← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 86

Sashe 16

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon daya mata yasa tayi shiru tana sinne kai, matsowa yayi daf da ita yace "Nake k'ok'arin yi miki me?"

Yanda ta sake soke kai k'asa yasa shi sakin murmushi a ran shi yana jin kanshi na huruwa sama na farin cikin ya tsorata ta ta k'i fad'an abinda tayi niyya, juyawa yayi yana sake maida hankalinshi kan sautin nan da yake ji, a bazata ya ji muryarta tace" Zaka min rashin d'a'a mana."

Lumshe ido yayi tare da juyowa, da yatsu biyu ya mata kurmanci ya nuna mata" Ki maida hankali, akwai abinda ke tahowa ta nan."

Jinjina kai tayi fuskarta fal tsoron abinda ya fad'a d'in, yanda yake sand'a ita ma haka take yi tare da ciro bindigarta ta kashe jiki ta rik'e da kyau, sautin k'ara kusanto su yake, kamar numfashi had'e da gurnani, abinda ya sani kawai shi ne idan ma dabba ce to babba ce daga yanda k'ananan tsirrai ke motsawa, duk da ba'a jin sautin tafiya, amma sai dukansu jikinsu ya basu lallai fa kamar ana sauke takon k'akk'arfar k'afa a zuk'atansu.

Kamar almara ko a mafarki sai ga k'osasshen zaki ya b'ullo daga sark'ak'iyar itacen da duwarwatsu, tuni Umad ya zaro ido dan wallahi a take ji yayi wannan zakin shi ne wanda aljanar nan ta fasalta, dan ba k'arami bane wajen girma haka ma a shekaru, dan fuskarsa ta nuna haka, lalubo hannun Ayam yayi da ta lek'a ta kafad'arshi, tana ganin zaki ta saki fara'a cikin jin dad'i tace "Oh my God, lion."

Da azama ya juya ya fuskanceta ya d'ora yatsarshi a labb'anshi yace "Shiiiiiii."

Juyawa yayi ya kalli zakik dake tafe a tak'ama da gadara, ga dukkan alamu ihunta ne ya fargar da shi cewa an shigo komarshi, ko kuma dai shawagi ne ya ke amma ba farauta ba.

Had'e yawu yayi ya laluba a hankali ya cire gilashinshi ya soka a gaban rigarshi mai mab'allai, sake damk'o hannunta yayi da niyyar su ratsa ta b'angaren hagunsu su zagaye zakin su fita dan su tsira da ransu, sai dai suna fara takawa kamar sunanshi ne suka kira sai kuwa ya juyo ta bangaren da suke.

K'amewa Umad yayi ya rintse ido yana furta "Hasbunallah wani'imal wakil."

Haba wa? Ai sai zakin nan yayi wata kukan kura, gudu cikin k'arfi da salo ya yo kan su, Umad na ganin haka ya ja hannun Ayam da gudu, tsaf ta kubce hannunta daga na shi ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci zakin.

Umad dya tsaya ya ga me ya tsayar da ita yana ganin zakin nan ya nufo kan ta cikin gurnani bakinshi a bud'e, bai san me ya aikata haka ba, a kan wani dalili ya ji zai iya fansar rayuwarta, shi dai ji yayi kawai ba zai iya bari komai ya sameta ba, dan haka yayi gaggawar tureta gefe ya tsaya inda take, bindigarshi ya saitawa zakin ya rik'e da kyau yana jiran ya ga me zai faru.

Zakin nan na zuwa bai b'ata lokaci ba wajen nuna izzarshi, wani irin tsalle ya daka sama sai kuwa a jikin Umad bayan ya saki duka faratunshi, tare suka fad'i inda bindigar ma tayi ta kan ta, wata irin mirginawa zakin yayi y ske mik'ewa tsaye, Umad ma duk da bala'in dukan nan da yaji bai hanashi jarumtar tashi ba.

Sake shirin kai farmaki yayi a karo na biyu, saidai ina gaba da gabanta, tuni Ayam ta shiga tsakanin Umad da zakin nan kan gwiwarta tana d'aga masa hannaye alamar sun yi saranda sun mik'a wuya, ai Umad yanda kasan idonshi zasu fad'o k'asa haka yayi dan al'ajabi, kallon zakin yake irin yanda ya tsaya cak suna kallon juna ita da shi.

Juyawa yayi ya hangi bindigarshi, gyara zamanshi yayi zai rarrafa ya d'auka Ayam tayi saurin juyawa ta kalleshi, da hannu ta masa alama a hankali tace "Shiiiiiii!"

Da mamaki bakinsa a sake yace "Kuuuutt! Ni d'in?"

K'uro idonta tayi sosai ta d'ora yatsa a labb'anta cikin rad'a tace "Kayi shiru mana, na maka alk'awari ba zan fad'awa kowa kana tsoronshi ba."

Juyawa tayi ta kalli zakin, a hankali ya dinga takowa har saida ya tsaya gabanta, lumshe ido tayi dan ita kan ga zuciyarta rawa take tana jin me ye a jikinta da yasa zakin ya daina hargagin son halakasu? Me ma yasa tayi tunanin shiga tsakaninshi da Umad ne?

Gashin da ta ji na tab'a jikinta yasa ta bud'a ido, cike da d'ard'ar da tsoro ta kai hannunta na hagu ta shafa gashin nan, sai kuwa zakin nan ya sake kwantar da kan shi a jikinshi, dariya ce ta sub'uce mata ta juya ta kalli Umad tana fad'in "Yallab'ai ka gani, na tab'a shi yau, burina ya cika."

Sake juyawa tayi ga zakin ta ci gaba da shafa shi har zuwa bayanshi, kallon idon juna suke ita da zakin. Umad kam mik'ewa yayi tsaye ya d'auki bindigarshi, zai saka a k'ugunshi ya ji Ayam tace "Sunana Ayam, kai fa?"

K'ura mata ido yayi har ta kalleshi ta nunawa zakin tace "Malami na ne, sunan Umad."

Da sauri Umad ya k'arasa ya gareta ya finciko hannunta yana fadin "Tashi muje na maida ke inda na d'auko ki, rayuwa cikin mutane bata kamace k..."

Wata zaburowa zakin yayi ganin yanda ya finciki Ayam, tuni suka ankara Ayam ta dakatar da shi da hannu Umad kuma ya k'urawa zakin ido, sake durk'usawa tayi kan gwiwanta ta marairaice tace" Zan tafi ka ji, abokina ne shi kar ka cutar da shi, zan dawo wani lokacin."

Mik'ewa tayi bayan ta sake shafa gashin nan na shi ta bi bayan Umad, sauri take kamar yanda shi ma yake yi hankalinsa a matuk'ar bala'in tashe, idan kai na bindiga ya fashe to tabbas na shi zaiyi kowane lokaci, gashi wata zuciyar na ta fad'a masa ita ce, amma sai ya kawar da zancen saboda tunanin ta ya zai sameta a b'agas haka? Sannan yanda aka suffanta kyawunta wannan ko kama k'afarta ba tayi ba, da ma dai kyawunta ya kai na Zafreen zai iya yarda.

To amma kuma wasu halaye da d'abi'unta abun tsoro yake son fara bashi, sai kuma yanzu ya fara gasgata canal Jacob da yaga ko fuskarta baya kalla.

Sautin dariyarta da yaji ne yasa shi juyowa a hankali, wani k'arami kuma mai kalar shud'i da yellow d'in tsuntsu ne ya gani a tafin hannunta tana wasa da shi kamar tana masa cakulkuli, da azama ya dawo gareta ya d'auki tsuntsun ya d'aga hannunshi sama ya tashi, a karan farko daya tab'a ta da niyya kenan, hannayeshi biyu ya sa ya tallabi fuskarta suka kalli juna.

Muryarsa na rawa kamar wanda ya kid'ime yace "Ke! Kalle ni da kyau, ki wa Allahn daya hallice ki karki haukata ni, ki fad'a min gaskiya Ayam, who the hel are you?"

Yanda ya matse kumatunta yasa bakinta kumburowa, cikin shagwab'a ta kalli idonshi ita ma tace "Ni ce, Ayam... Utais."

Cikin jin haushi ya saketa ya juya yace "Merde."

Murmushi tayi ta bi bayanshi saboda ya ci gaba da tafiyarshi, k'asa ta shiga kallo tana tafe tana rausayarta, tsautsayi yasa idonta sauka akan wata k'atuwar wahainiya kore shar da ita, bud'e hannayenta tayi ta sunkuya kamar zata rumgumeta tace "Wow! Wahainiya."

Da sauri ya juyo ai kuwa da gudu ya arta ya damk'ota dan tayi niyyar bin bayan wahainiyar, yana nasarar cabkar k'ugunta ya cirata sama ya labta a wuyanshi, cikin takon k'arfi da sassarfa ya shiga takawa har saida ya isa gaban helicopter dake tsaye yana jiransu, yana k'arasawa matuk'in ya fito yana tambayarsa lafiya? Dan ya d'auka ko ta samu rauni ne, da hannu ya masa alamar ya tashi jirgin kawai, yana zuwa jefata yayi ciki shi ma ya shiga ya zauna.

Jingina yayi a kujerar ya lumshe ido, a sanyaye ya shiga sauke numfashi wani bayan wani, saida suka daidaita a sama sun fara nisa ya bud'e idonshi, d'an juyawa yayi ya kalleta jin shiru, gabanshi ne ya fad'i sakamakon had'a idon da sukayi, ta masa k'uri da ido ta fito da 'yan hak'oranta kawai tana kallonshi.

D'auke kan shi yayi a kan ta ya d'ora hannunshi kan cikinshi, a hankali ya fara b'alle mab'allen rigarshi saida ya ciresu tas, singlet d' in shi kuma jini ne ya fara b'ata ta sakamakon faratun zakin nan da suka tab'a shi.

Tana ganin haka ta sake zaro ido tace "Wayyo Allah, jini kake zubarwa."

A tsawace yace "Shiru dallah."

Gum ta ja bakinta ba ta sake cewa uffan ba, amma kuma idonta akan shi suke, duk wani motsinshi biye take da shi, yana k'ok'arin cire rigarshi ta kakin shi suka sake had'a ido, cike da takaici yace "Wai malama mi ye na k'ura min ido? Ki kalli gabanki mana."

Ba tare data d'auke idonta a kan shi ba tace "Tambayoyi gareni, ina tunanin ko ba zaka iya amsa min su bane."

A hassale yace "To kuma da kika san haka me yasa zaki zuba min wannan idanun na ki masu kama da *dutsen lu'u lu'u*."

Wata kyakyawar dariya tayi tare da cire hular kan ta gajeran gashinta daya fara tsirowa ya bayyana tace "Da gaske?"

Girgiza mata kai yayi ya k'arasa cire rigarshi, zaro ido tayi tana kallon k'wanjinshi, da gayya ya sake juyawa ya kalleta, cike da gatsali yace "Daina kallo na, ko na birgeki ne?"

Da sauri ta kau da kan ta tace "God forbid, me zan ci da kai ni kuma?"

Kallonta yayi galala yace "Amma wace gulma ta kai ki d'akina daren jiya?"

K'yak'yabta ido tayi tace "Kawai na je tantancewa ne."

K'ala bai ce mata ba sai ma mayar da rigarsa da yayi, haka har saida suka sauka inda suka rabu da sauran d'aliban, tuni sun samesu a wurin duk suna jiransu, tuni su Deeyam suka kewayeta suna tambayar ta ko ta ga zaki ? Da farin ciki ta shiga labarta musu har suka shiga mota dan komawa su ma suna fad'a masa abinda ya faru ta b'angarensu.

*Tankara*

A sauk'ak'e Haman yayi nasarar samun gidan Ruman, bayan sun gaisa kuma ya fad'a mata shi jami'i ne, cikin rashin fahimta da tsoro tace "To amma yallab'ai me kake nema daga gareni? Me na yi?"
Chapter 16 · 0% Book details