← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 86

Sashe 13

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin taushin murya yace "Ayam, me ye dalilin da yasa kika mari gimbiya Zafreen? Shin ban fad'a miki ki fita a sabgarta ba?"

Gyara tsayuwarta tayi ta juya ta kalli Zafreen d'in, sai kuma ta kalli waziri daya cika fam yana jiran fashewa, tab'e baki tayi ta kalli canal tace "Tun ranar ai na fita a harkarta, ita ce ta sake shiga hurumi na."

Wata irin tsawa ya daka mata tare da buga tebur din ya mik'e tsaye yana fad'in "Ke d'in banza, wacece ke da zaki ja da ita? Kinsan matsayinta a makarantar nan kuwa? To ko yanzu ta so z..."

A hassale ta kalleshi gaba da gaba ta zazzaro idon ta wanda launin shud'i yayi wani kore-kore ga mai kallonsu, cikin tsiwa da fad'a tace "Waye kai da zaka min tsawa? Uba na ne kai ? Na sanka ne? Ka zo d'aukar mata fansa ne? To ina jira kayi yanda zakayi da ni."

Sake k'ura masa ido tayi ta nunashi da yatsa manuniya tace "Malam murya k'asa, ni ba kowa bace amma haka kawai nake jin na tsani a d'aga min murya, kuma a jinina nake jin kamar ina da izzar da zan hukunta duk wanda ya min hakan cikin d'anyan kai."

Juyawa tayi ga canal, tuni ya gyara zamanshi yana ta k'yak'yabta ido, tabbas da yana da addinin musulunci a lokacin daya shiga karanto addu'ar tsari da shed'anu, sam bai yarda da Ayam dan lamarinta tsoro yake bashi, shi fa babu kamar ma yanda jikinshi ke d'aukar b'ari idan ya hangeta kawai, har ya kan tambayi kan shi k'awayenta da sauran mutane basa jin hakane ? Sai kuma ya ba kanshi amsa watak'ila dan sun saba da ita ne shiyasa, dan sun fad'a mishi tun suna yara suke tare tun a makarantar *Ansawwd* (ma'ana *inganci*).

A sanyaye kamar ba ita ba tayi kalar tausayi tace "Canal yarinyar nan fa marin k'awata tayi, kuma ka sani kai ma bana son a tab'a min k'awayena, to me yasa zan k'yaleta?"

Cikin sub'utar baki yace "Gaskiya ne, na sani Ayam, yanzu kiyi hak'uri ki je na jiranki zaku tafi jeji."

Wani k'ayataccen murmushi ta saki tace "Shukran."

Sakin baki yayi a ranshi yace "Yau ma wani yaren?"

Juyawa tayi cikin takon k'arfi da salo ta fita a ofishin babu wanda yayi yunk'urin hanata, Umad dake zaune mik'ewa yayi ya sarawa canal d'in sannan yace "Yallab'ai da izininka zan tafi."

Da hannu ya nuna masa k'ofa alamar ya tafi d'aya hannunshi kuma na share gumi da yayi, saida Umad ya fita Zafreen ta girgiza kan ta ta dawo hayyacinta, rarako idonta tayi tace "Kutumar can, wacece ita?"

Khatar daya kasa anfanuwa tunda ta shiga kora masa bayani ko k'yabtawa bai yi sai yanzu, cikin fitar hayyaci da rashin sanin me ya fad'a yace "Ta musamman."

"Me?" Zafreen ta fad'a a tsiwace, kamar mari ta gaura masa haka ya zabura ya juya ya kalli canal, cikin masifa ya shiga fad'in "Dama haka kake mata kashedin? Wai wannan wace yarinya c da kai kan ka ke tsoron had'a ido da ita? Me ta taka a k'asar? Dan gwamnati ta d'auki nauyin karatun ta ba shi ke nufin zata taka kowa ba, ka fad'a min wacece ita?"

Tsura masa ido canal yayi yace "Wacece ita?"

"E, wacece ita?" Ya fad'a a zafafe, numfashi ya sauke sannan yace " *Abinda idonka ya nuna maka*, ita d'in ita ce, bayan haka bansan komai ba."

Tsaki Khatar ya ja tare da juyawa ya kalli Zafreen yace "Zo muje gimbiya."

Da sauri suka fice a ofishin canal na kallonsu, saida suka fita har da bayinsu shi ma ya ja tsakin yace "Aikin banza, naga ma kai ka fini firgita da lamarinta tunda suman tsaye ka yi, can kuje ku k'arata da matsalarku da ita ni ku daina sakani, tunaninta kad'ai hawan jini yake tayar min."

*Ayam* kam na fitowa ta kawo daf da motocin da Khatar ya zo ta tsinkayi muryar Umad yace" Ke."

Yi tayi kamar bata ji ba ta ci gaba da tafiya, sake fad'in yayi" Ke."

Nan ma ko waiwaye bare hasa ran zata tsaya, saida ya bushi iska ya daddage yayi ta maza yace" Ayam."

Cak ta tsaya tare da juyowa tana murmushi tace" Na'am yallab'ai."

Gyara tsayuwarta tayi saida ya k'araso yana d'an cije leb'e da mamakin kenan ta ji banza ne ta masa? Tsareta yayi da ido kamar mai son gano wani abu a fuskarta sannan yace" Me yasa kika wa babban mutum fitsara? Dama rashin kunyarki ta kai haka? Sannan me yasa kika mareta?"

Ajiyar zuciya ta sauke irin ka dameni d'in nan sannan ita ma ta zuba idonta a na shi a yaren Italy tace"...

*Saura k'iris a rufe free page, hanzarta ki biya na ki, farashin mai sauk'i ne.*

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:32 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*8*

Cikin yaren Italy tace "E tu? Il figlio verde o uno dei loro cortigiani (kai kuma fa? D'an korensu ko d'aya daga cikin fadawansu?"

Zaro ido yayi a tsawace cikin b'acin rai yace "Silenzio! Omicidio cosa ci dirai, pazzo (shiru ! Ki dinga sanin me zaki fad'a mana, mahaukaciya)."

Cike da shak'ihanci ta gyra tsayuwa tace "Kai ma ka dinga sanin sunan da zaki dinga kirana dashi malam."

Girgiza kai yayi irin na takaicin nan yace "Nonsense (shashanci)."

Murmushi tayi tace "I'm not talking about nonsense, I'm telling you so i can do what you don't expect (ba ina magana bane akan shashashanci, ina fada ne dan zan iya yin abinda baka tsammani)."

Da mad'aukakin mamaki yace "How do you change language like this? Who are you (ta ya kike iya canza yare haka? Wacece ke)?"

Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi tace "Tu me prend juste comme tu me vois, je ne sais m锚me pas, c'est juste moi (Ka d'auke ni a yanda ka ganni kawai, ni kai na ban sani ba, ni ce kawai)."

Juyawa tayi a sanyaye zata tafi ya bita da kallo, gyara tsayuwa yayi har ga Allah jiri yake ji na son kwasarshi ya jefar a k'asa, yarinya kamar aljana ko wata matsafiya, da sauri ya girgiza kan shi ya kawar da abinda zuciyarshi ke sak'a mishi a kan ta, takawa ya shiga yi da k'arfi k'arfi har ya isa garesu inda suke tsatsaye.

Ganinshi ya taho yasa d'aliban duk suka dinga shiga cikin motar wasu ta k'ofar gaba wasu ta baya, Ayam ma na daf da shiga ta ji an ce "Gimbiya ta."

Da farin ciki ta kalli inda ta ji sautin kuma ta gane sautin waye, da gudu ta sauko a matakalar ta nufeshi tana fad'in "Pah."

Tana zuwa ta bud'e hannaye zata fad'a jikinshi kawai ya rusuna kamar yayi ruku'i, hakan ya k'ara saka Umad ghara tsayuwarshi yana kallonsu.

Marairaicewa tayi ta turo baki tace "Pahhh? Me yasa?"

D'agowa yayi yana dariya yace "Tuba nake, ai ba laifi nayi ba dan na kira gimbiya ta da gimbiya."

K'arasawa tayi ta bud'e hannayenta ta rumgume shi tsam tana sauke ajiyar zuciya, bai yarda ya rik'e jikinta ba, dan wanda tayi ma suna d'aukan hakan wata alfarma ce garesu, su suka raini yarinyar tun tana k'arama, sun sha al'ajabi da mamaki a game da abinda ya shafeta, har wasu lokuta sukan shiga yanayi na tsoro da fargaban ko dai ba mutum bace, lallai sun yarda rashinta a msarautar nan shi ne yafi alkairi.

Hannunshi dake b'oye a bayanshi ya fito da shi cikin murmushi yace "Gimbiya ga kyautar ki."

D'agowa tayi ta kalleshi tasa hannu biyu ta karb'a tana dariya tace "Amma Pah ai gobe ne ranar, me yasa ka kawo min kyauta yau?"

Da fara'a a fuskarshi yace "Maman ki ta fad'a min kin je bana nan, kuma kin kira kika tambaye ni, shiyasa na kawo kai na kafin ki sake nema na."

Fad'ad'a murmushinta tayita sake rumgume shi tace "Thank you Pah, I'm so proud of you."

Kallonta yayi a ladabce yace "Na sha fad'a miki bana gane kowane yare bayan na slovaque da azharbaijan, ban fahimci me kika fad'a ba."

Had'e murmushinta tayi tace "Pah, dama ina so na tambaye ka, wai me yasa sai na dinga yin yaren da ni kaina ban sani ba? Na lura hakan ya fara tsorata mutane game da ni."

Girgiza kai yayi yace " Ban sani ba, bansan komai akan haka ba, ina ga baiwarki ce haka."

Cike da gamsuwa ta saki fuskarta tace" Pah, ce wa nayi nagode sosai, kuma ina matuk'ar alfahari da kai."
Chapter 13 · 0% Book details