← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 86

Sashe 70

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka shi ma Wudar shirin ya gama tsaf ya ce ai tare zasu tafi, duk da ya yi tambayar har ya gaji cewa ta fad'a masa ina za ta je, sai kawai ta ce wajen d'anta Umad, yin me? Yana ina? Duk ta k'i amsa mi shi, hakan yasa yanzu dai kafin ta baro gidan ta baro hadimai na ta loda kayayyaki a moto wanda duk mai hankali ya gani zaka san neman aure ne za'a je yi, sai dai na wa? Kuma a ina? Bata sani ba, cikin wannan hada hadar ta kutso kai ta badd'a kama ta fita abinta.

Akan babban titin dake bayan filin jirgi motoci na police guda biyu suka tari gabansu, dole ta sa dreban tsayawa da tunanin laifin me ya yi kuma? Wace dokar ya taka ne haka mai girma a cikin tuk'i? Jami'ai hud'u ne suka fito daga motocin, sai jami'a mace d'aya data fito, cike da izza Umad ya fita ya bjd'e murfin da Joy ke zaune tana kallon me ke faruwa, amma sam hankalinta bai tashi na saboda bata ga abinda tayi ba.

Suna k'arasowa dukansu suka sara masa da girmamawa, da mamaki Joy ta kalli jami'an sannan ta kalli Umad da tunanin wa ye shi kuma a gwamnatance, hannunta Umad ya kamo sanda jami'ar ta k'araso ya karb'i ankwan hannunta, ba zato ba tammani ya mata awarwaro da ankwar nan a hannayenta, mamaki ne ya hanata katab'us sai kallonshi tana fad'in "Kai Umad, lafiya? Me na yi kuma? Me ye haka wai? Ka manta ko ni wacece?"

K'ala bai ce mata ba sai jan hannayenta da yayi saida ya sadata da motocin jami'ai ya dannata baya ta zauna sannan ya mayar ya rufe, gilashi ya ciro bak'i daga aljihunshi ya manna a idonshi, juyawa yayi zai shiga mazaunin mai zaman banza ya ji tana jijjiga tana fad'in "Kaiiiii! Umad, ka kunce min abar nan, me na maka ne wai?"

Shiga motar yayi ya ja wata raga dake tsakanin kujerar baya da kujerun gaba saboda baya da buk'atar hayaniyarta, saidai yana jin yanda take ta bubbuga motar tana hargagi, bai kulata ba saidai yana kallon wani jami'i da ya d'auko jakar Joy d'in a bayan taxin nan sannan ya biya mai taxin suka taho, tayar da motocin suka yi har da jiniya irin ta yan sanda sannan suka nufi babbar headquarter jami'an bincike na k'asa.

D'akin bincike suka ajiye ta, kalle kalle ta shiga yi tana ta jujjuyawa, d'akin studio ce ta musamman, dan iya maganarka kawai zaka ji sai wanda ke kusanka, amma ko iska bata shigowa daga waje bare ta fita, lullub'e yake da bak'in yadi mai kaurin gaske, sai wata faffad'ar taga wacce ita daga ciki kanta take gani ma'ana madubi, saidai daga waje jami'ai ne na musamman da na'urori a gabansu, inda daga nan suke iya sauraren duk abinda ke faruwa ko zai faru a ciki.

Kujera biyu ce wacce take zaune a kai sai wacce ke fuskantarta, inda k'akk'arfan teburin dakz gabanta aka d'aure hannayenta da ankwa mai d'an tsayi wacce ta fi wacce aka saka mata da farko.

Cikin hargagi ta fizgi hannayenta tana kwaroroton fad'in "Wai babu kowa a nan ne? Me na yi ne? Akan wane dalili zaku kawo ni nan ku a je? Ina buk'atar ku kira min lauyana."

Shirun da yayi yawa babu mai kulata ne yasa ta sake fizgar hannayenta har saida kujerar da take zaune ta motsa tare da fad'in "Banzaye kawai, sai kun yi nadamar ajiye ni a nan da ku ka y...."

Cak maganarta ta tsaya saboda k'ofar da aka bud'e aka shigo, Umad ne fuska kici kicin saidai akan bak'ak'en kayanshi ya d'ora wata bak'ar jacket mai d'an ratsin fari sai daga baya an rubuta Police da manyan harufa.

A gadarance ya k'arasa ya ja kujerar sannan ya ciro k'aramar bindiga daga k'ugunshi ya ajiye, zaune yayi ya rumgume hannaye ya jingina a kujera yana zuba mata idonshi da ba wani girma ne da su ba sai tarin kwarjini kamar na damisa, murya a dak'ile kamar saukan aradu yace "Magana ce za mu yi ba wasa ba, kuma duk abinda zai fito daga bakinki ya zama gaskiya, idan ba haka ba zan manta da wacece ke a gare ni na d'auki tsatsauran mataki a kan ki."

D'ora hannayenshi yayi a kan teburin ya d'ag girarshi ta hagu sama yace "Kin fahimta?"

A hassale tace "Kai wane irin d'a ne? Ni fa k'anwar mahaifiyarka ce, Umad me na yi da za ka kawo ni nan?"

Had'e yawu yayi tare da sake tsura mata ido yace "Khatar ya fad'a mana kina da alak'a da harin da aka kai masarautar Egypt shekarun da suka wuce, me zaki ce a kai?"

Zazzaro ido tayi na mamakin ya kuma wannan maganar ta fito? Khatar? Ya aka yi Umad kuma ya san shi? Duburburcewa tayi ta kalleshi tace "Ka ga Umad ba zan yi magana ba, ina son ganin lauya na sannan."

Wani jan kallo ya mata da yasa ta sadda kanta k'asa cikin dakakkiyar murya yace "Tunda kika ga na zo da ke nan kai tsaye, kuma na d'auko miki gundarin zancen a take, ke kinsan ba wasa ba ce ta kawoni, Joyran..."

Ya kira sunanta ya nunata da yatsa kafin yace "Ki bani amsar tambayata kafin na turo jami'ar da za ta bincika min ke yanda ya kamata."

D'aga hannayenta tayi dake d'aure tace "Shikenan na ji, zan fad'a ma ka Umad, amma..."

Marairaicewa tayi tace "Kar ka bari kowa ya ji maganar nan Umad, ka ji?"

Jajayen idonshi kawai ya zuba mata yana kallo, cikin shashek'ar kuka na munafurci ta fara fad'in "Tabbas da taimako na a cikin kai harin nan, sai dai ba da makami ba ko wata hanya ta daban, mun kasance muna soyayya ni da Khatar tun a makaranta, sanda yaya Kossam ke d'aukar nauyin karatuna da duk wasu buk'atuna, sai na fara jin kishi a kan ta ina jin haushin me yasa ba ni ba ce a matsayinta? Wata rana na zo hutu Giobarh sai mahaifinka ya umarci da mu shirya za'a yi taro a k'asar Egypt, mun tafi cikin farin ciki tare da ku da kuma yaya Kossam, a Egypt sai muka had'u da Khatar shi ma ya aje a lokacin ba'a masa wazirin sarkin Khazira ba, duk sanda k'afa ta d'auke ni da shi muna tare muna soyayyarmu, a nan ne har na samu damar fad'a masa abinda na ke ji a zuciyata game da yar uwata, tambayar da ya min ita ce *"Me ki ke so a yi kenan?"*

"Sai na fad'a masa ina so na zama sarauniyar Giobarh, na zama mai fad'a a ji a masarautar, da fari ya nuna min kishinsa saboda mun yi alk'awarin aure da shi, amma washe gari sai ya zo min da maganar wai zai cika min buri na, da na matsa masa me zai yi ne sai ya ce min *"Sarki Musail ne ya nuna sha'awarsa ga 'yar sarkin Egypt, saidai ita ta nuna bata son shi d'an yar uwarki (Urab) take so, kuma sarki Musail ya bani wuk'a da nama na yi duk abinda ya dace dan ganin ya sameta, dan haka zan jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya."*

" Na tambayeshi ban gane me ya ke nufi ba, sai ya ce min *"Yau da dare zan sa a kashe min d'an yar uwarki, hakan zai sa sarkina ya samu Juman, daga baya zamu bar duk shaidar da zata nuna sarki Musail ne yasa a yi wannan aika aika, kinga kenan mun haddasa gaba mai tsanani tsakanin masarautar Giobarh da masarautar Khazira, hakan zai sa sarki Wudar ya nemi d'aukar fansa ko ta ya ya, idan aka yi nasarar cin Giobarh da yak'i, a k'arshe za'a kafa sabuwar daula a Giobarh kuma ke zaki zama sarauniyarta, idan kuma aka yi nasara akan Khazira..."*

"Da sauri na tambayeshi to me zai faru? Sai ya ce *" Zan zama sarkin Khazira, ke kuma sarauniyar gaba d'aya Bussam, ya kika gani ?*"

" Na ji dad'i sosai har cikin zuciyata, hakan yasa na yi dogon tunani a lokacin sannan na bashi ta wa shawarar na ce *"Madadin ka sa a kashe Umad shi kad'ai, me zai hana ku d'auki hayar mahara da dama su kawo hari aasarautar nan yau cikin dare?*"

"Tambaya ta ya yie ye anfanin yin haka? Sai na ce masa *" Idan fa aka yi rashin sa'a aka kama wad'anda kuka turo, to shakka babu zaka kwana a ciki, dan gidan nan yanzu baibaye yake da hadimai da dogarai saboda yawan safakunan dake ciki, amma idan mutanen dayawa kuma kan mai uwa dawabi aka yi, to kai tsaye ba za'a zargi wani sarki ba, dukansu zasu dinga wa juna kallon kallo ne, a cikin hatsaniyar kuma sai a kashe Urab, ni kuma nasan mutuwar Urab daidai take da mutuwar Kossam, dan tana matuk'ar son yaron, kaga ni kuma ta wannan hanyar zan k'arasa kassara rayuwarta.*"

" Haka muka kwana da shirinmu, kuma mun yi nasarar aiwatar da abinda muka tsara, a hakane aka kashe Urab kisan wulak'anci, wanda sanadiyar haka mahaifiyarka ta yanki jiki ta fad'i, ba'a iya aiwatar da komai ba dan masarutu da dama sun rasa mutanensu a lokacin ko da kuwa hadimi ne, ni kuma daga lokacin sai..."

Fashewa tayi da kuka na gaske ta sunkuyar da kanta, wani wawan buga teburin yayi da yasa ta zabura kamar zata tashi tsaye, wanda hakan yasa fitsarin da take ji ya banko a guje ya taho mata daga zaunen da take, kwararararan da ya ji abu na zuba a k'asa yasa ya d'an yi jim yana saurarawa, a hankali ya tura kujerar da yake zaune baya sannan ya d'an lek'a, da sauri ya kalleta ya girgiza kai yace "Ina jinki."

Yamutsa fuska tayi ta matse k'afafunta kanta k'asa saida ta gama tsiyaye fitsarin tas sannan ta d'ago a hankali ta kalleshi, a kausashe ya kuma fad'in "Ina saurarenki."
Chapter 70 · 0% Book details