Sashe 67
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Dhurani ya mik'e yana fad'in "Ba zai yiwu na Musail, akan me zaka k'ask'anta ni haka? Ka sani wasa kake da wuta kuma zata k'ona ka."
A hassale ya kalleshi yace "Na yarda Dhurani, amma dole ka fuskanci k'ask'anci a rayuwarka kafin ka mutu."
Cikin fitar hayyaci ya fara fizge fizge saboda rik'eshi da Adah yayi yana fad'in "Musail sai na kasheka, sai na kasheka zan ji sauk'i a cikin zuciyata, kamar yanda babanka ya kashe min kakana, dole kai ma ka mutu mutuwar wulak'anci."
Da kallo suka bishi har Adah da wasu dogaran suka d'auki suka fice da shi, da mamaki Ayam ta kalli Musail tace" Pah, me yake magana a kai ne wai? Wacz d'aukar fansa?"
A tsaanake ya kalleta yace" Mahaifina ya kashe kakansa lokacin da kakanshi Allah ya masa baiwa kwatankwacin ta ki wacce ake alfahari da hakan, saidai kakan na shi yayi anfani da haka ta hanya marar kyau, a wasu k'auyukan talakawa na fama da matsalar ruwa, mahaifina ya rok'i alfarmarsa ya bayar da wani filinsa da bincike ya tabbatar za'a samu ruwan da gaba d'aya gari zai sha ya wadatu, amma ya k'i a lokacin, saida mahaifina ya siyi filin da manyan kud'ad'en da suka wuce k'a'ida, sun yi hakan a sirrance kamar yanda mahaifina ya buk'ata, sannan ya aje takardun filin na k'warai a hannunshi bayan sun saka hannu, hakan yasa har yanzu mutane ke ganin kamar kakan Dhurani shi ne ya zamar musu silar samuwan wannan ruwan, inda suka girmamashi suka d'aukakashi ya zama waliyinsu, hakan da ya faru shi ne mafarin matsalar da ta sa mahaifina ya kashe shi, saboda mahaifina yana da adalci ba kamar ni ba da zalinci ya fi yawa a mulkina."
Numfasawa yayi sannan ya cigaba da fad'in" Lokacin da mutane suke girmama suke zuwa da matsalarsu dan ya magance musu, lokacin ne k'anwar mahaifina ita ma ta je dan ya mata addu'a a gaban bak'in gunkin da suke bautawa dan ta samu miji tayi aure, saboda tun bayan mutuwar mijinta tana zaune gida babu aure, saidai madadin ya mata addu'a sai ya mata fyad'e, sannan ya tsorata da fad'in idan ta fad'a abun bauta zai la'anceta ba kuma zata ga biyan buk'ata ba, k'anwar mahaifina ba lusarar mace ba ce, dan haka ta tureshi daga jikinta sannan ta tabbatar masa zata fad'a dan mahaifina ya k'watar mata 'yancinta, jin haka sai ya tsorata ya kamata ya kuma shak'e wuyanta, bai saketa ba saida ya ga ta daina shurawa kad'ai alamar ranta ya bar gangar jikinta, da taimakon yaronsa na hannun damansa suka binneta a gonar wani manomi, saidai da ubangiji ya tashi kawo k'arshenshi, a sauk'ak'e aka tono gawarta saboda mammalakin gonar da ya ga abinda bai tab'a gani ba kuma ba shi yayi ba, bayan an tonone aka ga gawarta wacce lokacin hankalin masarauta ya tashi ana ta nemanta, wannan dalilin ne ya hassala mahaifina ya sa jami'ai a cikin lamarin, to fa shine da aka gano gaskiyar maganar ta hanyar amintaccen yaronsa kawai mahaifina ya cire masa kai ba tare daya jira hukuma ta d'auki matakin daya dace a kan shi ba."
Jiki na kakkarwa Juman ta kalleshi tace" Ba wannan ba, maganar aure... Ayam da Umad...me hakan yake nufi?"
Gyara zama ya kuma yi wanda Ayam ta kalli Umad ba ko k'yabtawa tana jira ta ji me mahifinta zai fad'a, cikin nutsuwa Musail yace" Tun daga sanda ya fara shigowa rayuwarki na samu labari daga gurin masu bibiyarki ba dare ba rana, da kallon fuskarshi a allon wayata da aka turo min na san ko wanene saboda kama da yake da sarauniyar Giobarh da kuma yayanshi Urab wanda na kasa yayin neman auren mahaifiyarki, bayanan da suka biyo bayan hoton su suka tabbatar min da kokonto na, bincike na sa aka min sosai a kan ka har saida na san abubuwa uku game da kai masu mahimmancin da ba kowa ya sani a ge da kai ba, na farko shi ne musulunta da ka yi iyayenka basu sani ba, na biyu kuma shi ne aikin sirri da kake da hukunmar binciken miyagun laifuka, na uku kuma shi ne k'udirinka akan Ayam, da haka nasan ranar da ka je gidan su Habbee ka kuma nemi aurenta a wajensu."
Da sauri Ayam tace" Pah ban gane ba? Ya nemi aurena kamar ya?"
Jinjina mata kai yayi yace" Hakane, ya nemi aurenki a wajensu, duk da ba amincewarki a ciki, amma ni na yarda da shi saboda mutumin kirki ne, zai kula da ke Ayam."
Kallon Umad tayi d kanshi ke sadde yana wasa da yatsun hannunshi, a sanyaye ta furta" Ta ya haka ma zata faru? Bayan babu soyayya a tsakaninmu."
Murmusawa Musail yayi yace" Zaku saba Ayam, da sannu za ki so shi, amma dai ba zan miki dole ki zauna da shi ba, dan na fi kowa sanin illar haka, akwai zuciyar da kyautatawa bata sa ta tausasa."
Had'a ido sukayi da Juman da sauri tayi k'asa da na ta tana mai jin kunyarshi, muryar Zafreen suka ji dake tsaye tace" Duk wannan ba shi zai sa na saurara ba, ka rabani da wacce ta haife ni, sannan ita ma ta rabani da wanda na ke so."
Ta k'arashe tana duban Ayam da ita ma ta kalleta a lokacin haka a Juman, da mamaki Juman tace" Wa ye kike sl da ta rabaki da shi haka?"
Nuna Umad tayi tace" Wannan ne."
Kallon Umad sukayi da yayi kamar bai san suna yi ba, Juman ce tace" Amma ai ita ma bata sani ba, ki bi komai a hankali mana Zaf..."
D'aga mata hannu tayi tace" Kinga ni ba da ke nake ba, hak'uri na hak'ura da shi dole, tunda na ji ya rabata da budurcinta daren shekaran jiya, amma ku sani wallahi ba zan rasa abunda nake so ba ni kad'ai, dole dukkanmu mu rasa wani abu da muke so."
Mik'ewa Juman tayi tana kallonta tace" Kamar ya? Me kike nufi?"
Tab'e baki tayi tace" Ina nufin dole na kashe yarinyar nan sannan na kashe shi shi ma.."
Ta k'arashe da nuna Musail, da sauri Ayam ta mik'e tsaye tana fad'in" Idan ina raye ba zaki kashe mahaifina ba, idan kuma ni zaki kasheni saboda Umad ne, to ki d'aukeshi na bar miki, ni ba wani damuna yayi ba..."
Ta k'arashe maganar da kallon gefen da Umad yake, duk da kansa a k'asa yake amma saida ya dakata da matsa hannayenshi da yake yana taune leb'ensa yana nanata kalmar *ba damuna yayi ba*.
A hankali Musail ya mik'e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace "...
*Ki garzayo ki biya na ki.*
*Alhamdulillah.*
01/01/2022 脿 11:43 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*39*
A hankali Musail ya mik'e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace "Na d'auka na raineki da kulawa, ki kashe ni ba damuwa, amma 'yata ki rabu da ita ta rayu cikin farin ciki."
Tsakiyar idonsa ta kalla tace "Ni ba' yar ka ba ce? Idan ka san ba ka so na me ya sa ka yi cikina?"
D'auke idonshi yayi daga kanta yace "Ina so na ji daga bakinki, shin da hannunki a wannan harin ko babu?"
A hassale tace "Da hannu na a ciki, kuma da taimakon wad'anda ba ka tsammani na zartar da hakan, d'ayan ka kama shi yanzu sai kuma ni da ke gabanka, amma na biyun ina tabbatar maka zai ga bayankkkka..."
Duk da ta kai k'arshen kalmar amma marin daya mata ya gigita ta sosai, k'ara ta saki ta da durk'ushewa tana dafe kunci, da sauri Ayam da ta fi kusa da ita ta sunkuya ta kamata sannan ta kalli Musail dake huci tace" Pah, ka yi hak'uri mana."
Tallabo fuskar Zafreen tayi dan ta ga ko bata ji ciwo ba, da k'arfi ta fizge fuskarta ta mik'e a hassale ta kalleshi sannan tace" Ko za ka kasheni ba zan canza k'udiri na a kan ka ba, mugu."
Juyawa tayi da sauri zata koma d'akinta sai kuma ta tsaya cak sakamakon fadawan da suka shigo da gudu gudu suka jeru a bakin k'ofar, daga ganin dakarun zaka fahimci daga masarautar da suke, Juman da ta fi kowa gane su wanene tuni ta mik'e tsaye tana zazzaro ido tana kallonsu.
Babban dogarin cikinsu ne ya fara shigowa hannunshi rik'e da bindiga dan bada tsaro, a bayanshi tsofaffin suka shigo, cikin nutsuwa da shan k'amshi suke takon, saidai fuskarsu ta nuna alamun tashin hankali da jimami, rik'e suke da hannun juna cikin shiga ta alfarma, fararen kaya masu ado kamar ba gobe, inda Bilkees ke sanye da wani babban lullub'i har yana jan k'asa.
Saman fuskokin da suka sauke dubansu yasa fuskarsu ta canza daga alhinin nan zuwa murmushi dake bayyanar da tsantsar farin ciki da kuma annuri.
Umad da Haman da shi dai tunda ake tattaunawar nan bai ce uffan ba ne suka mik'e a tare saboda girmamawa, Juman na had'a ido da iyayenta wani dad'i ya lullub'eta, da gudu ba tare da jin ta manyanta ba ta isa garesu, tana zuwa ta sake k'urawa fuskokinsu ido, ba ta jira komai ba ta fad'a jikin mahaifiyarta wacce ita ma k'walla suka fara gangaro mata.
Cikin kuka mai tsananin gaske Juman ta furta "Mah, na yi kewarku sosai."
Cikin kuka ita ma ta amsa da "Ni ma haka Juman, kin girma sosai."
K'am k'am suke mak'ale da juna hakan yasa sarki Abdallah rumgume su gaba d'aya yace "Ni ne ba kwa k'auna kenan?"
D'an d'agowa sukayi suna had'a ido ta fad'a jikinshi tana sake fashewa da wani kukan, daddab'ata ya dinga yi yana share k'walar farin ciki shi ma yana fad'in "Shikenan 'yata, ya isa haka, kukan ya isa haka."
Da sauri Ayam ma ta matso ta rumgume Bilkees, sun jima haka kafin ta d'ago tana murmushi saboda abinda sarki Abdallah ke fad'i cewa "Mik'o min matata nan na rumgume."