← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 86

Sashe 60

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rik'e hab'a sarki Musail yayi a dak'ile yace "Wane irin labari kuma waziri?"

A sanyaye yace "Ranka shi dad'e, gimbiya Zafeera ce aka farmaketa a d'akin sarauniya, yanzu haka sun tafi asibitin cikin gida."

A kasalance sarki Musail yace "Kenan bata mutu ba yanzu ma? Wai wane irin mutane ake ba wa aikin nan ne?"

Kaf fadar suka dinga kallo kallo sai Dhurani daya kalli sauran fadawan da basa cikin tsarinsu yace "Zaku iya jira a waje, da alama mai martaba na cikin alhini."

Jiki a sab'ule cike da takaici suka mik'e suka fita, wanda ya rage Khatar ne da shi Dhurani sai kuma Adah, da sauri Khatar ya kalleshi yace "Sarki na, da alama akwai mai ruguza mana tsarinmu, jiya cikin dare mutanenmu sun ziyarci d'akin gimbiya Zafeera, amma basu sameta gaba d'aya, saidai ko ma waye ya kai mata farmakin nan yanzu, bana jin d'aya ne daga cikin mutanenmu, dan har yanzu babu wanda ya tuntub'e ni da maganar."

Da mamaki Dhurani yace" To wa ye kenan ya yi?"

Girgiza kai Khatar yayi yace" Ban sani ba gaskiya, sai dai nan gaba zamu sani."

A k'ufule sarki Musail ya kalleshi yana ji ya shak'i wuyanshi sannan bakinshi ya furta" Kai Khatar 'yar ta wa kake so ka kashe? Yata ta ciki na? Shin me ta tsare maka a rayuwa?"

Amma sai ya dake yace" To wane irin hwanb'asawa kake game da lamarin? Ba dan ka ce na bar maka a hannunka ba, da yanzu na shak'e wuyanta."

Da sauri Khatar yace" A' a yallab'ai, ai shi yasa na ce zan yi komai, kar ka d'auki matakin nan da hannunka, ina k'ok'ari a kai."

Cikin d'aga murya yace" Wane k'ok'ari ka ke?"

Cikin ladabi yace" Yallab'ai ai jiya mun yi k'ok'arin ciyar da su guba a abinci, amma sai wani abu ya faru suka tsallake wannan tarkon..."

D'aga masa hannu yayi tarz da duk'ar da kanshi k'asa, k'afarshi dake sanye cikin takalmi masu kyau da k'yalli ya dinga buga k'afar d'aya bayan d'aya, wani huci ya fara jerawa yana saukewa, jikinshi rawa ya fara d'auka tsabar takaici da k'uluwa, d'aga kanshi yayi da sauri ya mik'e tsaye da wani irin sauri ya kama hanya ya fita tsabar haushi har k'afafunshi na hard'ewa.

Da kallo suka bishi har da Adah ma daya bi bayanshi da sauri yana hararen Khatar, kallon junansu sukayi Khatar yace "Me ya faru kuma?"

Girgiza kai Dhurani yayi yace "Ba na ce ba, ban dai fahimci komai ba, duba da ko halin da aka fad'a masa 'yarsa na ciki bai damu ba."

Cikin rad'a Khatar yace "Ko dai bai ji dad'i ba ne da na fad'a masa."

Harara Dhurani ya wurgawa k'ofar kafin ya kalli Khatar yace "Rabu da shi."

*Sarki Musail* na fita daga nan cikin sauri ya shiga takawa zuwa asibitin, da girmamawa Adah yace "Ranka shi dad'e, ka bari a d'auko mota."

A hassale yace "Ni rago ne ? Na ce ba zan iya tafiya can d'in ba?"

Wucewa yayi kamar zai tashi sama Adah na bin shi, daf da k'ofar shiga Umad ya zagayo ta bayan asibitin shi maa kid'ime suka kacame, turus sukayi suna kallon juna sai kuma suka fara k'ok'arin shigewa.

Karo sukayi da juna hakan uasa Umad dakatawa Musail ya wuce sannan ya shige shi ma da gudu, inda suka ga Juman tsaye suka tsaya a tare suka had'a baki wajen fad'in "Ya jikin ta?"

"Ya jikin ta?" Kallon juna sukayi sai kuma suka kalli Juman da ta ja majina tace "Ban sani ba ni ma, tana ciki har yanzu basu fito ba."

Lumshe ido yayi ya jingina a bango ya rumgume hannayenshi, k'ok'arin dakatar da zuciyarshi kawai yake akan abinda take raya masa, sam baya so ya fara d'aukan mataki sai ya ji halin da take ciki, indai har aka fito masa da gawarta yanzu, to shakka babu Zafreen ma za ta bi yar uwarta ba da jimawa ba, dan a dalilinta zai bayyana waye shi a duniya.

Tsantsar tashin hankalin shi ne rasa dalilin da yasa za ta yi haka, saboda sarauta ne? Ko kuma dai son zuciyarta? Ko kuma wani ya sakata? Girgiza kai ya fara yi a hankali idonshi a rufe yana jinjina lamarin.

Takon takalmin da suka ji a bayansu an shigo ne yasa su juyawa shi ma a nutse ya bud'e ido, zuba mata su yayi tun daga k'asan takalminta masu tsinin gaske bak'ak'e, zuwa dogon wandon jikinta daya kamata bak'i, sai rigar mai siraren hannaye ita m bak'a da gashinta data d'aure, dan kyau kam akwai shi, saidai kyan d'an maciji ne.

Sarki Musail ma kallonta yake da mamakin abinda ya kawota, idan har ta san me ya faru shi ne zata shigo haka? Ba wani alamar abun ya dameta a matsayin Zafeera na yar uwarta, girgiza kai shi ma ya d'auke kanshi daga kallonta, tana zuwa ta ja birki ta tsaya ta kalli Juman a shek'e tace "Mah, ta mutu ne?"

Wannan tambayar da tayi ita tasa kowa dake wurin kallonta, gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k'ugu d'aya irin zai kirta rashin mutumcin nan yana kallon k'wayar idonta yace "...

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*35*

Gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k'ugu d'aya irin zai kirta rashin mutumci nan yana kallon k'wayar idonta yace "Ki zo kin ji ta mutu ne dalilin yankan da kika mata?"

Wur wur ta kalleshi tana wurga ido zuwa fa Juman da sarki Musail, k'are masa kallo tayi ta rik'e wayarta da kyau tace "Me kake fad'a ne haka?"

Rai b'ace ya girgiza kai tare da tab'a ta ya koma d'aya b'angaren ya tsaya, dan in takura kanshi wajen yin magana, to shakka babu kasheta zaiyi da marin da ba lallai ta rayu ba, idan kuma ta rayu ba zata rasa kamuwa da matsalar ji ba.

Juman dake ta kallon Zafreen d'in ce ta girgiza kai tace "Akane Zafreen? Yar uwarki ce fa."

Wani mugun kallo ta mata kafin ta d'auke kan ta zuwa ga k'ofar da aka bud'e, a hankali aka turo gadon da take kwance a kai an mata allurar bacci da kashe zafin jiki kafin aka mat d'inki a wurin.

Duk rufa sukayi kan su har aka fito da ita gaba d'aya, kallonsu likitar tayi tace "Ba ta cikin had'ari yanzu, idan ta samu hutu zata wartsake."

Dafe k'irji Juman tayi tace "Alhamdulillah."

Turata aka yi zuwa d'akin hutu inda Juman ta bi bayansu, saida suka shige d'akin Zafreen ma ta juya a fusace ta bar wurin takalminta na k'ara, ita ma tana ficewa sai suka kalli juna Umad da Musail, kallo irin gwada gwa, hannu ya zura aljihu ya ciro makullin motar da ko ina yana tare da shi, mik'a masa yayi yasa hannu ya karb'a ba wanda yayi magana Musail d'in ya bar asibitin shi ma Adah ya rufa masa baya, suna fita b'angaren shi yayi yana bayar da umarnin "Adah ka kira min Khatar a b'angarena yanzu yanzu."

Rusunawa yayi yace "To ranka shi dad'e." Ya fad'a yana ratse hanyar da suke bi a tare.

*Suna* fita Umad ma kiran sarki Abdallah yayi ya fad'a masa halin d ake ciki, cikin tashin hankali sarki Abdallah yace "Ya take yanzu Umad? Tana ina?"

A sanyaye yace "Tana lafiya yanzu, ga ta can d'akin hutu."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah, na ji dad'in haka."

A dak'ile Umad yace "Sai dai kuma akwai matsala."

Nutsuwa yayi sosai yace "Wace irin matsala Umad? Me ya faru?"

A nutse ya sanar da shi abubuwan da suka faru daga zuwanshi, madadin mamaki da wasu tambayoyin sai kawai ya ji yana murmushi mai sauti yace "Umad, Umad, shi ne ka tare da amaryata ba sanarwa ko? To gobe zan shigo Khazira, shigowa ta farko bayan aurar da 'yata, kuma a fadar Musail zan sauka dan a shirye na ke da shi, sannanba ni kad'ai ba har da sarauniyata, dan ita zata raka maka amaryarka d'akinta."

Yar dariyar da bai zata ba ce ta kubce masa yana girgiza kai, shiru da dukansu sukayi ne yasa a tare suka d'auke wayar daga kunnensu.

*A* wajen Musail kuma yana tsaye a falonshi yana safa da marwa Adah ya dawo tare da Khatar, suna shigowa ya kalli Khatar saida ya zo daf da shi ya tsaya, rusunawa yayi yace "Sarki na ka ce in zo?"

Dafa kafad'arshi yayi tare da zagayashi cikin tako d'ai d'ai yana fad'in "Khatar kasan wani abu kuwa? Na jima ina taraka, na dad'e ina rik'eka a zuciyata, amma alamu kullum nuna min su ke ni d'in nan dai ni ne zan ga bayanka."

A rikice ya juya ya kalleshi cike da neman k'arin bayani yace "Ranka shi dad'e, ban gane ba? Me kake fad'a ne haka?"

Murmushi ya sakar masa tare da zagayowa gabanshi ya kalli fuskarshi yace "Kar ka damu, zaka fahimta yanzu."

Ba tare daya d'auke hannun daga kafad'a ba yace "Khatar, nasan abubuwa da dama da kuka aikata min kai da Dhurani, tabbas ni mugu ne kuma azzalumi, amma ba shashasha ba, lalacewata bata kai matakin da zan so kashe 'yata ta cikina ba saboda son mulki, hasalima yarinyar da kuke ganin kamar ina k'in ta ne, tsananin azababbiyar soyayya na ke mata, soyayyar da ko mahaifiyarta bana jin tana mata ita."

Wani mugun kallo ya masa yace" Shi ne ka yi k'ok'arin kasheta? Kuma ma harda matata? Matar da na fi so a rayuwata?"

Girgiza masa kai yayi yace" Ka yi kuskure, ka yi kuskure Khatar."

Hannu ya mik'awa Adah shi kuma ya ciro wuk'ar dake k'ugunshi ya mik'o masa, yana damk'e wuk'ar a hannu bai yi wata wata ba wajen rumgumo shi jikinshi ya burma masa wuk'ar nan a ciki, k'arar daha bud'a baki zai yi sai kuma Adah ya koma ta bayanshi ya murd'e masa wuya tsaf, daga haka suka gama da Khatar aka rufe babinshi.

Za a iya cewa mutuwar kare Khatar yayi, dan uamrni ya ba wa Adah a jefar da gawarsa nesa da nan inda kafin a gano shi ya kashe shi lokaci ya ja.
Chapter 60 · 0% Book details