← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 86

Sashe 55

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jim tayi sai kuma ta d'aga kafad'a alamar bata sani ba, matsawa Juman tayi kusanta ta ja dogon hancinta tace" Ko dai ko dai? Ko dai akwai abinda k'aramar yarinyata ke b'oye min ne?"

Rik'e hannun Juman d'in tayi data ja mata hanci da shi tana k'yalk'yala dariya tace" Mahhhh...hancina fa, ni ba wani abu da nake b'oye miki, d'azu ma ba'a gabanki na saka kaya ba?"

Janye hannunta tayi daga hancinta sai kuma ta shiga mata cakulkuli tana fad'in" Ban yarda ja'irar yarinya, fad'a min me kike ji a kan shi? Da alama idan baki zama sarauniyar Khazira ba zaki zama sarauniyar Giobarh."

Cikin farin ciki suka dinga wasarsu har Juman ita ma ta canja kayanta suka kwanta, daga kwance ma duk abubuwan da zasu anfaneta a cikin addininta ta dinga sanar da ita, k'aramar wayar da Ayam har ta manta ta ta ce sak'o ya shigo, d'auka Juman tayi ta mik'o mata tace "Wayarki."

Karb'a tayi tana duba wayar dan har ta manta wace kala ce ma, bud'e murfin tayi ta duba sak'o gajere kamar haka _"Ki ji magana ta, bayan d'akinki da na mahaifiyarki ki kwana a ko ina ki ke so, idan kuma kina son kasancewa cikin tsaro, to ki kwana a k'ark'ashin kulawar Umad."_

Tashi tayi zaune tana sake karanta sak'on, me hakan ke nufi kuma? Wa ye ya turo mata sak'o haka? Gashi dai lambar ma a rufe take, tsaki tayi kawai ta rufe wayar ta aje gefe ta koma ta kwanta.

Cike da kulawa Juman ta kalleta tace" Lafiya? Me ya faru?"

Ba yabo ba fallasa ta amsa da" Ba komai."

D'ora mata tayi daga inda suka tsaya ta ci gaba da fad'in" A duk wani hadisi daya tabbata kuma ya zo daga iyalai ko sahaban manzo (S. W. A) babu wanda ya nuna Annabi Muhammad yayi wankan tsarki wanda ba cikakke ba, ma'ana wankan da bashi da alwala, amma magaba sun inganta wanka da baya da alwala ma, wasu daga ciki sun ce ko da a cikin kogin ruwa ka tsumbula da niyyar wankan janaba to yayi, haka ma idan a buta ne ka d'aga ka kwarara a kan ka shi ma yayi..."

Numfashin da Ayam ke saukewa ne yasa ta satar kallonta, ai kam idonta a rufe alamar bacci, da alama kuma ta fara jin dad'inshi saboda yanda ta turo baki hannunta akan cikin Juman, murmusawa tayi ta d'an muskuta kwanciyarta sannan ta gyara hannunta ta fara shafa gashin Ayam d'in.

Irin dad'in da take ji marar misaltuwa na ratsata sanadiyar kasancewa tare da 'yarta, hakan yasa murmushi ke shinfid'e akan fuskarta idonta a lumshe tana d'an rera wak'a a can k'asan zuciyarta ta farin ciki da godiya ga Allah, sannu sannu ita ma har baccin ya d'auketa mai dad'in gaske data jima ba tayi irinsa ba.

Yanda ya ji shiru daga d'akin yasa shi shigowa cikin sand'a, ganin dukansu bacci suke yasa ya ci gaba da takawa saida ya zagaya inda Ayam ke kwance, a hankali savoda baya so su farka ya sunkuya tare da d'an d'ora hannayenshi a kan gadon ya tokaresu, matsawa ya dinga yi saida ya kai kanshi kusa da na ta, cike da shauk'i da so da k'auna ya d'ora labb'anshi ya sumbaci kanta, a hankali ya d'ora hannunshi akan gashinta ya shafa wasu k'walla na cika masa ido.

Motsawar da Ayam ta d'an yi ce tasa ya zabura ya mik'e tsaye ya rarraba ido cikin rashin gaskiya, kamar zata bud'a ido sai kuma ta sake yin ram da cikin Juman ta ci gaba da shek'a baccinta.

A hankali ya zagaya ta b'angaren Juman yasa hannu ya daddab'ata, a tarz suka bud'a ido suka kalleshi kafin su raba jikinsu dana juna, cikin had'e fuska sarki Musail yace "Ke me kike a nan? Ba ga d'akinki can ba?"

Turo baki tayi gaba tace "Pahh, nan nake so na kwana, kai ma ka zo ka kwanta a nan."

Murmusawa yayi yace "Zafeera, ki je d'akinki ki kwanta kinji, na zo ganin mahaifiyarki ne tunda na ga ita bata san ta je inda nake ba."

Cikin magagin baccin daya kasa sakinta ta kalli Juman sannan ta rarrafa ta sauka daga kan gadon, ganin kamar tana had'a hanya yasa shi saurin kama hannunta ya rumgumota a jikinshi, saitin kunnenta ya rad'a mata" Ki tabbatar baki je d'akinki ba a daren nan."

D'aga kanta tayi t kalleshi da mamaki da kuma fad'aw tunani, amma kafin ta ankara ta turata k'ofar d'akin ya rufe ya barta tsaye da zulumi.

Ganin gidan shiru ga fitilu duk an kashe yasa ta saurin d'aga k'afa ta nemi haurawa sama, dakatawa tayi sai kawai ta bi ta wata kusurwar duk da bata san ina zata kai ta ba, cikin tsoro tsoro take tafiya tana sand'a, duk k'ofar data wuce saita kalla da mamakin yawan d'akunan dake cikin gidan, jin ana bud'e wata k'ofar daga bayanta da makulli yasa ta saurin ruguwa cikin sand'a, d'akin dake k'arshen kusurwar kawai ta bud'a ta kuma yi sa'a a bud'e yake, dan tsoronta bata san wa ye zai fito ba, kuma sak'on nan da kuma abinda mahaifinta ya fad'a mata ya tsorata ta sosai, ga ka duhun cikin gidan wanda sai d'an siririn hasken jar fitila kawai.

Tana shiga d'akin ta mayar da k'ofar da sauri ta rufe tare da juyawa ta dafe k'irji dan ta sauke numfarfashi, sai dai bala'in data gani ne ya yi barazanar tafiya da numfashinta, kakkafewa idonta sukayi inda ta ja numfashi amma bata samu damar saukeshi ba, ga hannunta akan k'irji ta tsaya k'am kamar gawa.

Fitowarshi kenan daga wanka ya gama goge jikinshi, wandonshi ya d'auka 3 quater zai saka, hakan yasa shi zame towel d'in dake d'aure a k'ugunshi, amma da ya ji an shigo d'akin kamar ba lafiya ba sai ya dakata ya juya da k'arfi rai b'ace da tunanin wane marar tunanin ne, ganinta yasa komai na shi ya tsaya ya rasa abun yi, musamman daya fahimci kamar ta fita hayyacinta sakamakon mugun ganin da ta yi. 馃槍

A saib'ance ya sunkuya ya d'auki towel d'in ya d'aura yana jan tsaki da fad'in "Ko ma menene ke kika ja."

Wani tsakin ya kuma saki tunawa haka ma waccen ranar ta bankad'o mata kai d'aki, saidai anyi sa'a ranar yana cikin ban d'aki ne.

Sake juyawa yayi ya kalleta ya ga tana nan yanda take, girgiza kai yayi ya fara takawa zuwa gareta, yana tsayawa gabanta ya k'yasta mata hannu yace "Ya dai? Kin ga wani abu ne?"

K'arfin halin irin na ta yasa ta d'aga baki za tayi magana, sai ta ji babu abinda zai iya fitowa sai kurmanci, hakan yasa ta daddagewa ta d'aga bakinta ta kwamtsa k'ara, da wani irin sauri ya sa hannu ya rufe mata baki tare da jawota jikinshi ya had'e gam, tana jin haka sai kuma numfashinta ya b'ace b'at ta sume a jikinta, hakan yasa jikinta ya saki kamar wata matatta.

_Domin samun *lu'u lu'u* da kuma *Badak'ala*, ki biya naira d'ari biyu kacal ko kuma 400f cfa, dan samun na ki tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52._

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*32*

Girgiza kai Umad yayi ya huro iska daga bakinshi, d'ago kanta yayi ta hanyar jawo gashinta ya kalli fuskarta, da gaske suma tayi daga ganinshi haka? Ko kuma dai dama a kid'ime ta zo?

K'ofar da aka k'wank'wasa ne yasa shi kallon k'ofar a tsorace duk da hakan ba d'abi'arsa bace, duburburcewa yayi ya fara tunanin inda zai sakata, dan ganinta a d'akinshi a wannan yanayin zai iya zama barazana ga shirinshi, da sauri ya jata zuwa drower dake gefen ban d'akin ya bud'e, cak ya d'auketa ya sakata a ciki zaune dangalgal akan k'ugunta saboda babu kaya a wurin, mayarwa yayi ya rufe daidai da bud'o k'ofar an shigo, cikin rashin gaskiya ya kalli k'ofar yana d'an k'ank'ance idonshi.

"Zafreen." Abinda ya ambata kenan a zuciyarshi, k'aramin tsaki ya ja na takaicin halayyarta, yanda take takowa gabanshi cikin rigar bacci iya cinyoyinta, hakan yasa shi ya fad'a tunanin to me take nufi? Saida ta zo gabanshi ta tsaya ta d'ora hannunta akan wuyanshi, cike da saloda k'warewa tace "Yal'ab'ai, ba kayi bacci ba?"

D'ora hannun d'aya tayi hakan yasa ta sarkayeshi da hannayenta ta yanda ba zai iya zame mata ba, kanne masa ido d'aya tayi tace "Kasan wani abu? Na zo ne na tayaka hira, nasan zaka buk'aci hakan."

Zuba idonshi yayi cikin na ta tare da saka hannayenshi biyu ya d'auke hannayenta daga wuyanshi, had'e fuska ya sake yi murya a dak'ile yace "Ki daina tab'ani, saboda ni muharraminki ne."

D'aga gira tayi tace "Me ye haka kuma?"

Juyawa yayi kan gadon ya d'auki rigarshi singlet bak'a yana fad'in "Ba zaki gane ba, amma addini na na da tsari, ba komai ya lamunce min aikatawa ba."

Da alamar tambaya tace "Addininka? Wane addini kenan?"

Saida ya fara saka rigarshi yace "Addinin musulunci."
Yana sakawa ya juyo ya kalleta yace "Zaki iya tafiya, dare yayi, bai kamata kasancewarki nan ba."

Lab'e baki tayi tace "Me ya hanashi kamatan?"

Nunata yayi a hassale yace "Saboda ke ba matata ba ce."

Zaro ido tayi cikin sangarta tace "Dama kana da mata?"

A hassale ya tunkareta ranshi b'ace ya figi hannunta, bud'e k'ofar yayi ya wurgata waje sannan ya kalleta yace "Baki san ko ni waye ba, ki yi nesa da ni har zuwa lokacin da zan bar nan, idan kuma baki kiyaye ba..."
Chapter 55 · 0% Book details