← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 86

Sashe 34

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bin bayanshi yayi da ido sarki Musail ya ma Dhurani signar ya biyoshi, shi ma wucewa yayi a k'arshe suka bar Zeyfi tsaye dan sauran abokan tafiyar sjna farfajiyar gidan, ganin haka ita ma sai ta koma ta zauna tana gyara lullub'inta ta maida hankalinta ga kallo b'angare d'aya kuma tana tunanin ko me ya sa ya zo nan da ita kuma?

A ciki kuwa zazzaune sukayi suna ta kallon juna kafin sarki Musail yace "Ina jinka? Me yasa ka sace min yarana duka biyun?"

Murmusawa yayi ya sauke numfashi yace "Ba na sacesu bane dan na cutar da su."

Da sauri sarki Musail yace "To me ka musu?"

Numfasawa yayi sosai ya d'an muskuta yace "A makarantar da su gimbiya suke akwai wasu makusanta na, daga bakinsu na samu labarin lallai ana bibiyarsu, da fari ban d'auki abun da mahimmanci ba saboda abunda ke tsakanin mu, amma a ranar da wata yar ajin su gimbiya Zafreen ta fad'a min ana shirin d'aukesu, sai na yi gaggawar tayar da hatsaniya dan na d'aukesu ba tare da hankalin kowa ya kai cewa su ne kawai aka rasa ba, sai dai kash ! Sarki Wudar yana da matuk'ar wayo da kuma mutane sosai, duk tsaron da nake ganin na ba wa gimbiyoyinmu saida ya d'auke mafi mahimmanci da tsadar."

Nisawa sarki Musail yayi yana kallonshi yace "Kenan yanzu gimbiya Zafeera tana hannun Wudar?"

Jinjina kai yayi yace "Shakka babu."

"Ta ina ya bi ya d'auketa a cikin gidan da kake ikrarin ka bata tsaro?"

Ya fad'a yana watsa mishi wani kallo, ba tare da alamar tsoro ko firgita ba yace "Na yi iya k'okari na wajen killacesu, saidai ko ma ta ya ya suka d'auketa a gidan nan na fi tunanin sa'ilin da sarki Wudar ya buk'aci mu keb'e ne ni da shi, to a lokacin mutanenshi suka d'auketa, ko kuma wannan d'an na shi."

Jinjina kai sarki Musail yayi yace" Shikenan, zai gane yana tare da kadarata ma fi tsada da daraja a duniya."

Da sauri Bukhatir ya kalleshi yace" Yawwa sarki na, ina so kayi iya k'ok'arinka wajen..."

Shiru yayi ya had'e maganarsa sakamakon kallon da sarki Musail d'in ya masa, sunkuyar da kan shi yayi yace" A gafarce ni."

Wani malalacin murmushi sarki Musail yayi yace" Har yanzu ban ji zuciyata ta gama yarda da kai ba Bukhatir, kai ma nasan kana son ganin bayana, ka samu Zafeera kuma ka rabu da ita ta sauk'i haka, da wuya gaskiya."

A ladabce yace" Ka yarda dani sarki na, babu hannu na a b'atanta, hasalima sanda sarki Wudar ya zo ya so yi min tayin gimbiya Zafeera da duk abinda ya mallaka, amma na nuna mana darajarta ta wuce haka."

Wata yar dariya yayi yatsare shi da ido yace" Amma me ya kai shi gidanka a ranar data kasance tana gidanka?"

Kura masa ido yayi yace" Iyeh?"

Wani kallon firgitarwa Dhurani ya masa yace" Aka ce me ya kai shi gidanka a wannan lokacin? Wata k'ulalliya xe a tsakaninku ?"

Girgiza kai yayi yace" Kamar yanda na fad'a maka yana da mutane da dama da suke masa lek'en asiri, kar ka k'aryatani idan har na fad'a maka a masarautar nan ma yana da yan sa ido, dan ta hakane ya samu cikakken labarinta."

Kallonshi yayi kamar zai hango gaskiya a fuskarshi sai kuma yace" Na yarda da abinda ka fad'a yanzun, amma Bukhatir..."

Ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya d'ora da" Alamu sun nuna a matse kake da son ganin an samo gimbiya Zafeera, shin idan aka yi hakan me ye tukuicinka kai?"

Gaba d'aya gabansa ya yanke ya fad'i ya shiga tunanin abinda zai fad'a masa, amma yanda ya tsareshi da ido yasa dole ya sunkuyar da kai yace "Farin ciki ma ya wadace ni idan har d'iyar yar uwata ta fito a hannunshi cikin k'oshin lafiya."

Dariya sarki Musail ya bushe da ita kamar wani mahaukaci ya dinga gaggab'awa, da k'yar ya tsagaita kuma kamar ba shi ba ya kalli Bukhatir fuska a hade yace "Shikenan, zamu gani."

Juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "Ba dan kar ka fita kana fad'in ban iya tarban bak'i ba, da ko ruwa ba zan ba ka ba Bukhatir dan nasan manufarka a kai na, amma karamci na ya isa insa a wadataku da abinci ko dan labarin daka siyar min."

Da mamaki Bukhatir ya kalli k'eyarsa cike da takaicin wulak'ancinshi, wato ya ma d'auki abinda ya fad'a masa a matsayin labari har kuma ya siya? Sarki Musail ne ya katse masa shirunsa sanda ya juyo a hankali ya kalleshi yace" Ya suke? Suna cikin k'oshin lafiya?"

Wani kallo Bukhatir ya mishi yana ji kamar ya mik'e ya shak'eshi, wallahi da yana da sarauta a lokacin babu abinda zai hanashi d'urawa Musail ashar saidai duk su k'one a nan, iyayen Juman fa yake tambayarshi, shi bai san komai ba dangane da yanda aurensu ya kasanxe da Juman, amma dai tabbas ya fahimci akwai barazana a ciki wacce ita ce ke d'awainiya da iyayenta har yanzu, tunda ya d'auketa daga garesu shekara ashirin da bakwai har yau bata tab'a taka k'asar Egypt ba ko da sunan taro bare da niyyar ganin mahaifanta, hakazalika su ma basu tab'a yunk'urin kawo mata ziyara ba, tsufa ya cimmu su sosai amma damuwarta ita ce ta k'ata tsofar da su, dan wasu lokuta har k'aura sukeyi daga masarauta su ware kansu gefen gari su hana kowa zuwa inda suke.

Amma dan rashin mutumci shi ne yake tambayar wai suna lafiya? Da k'yar ya d'aga labb'anshi yace "Suna lafiya, sai dai ba sa cikin farin ciki."

Tab'e baki Musail yayi yace "Hakane zai kasance dama, kuma kai ma nasan ba ka farin cikin, amma ka sake jaddada musu su sake yin nesa da ita, dan halin da take ciki yanzu idan suka ji zuciyoyinsu bugawa zasuyi su mutu a take."

Yar harara Bukhatir ya wurga ma k'eyarsa sannan ya jinjina kai alamar to, ficewa yayi Dhurani na bin bayanshi shi kuma ya bi su da kallo da son sanin me kuma ke faruwa da Juman d'in? Tana ina ma? Me yake damunta? Shin tana farin ciki da auran waccen dabban ne ko kuma a'a?

Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad'i ya d'auke kan shi daga k'ofar yana d'an jan tsaki, mik'ewa yayi ya fito ya dawo falon ya samu Zeyfi zaune tana kallo, haushi ya ji ta bashi da kallon fuskarta, gefenta ya zauna yana sake murtuke fuska, ita kuma cikin ladabi ta kalleshi tace "Lafiya ko? Me kuka tattauna haka? Naga kamar ranka b'ace?"

Ture hannunta yayi data dafa na shi hannun yace "Ba komai malama, zaki iya yi min shiru."

A sanyaye tana had'e kukan dake taho mata a mak'osho tace "Me zai hana?"

D'ora kan ta tayi bisa kafad'arshi taake cukukuiye hannunshi tana siraro yar k'walla, cikin jin haushi ya kalleta dan har k'asan zuciyarshi yake jin tsanar yarinyar, baya sonta bai kuma tab'a son ta ba, ita kawai zab'in mahaifinsa ce ba yanda ya iya, amma shi kad'ai yasan irin dakon kayan da yake a game da ita, zama da wanda baka so babban k'unci ne da zai iya baibaye maka rayuwarka har abada, indai yana kusa da ita to baya farin ciki bare murmushi, ita kuma ga ta da na ci da jaraba a ganinshi, shiyasa in zaiyi wata bai nemeta idan ta kai kanta gareshi sai ya kirata da jarababbiya mayya.

Yanzu ma ya so tureta daga jikinshi, amma daya tuna sarki Musail ya ce zai wadatasu da abinci saiya k'yaleta, ammafa sai tsaki yake yana ta had'e fuska kamar kashi nea jikinshi, yayin da ita kuma take jin wata nutsuwa na sauka a zuciyarta na ganin bai turetaa jikinshi ba, sai ta ssamu kan ta da sake shige masa tana sauke ajiyar zuciya.

*Giobarh*

*Da yamma* sarki Wudar na zaune a lambun cikin masarautar tare da fadawa biyu dake nesa da shi yana jin dad'in yanayin, wazirinsa ne ya shigo bayan mai tsaron k'ofar ya masa izinin shiga, da sauri kamar zai tashi sama ya k'araso, zube gwiwoyinshi yayi k'asa yana mik'awa sarki Wudar takardar hannunshi yace "Shugaba na, gashi, akwai matsala fa babba."

Rai b'ace ya kalleshi ya karb'i takardar yace "Waziri ba na fad'a hutu nake buk'ata ba kar wanda ya dameni?"

A kid'ime yace "Ka gafarce ni yallab'ai, wannan takardar ta fito ne daga sarki Musail, hankalina ne a tashe shiyasa."

Da sauri ya shiga warware takardar ya k'ura ido dan karantawa, firgitattun kalamai ne kamar haka _"Daga yanzu zuwa wayewar garin gobe ina buk'atar ganin 'yata gimbiya Zafeera dake hannunka, watsar da buk'atata kuma yana nufin yak'i kake nema da ni, kuma a shirye nake da fuskantarka dan ina da adadin dakarun da zasu iya k'wato min babbar kadarata."_

A razane ya kalli wazirin yana jin zufa zata keto masa, jefar da takardar yayi ya tunkari hanyar fita, da sauri wazirin mmaa ya bi bayanshi yana mai son jin hukuncin da sarki Wudar d'in zai yanke, dan in har ya zab'i yak'i da sarki Musail to fa shi dai kam babu hannunsa, magana ta gaskiya ma zai tattara iyalinsa su bar k'asar har su gama sai ya dawo, dan ya sani ne ba zasu iya da sarki Musail ba, alfaharinshi kad'ai ya isa ya saka shi d'auko wasu rundunoni daga mak'wabtan masarautu dan su yak'esu su kuma yi kaca-kaca da su.

*Ayam* na d'akinta zaune duk ta matsu dare yayi ta ga abun bazatar nan ta ji an banko k'ofar an fad'o, da sauri ta mik'e tsaye tana gyara rigarta, da ladabi tace "Barka yallab'ai."

Murmusawa yayi tare da saita nutsuuwarshi wuri d'aya sannan yace "Barka gimbiya Zafeera."

Kallon idonshi tayi tace "Yallab'ai, zan fi jin dad'i idan ka kirani da Ayam."
Chapter 34 · 0% Book details