ta rik'e hannunta, kallon Adah tayi tace "Lafiya Adah?"

Da girmamawa yace "Lafiya lau ranki shi dad'e."

Kallon Ayam tayi fuskarta cike da damuwa tace "Ina jin tsoro Ayam, ina tsoron ko ya ga abinda ya faru yanzun."

Murmushi tayi cikin nutsuwa tace "Mah, ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru da yardar Allah."

Zage hannayenta tayi ta saka takalminta sannan ta ma Adah alama da ido su tafi, wucewa yayi gaba ita kuma ta bi bayanshi har zuwa fadar, har lokacin kuma bata daina kalle kalle ba dan har yanzu tsarin ginin masarautar na bata mamaki yanda aka k'erashi.

Suna shiga fadar ta d'ora idonta akan sarki Musail dake zaune kan wata tamfatsetsiyar kujera ta alfarma hannunshi d'auke da sandarshi d'aya hannun kuma ya dafe hannun kujerar.

Dhurani ne kawai a zaune sai Khatar a gefenshi shi ma zaune, cikin nutsuwa ta k'arasa tsakiyar kujerun nesa da sarki Musail a ladabce tace "Pah, an ce kana son gani na?"

Cikin sanyi da taushi yace "Gimbiya Zafeera wa ya baki izinin tara min talakawan cen a cikin gida har ku dinga min wani surkulle?"

Da fara'a a fuskarta tace "Pah, ba talakawan gari ba ne, dukansu hadiman cikin gidan nan ne."

Had'e fuska yayi yace "E na gani, tambayarki na yi wa ya baku izini?"
Chapter 50 · 0% Book details