Sashe 44
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyowa tayi sai kawai ta sauke ido akan shi, cike da fad'uwar gaba ba tare da tunanin zata iya hangoshi a cikin mutanen nan ba yayi saurin sunkuyar da kan shi k'asa, murmushi ta saki tace" E hakane, ni ba zab'abb'iya ba ce, tunda ni dai ban ga wani abu a jikina ko a cikin rayuwata ba daya sha bambam da na ku."
Wannan tsohon daya tab'a hannunta ne yace" To amma gimbiya ya maganar canjin da zaki kawo mana? Dan na b'ata shekaru da dama ina ciyar da abinci dan kawai ki bayyana ko 'ya'ya zasu samu rayuwa mai kyau fiye da ta wa, duk da ba k'arfin ciyarwar gareni ba."
Da mamaki ta kalli tsohon ta gyara tsayuwa tace" Baba yayanka nawa?"
Kai tsaye ya bata amsa da" Bakwai, maza hud'u mata uku, amma duka matan na gidan aurensu."
Kafeshi tayi da ido tace" Dukansu sunyi karatu?"
A ladabce yace" K'aramar 'yata ita ce aka haifa shekara biyu bayan haihuwarki, daga lokacin da aka haifeki dukda kinyi b'atan dabo, hakan bai sa na cire rai da samun canji ba, daga lokacin na daina biyan kud'in karatunsu na ce su zauna gida suna kama min sana'ata, dan canji ya kusa zuwa da zasu samu rayuwa mai kyau."
Had'e fuska tayi ta girgiza kai tana ji kamar ta wanka masa mari, saida ta feso zafin dake balbali a zuciyarta kafin ta sake jimk'e wayar nan dake hannunta ta kalli tsohon tace" A hakane kuma kake nema musu canjin rayuwa? Shin ko kasan da ace zan tattara takardun wad'anda sukayi makaranta ne sannan na basu aiki, kasan da 'yayanka babu wanda zai shiga ciki?"
Cikin jin haushi da fad'a ta kalli dukan mutanen tace" Ire irenshi na wa ke akwai a nan? Wace irin rayuwar jahilci da mutuwar zuciya kukayi a baya? Saboda kawai an ce an haifi zab'abb'iya, shin cikinku akwai wanda zai iya nuna min wani canji guda d'aya tak wanda cikin wanda suka gabaceni suka kawo muku wanda ya tallafi rayuwarku da ta yayanku?"
Kallon tsohon tayi ta d'ora da fad'in" Me aka tab'a canza muku kafin zuwana ni?"
Wulwula ido yayi sai kuma ya girgiza kai yace" E to, zab'abb'e daya gabata wanda daga gareshi muka samu labarin zuwanki, a lokacin muna da k'arancin ruwa, kuma mun kawo kukanmu so ba adadi a wajen sarkinmu, to a lokacin shi ne ya mana rinjiyoyin ruwa wanda a yanzu malaman fada suka mayar da su panpunan zamani."
Jinjina kai tayi tace" Na ji kun samu ruwa kyauta, bayan shi fa?"
Wata dattijuwa dake gefe ne tace" Wa ya fad'a miki gimbiyarmu? Ai bayan rasuwarshi da wasu shekaru sai iyalenshi suka fara karb'ar kud'in jama'a idan zasu d'ebi ruwa, yanzu haka yara ne birjik a duk gurin birtsatsen nan suna karb'ar kud'i ana d'iban ruwa."
Wani murmushi tayi tana girgiza kanta kafin tace" Anfani kawai suke da ku suna cika aljihunansu, amma daga yanzu ba zaku sake biyan kud'in ruwa ba, ni zan yi magana da sarkinku wato mahaifina, ku kwantar da hankul..."
Ihun da suka saka da k'arfinsu da tapi na murnar abinda ta fad'a yasa ta dafe kunnuwanta da ta ji ihun har cikin dodon kunnuwanta, addu'a suka dinga mata da fatan alkairi da kirari sanda ta juya tare da rakiyar hadimar nan dogarai kuma suna rik'e mutanen saida suka ga shigewarta an rufe k'ofar kad'ai hayaniyar ta lafa wasu suka fara barin wurin ma.
Suna cikin taka matakalar wayar dake hannunta tayi vibration, da sauri ta duba ta ga lamba ce babu suna, tab'e baki tayi ta bud'e ta kara a kunne, muryar sarki Wudar ce ta ji cikin shauk'i yace "Gimbiyata, fatan kin sauka lafiya?"
Da mamakin jin muryarshi d tunanin kenan shi ya turo mata da wayar? Ganin hadimar nan ta juyo tana kallonta yasa ta mata alama da hannu tace "Ki je kawai ina zuwa."
Saida ta ga ta juya ta tafi ta sauke ajiyar zuciya tace "Yallab'ai barka."
Cike da jin k'uruciya da rashin kunya sarki Wudar yace "Ba yallab'ai ba, ki kirani da mijinki."
Rintse ido tayi ta yatsina fuska kamar ta ga ba-haya tace "Yallab'ai?"
Amsa mata yayi da "E mana, ba kin min alk'awarin aure ba, alk'awari kuma a wurinmu tamkar d'aura auren ne."
S'an safe gaban goshinta tayi tace "Yallab'ai kana lafiya? Ya d'anka?"
Wani abu ya ji a zuciyarshi saboda tambayar d'anshi da tayi, amma sai ya share yace "Ina lafiya, ke fa?"
Jinjina kai tayi tace "Ina lafiya, nagode."
D'oraw yayi da "Kin tabbatar kina lafiya? Babu wani abu daya faru?"
Amsawa tayi da "E yallab'ai."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan, yanzu ya maganar alk'awarinmu?"
A tak'aice cikin jin ya fara hawa mata kai tace "Zamuyi magana, zan sake kira anjima."
D'if ta yanke kiran tana jan tsaki a zuciyarta tace "Kaga jaraba, me zanyi da kai ni kuma tsofai tsofai da kai."
K'arasawa tayi ta shige ita ma ta samu hadimar bakin k'ofa tana jiranta, tana zuwa ta kalleta tace "Ki kaini wajen sarki."
Da sauri ta kalketa jin wai ki kaini wajen sarki, rusunawa kawai tayi ta nufi hanyar da zata sadasu da shi d'in gabanta na fad'uwa dan bata san me zai mata ba idan har baya buk'atar ganin kowa ta kuma rakata gareshi d'in.
Saida suka jira a bakin k'ofar wani dogari ya musu iso, jim kad'an ya dawo ya ba wa Ayam d'in umarnin shiga abisa yarjewar sarkin, tana zura k'afarta akan wani mahaukacin tattausan carpet ta lumshe ido, wani irin sanyi ne ya ratsata tare da ni'imtaccen k'amshi ga wani irin shup shup da d'akin yayi, tana k'arasa shiga ta wara ido tana kallon ko ina, a take idonta suka hasko mata hoton mutanen da ta gani yanzu, wanda dayawa daga ciki kana kallonsu zaka san talauci ya musu katutu, amma dubi irin daular dake cikin gidan sarautar nan, ka rantse da Allah arzikin duk duniya aka tara a cikin gidan.
Jin bata ce komai ba sai kalle kalle take yasa sarki Musail gyara zamanshi yace "Ina jinki gimbiya."
Da sauri ta dawo da hankalinta kan shi tana motsa bakinta a hankali tace "Amm..Pah, dama ina so ne zamuyi magana."
D'ora k'afa d'aya kan d'aya yayi ya d'auki kofin glas d'in gefenshi da abun sha a ciki kalar ja ya kurba sannan yace "Ina jinki, zauna."
Inda ya nuna mata ta zauna ta kalla sannan ta kalli kofin daya aje gefenshi, kai tsaye dai bata ce barasa bace, amma dai ta d'an ji tana shakku duba da kwalbar data gani zungureriya a ajiye, a hankali ta k'arasa ga kujerun na alfarma royal da kula k'irar Italy, zaunawa tayi kamar akan k'aya sannan ta kalleshi, ganin ya sakar mata murmushi ya sa ita ma ta saki murmushin.
Da fara'a ya sake fad'in "Fad'i mana gimbiya ta, ina jinki."
A nutse cike da kunya ta fara alama da hannunta tana fad'in "Pah dama magana ce akan mutanen da suka zo gani na, sun zo da buk..."
D'aga mata hannu yayi yace "Gimbiya Zafeera, su ba mutane ne kamar kowane ba, talakawa zaki ce idan kina so na gane, ki dinga banbantawa."
Baki sake ta kalleshi sai kuma ta jinjina kai tace "To Pah, dama shi ne suka fad'a min ruwa ma da suke sha su talakawa siya suke, bayan kuma d'aya daga cikin magabata ne suka samar musu da su dan su sha kyauta, amma yanzu wasu ne suka mayar da hakan kasuwanci."
Irin kallon daya tsareta da shi yasa ta sunkuyar da kai, a dak'ile yace" Yanzu da kike fad'in duk wannan, me kike so na yi a kai?"
Cikin rawa da jikinta ya fara na tsoronshi da kwarjini yasa ta d'an muskuta tace" E to...ina ganin...idan.."
Sake d'aga mata hannu yayi yace" Dakat Zafeera, wa ya kitso miki duk wannan tsirfar da kika zo yanzu kike kora min? Yaushe kika zo nan d'in da har kika fara fahimtar matsalolin mutanen garin nan? Me kika sani? Me kike tunanin zakiyi?"
Yunk'urawa yayi ya mik'e tsaye tare da nunata yace "Kina ji ko, ba neman matsala bace ta kawoki nan, kin zo had'uwa dani ahalinki ne ba had'uwa da k'orafe k'orafen jama'ar gari ba."
Komawa yayi ya zauna tare da nuna mata k'ofa yace "Zaki iya tafiya."
Kamar zata fashe da kuka ta ske kallonshi tace "Pahh...ka ce zan had'u da Mah, kuma na ga har yanzu..."
Cikin jin haushi da tsawa yace "Kai! Wai me yasa kike da shan kai ne? Dama haka kike? Haka banzayen bayin nan suka raineki ko? Ki wuce ki bani wuri idan nasa an fito da ita zan sa a kiraki."
Mik'ewa tayi tsaye ta kalleshi, ita bat1 gusa ba ita bata sauke idonta ba, k'ura masa ido tayi tana kallo kamar mai son tsaorata shi.
Wani d'ar d'ar ya fara ji zuciyarshi na yi har da harbawar da baisan dalili ba, sai ga sarki Musail a gaban 'yarsa yana ta sissine kai, yana so dole ya kalleta ido cikin ido ya daka mata tsawa ta bashi waje, saboda ya nuna mata iko da izzarshi, amma kuma wani tasiri dake cikin idonta da suka ninka na shi kwarjini yasa dole yake kakkawar da na shi kamar mai jin kunyarta, gaba d'aya sai ya duburburce ya rasae zaiyi.
Ayam ma data fahimci haka sai ta ji ba dad'i ganin yanda mahaifinta ke mata, gyara tsayuwarta tayi tare da d'auke idonta daga kan shi, sanyaya murya tayi a nutse cikin ladabi tace "Ina so a fito min da sarauniya Juman, na zo ne dama saboda ita kuma idan na tabbatar da abinda nake son tabbatarwa zan bar nan da ita, ba sarautarku ta kawoni nan ba, saidai akwai abu d'aya da bana yarda da shi shi ne, *rashin adalci*."
Juyawa tayi a tsanake ta dinga takunta har ta fita a falon na shi, yanda ya idonshi suka kakkafe ya bita da kallo kamar ya ga gawa, rufo k'ofar da akayi ne ya dawo da shi hayyacinshi, a zabure ya lalubo wayarshi dake kan d'aya k'aramin teburin gefenshi ya danna wasu lambobin, ana d'agawa sarki Musail yace "...
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:38 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/