Sashe 12
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse yace" Ruman, k'auyen *Tankara*." (Mai Dambu ta mu ina godiya da wannan kyautar, Allah bar zumunci)
Hannu ya mik'a masa cike da jin dad'i yace "Nagode sosai,na ji dad'in had'uwa da kai."
Jinjina kai yayi shi ma yace "Ni ma haka, fatan nasara."
Murmushi yayi sannan suka saki hannun juna ya fita a lambun gaba d'aya, a hanyarshi ta zuwa k'auyen Tankara ya kira lambar Umad, dan yayi niyya yau zuwa gobe sai ya samo bakin zaren nan, dan sun jima suna doguwar tafiya saboda yarinyar nan, abinda ya fi basu wahala kuwa shi ne kafin su samu wanda zai iya basu bayanai a kan ta, da k'yar suka samu wata baiwa da sarki Musail ya ma ciki, amma saiya koreta saboda a lokacin yana cikin tashin hankalin neman Zafeera, ita kuma haushin yanda ya koreta bai sakata a layin k'wark'wararsa ba ma bare ta zama matarsa yasa ta fad'a musu bafaden da taji suna wani yare da su Habbee.
*Umad* na tsaka da jinjina k'arfin halin Ayam na marin da ta wa Zafreen ya ji k'arar wayarsa, da sauri ya d'aga ya d'ora a kunne amma bai ce komai ba, Haman da yasan komai ne ya fara fad'in "Kana ji?"
"Umm." Ya fad'a a k'asan mak'oshi, d'orawa da "Na samu mutumin nan Umad, ya ban adreshin d'aya mutumin kuma na sameshi."
A zabure ya tashi tsaye yace "To ya kukayi? Me ya ce?"
A tsanake yace "Ya fad'a min komai, yanzu haka zan je k'auyen Tankara ne."
Da mamaki Umad yace "Tankara kuma?"
"E." Ya fad'a kai tsaye, da alamar tambaya yace "To amma me yasa?"
Kamar yan1 gabanshi ya shiga girgiza kai yana fad'in "Umad lamarin nan fa ya wuce yanda kake tunaninshi, wai ma kasan da sarauniya Juman ita ce ta sa aka d'auke yarinyar dan ta kub'utar da ita?"
Da mad'aukakin mamaki Umad ya shiga zagayen d'akin hannunshi akan k'ugunshi yace "Idan na fahimceka sarauniya Juman ita ta umarci jakadiyarta Habbee da mijinta da su gudu da yarinyar, haka kake nufi?"
Jinjina kai yayi yace "Tabbas kuwa hakane."
Wani shak'iyin murmushi Umad yayi sannan yace "Hummm! Sannu sannu dai, komai ya kusa fitowa fili."
Zura hannunshi yayi aljihu yana takawa a hankali yace "Shikenan Haman, ka ci gaba da bincika mana komai a tsanake, Allah ya kiyaye ka."
Murmushi yayi yace "Nagode, sai na kiraka." Lumshe matsakaitan idonshi yayi alamar to kamar suna kallon juna.
*Khazira*
Hankali tashe babban malamin ya iso fada, sai ga sarki Musail na ta kewayar d'akin ya cire babbar rigarshi ya aje sai zufa yake, cikin tsawa da hargagi ya kalli malamin yace "Babban malami ta ci amanata, Juman ta ha'ince ni, shin soyayyar dana nuna mata ce ta gagara? Ko kuma butulci ne irin na mace?"
Jim ya d'anyi kamar zai ba wani damar fad'an wani abu, sai kuma yay saurin fad'in "Yanzu me ye abun yi baban malami? Ya zanyi na samota ta dawo gareni? Ina so na kamata da hannaye na, Dhurani bana so na mutu yanzu."
Ya k'arashe maganar yana d'aga murya, cikin rarraba ido Dhurani yace "Sarki na, wannan ai abu ne mai sauk'i, mu takura gimbiyar mu har sai ta fad'a mana."
Khatar ne yayi saurin fad'in "Da zata fad'a ai da ta fad'a, shekaru ashrin fa muka d'auka muna bilinbituwar nemanta, a gaban idonta muke yi da me ta tab'a taimaka mana?"
Sarkin yak'i Adah ne ya d'an jinjina kai duk da ba'a buk'ace shi ba yace "Gaskiya ne, amma ko bata fad'a da bakinta ba mu zamu nemota."
Kallonshi sarki Musail yayi yace "Adah bana son wasa, wane irin nema ne baku mata ba ? Tun kana da k'ruciya kake yawon nemanta, sai yanzu ne zaka ganta?"
Sunkuyar da kai yayi yace "Sarki na, sa'ilin da zamu kai sarauniya kurkukun sabah sun yi wani yare ita da d'aya daga cikin bayinka, bana tamtama cewa maganar da sukayi ta shafi gimbiya Zafeera."
Da saurin bala'i sarki Musail ya tunkareshi yace "Wanene shi? Me suka tattauna?"
Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba ya shugabana, dan kafin ta masa magana saida ta canza harshe."
A bala'in tsawace yace "Waye shi a gidan nan, je ka kawo min shi nan."
Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya juya cikin takon k'arfi yaf fita a falon, bai d'auki lokaci ba ya dawo waccen bafaden na bayanshi, gefe sarki yak'i Adah ya tsaya shi kuma ya zube har k'asa yana gaishesu, saidai a zahirinshi da bad'ini hankalinsa a tashe yake, ba ka da abun zargi ma ka ji tsoron amsa kiran sarki Musail bare kuma shi da yake ji a jikinshi asirinsa ne ya tonu.
Cikin daka tsawa sarkin yak'i Adah yace "Kai k'ask'antaccen bawa, sarki yana so ya ji abinda kuka tattauna tsakaninka da sarauniya Juman?"
D'aga kai yayi ya kali sarkin yak'i jikinshi na makyarkyata, kame-kame ya fara ya rasa me zai ce da shi, a sukwane sarki Musail yayi kan shi, kafin ka ce me ya saka k'afa ya hankad'ashi ya fadi kwance, kafin ya tashi yasa k'afar ya take masa k'irji, cikin k'araji yana zazzaro ido yace "Zaka fad'a min ko sai na kasheka a banza? Ka sani duk wanda yace zai shiga tsakani na da cikar burina kamar wanda zai taimakawa mak'iyana kyautar takobi ne dan yak'ata, dan haka ba zan bar shi a raye ba, yanzu fad'a min me ta fad'a maka?"
Cikin tashin hankali da tsananin tsoro yace" Sarki na, shugaba na ka min rai karka kasheni, ta ce ko ta halin yaya na isar da sak'onta, na fad'a mata ta ninka saka ido akan gimbiya."
A tsawace ya sake fad'in" Wacece? Kuma a ina take?"
Cikin rawar jiki yace" Wata tsohuwa ce, a k'auyen Tankara."
"Me sunanta?" Dhurani ya tambaya daga gefenshi, cikin rawar leb'e yace "Ruman, Ruman ne."
K'atuwar takobin dake k'ugun sarkin yak'i Adah ya jawo, kafin kowa ya ankara kawai ya sokawa bafaden nan ita a tsakiyar ak'ogwaronsa ta hudashi zuwa wuya, wani huci ya shiga saukewa ya mik'awa Adah wuk'ar yana fad'in "Duk wanda ya yi k'ok'arin hanani kasheta to shi ma kasheshi zan yi, sarkin yak'i."
Da sauri Adah ya amsa yana rusunawa, juya baya yayi yace "Ka d'ebi wasu daga cikin mayak'anka ku nufi Tankara, idan tana nan ku taho da ita, idan kuma hakan ya gagara ku sanar da ni, ni zan je har inda take sannan na kasheta da hannu na."
Amsawa yayi da "Angama Ranka shi dad'e." Kafin ya kama hannayen gawar nan ya jashi k'iiiii har ya fice da shi a falon.
*Larhjadin*
Ba wani yammaci bane sosai, amma dake makarantar akwai wadatar shuke shuke sai tayi luf sai iska mai sanyi dake kad'awa, duka d'aliban mata suna tsatsaye bakin mota inda dreban ke jiransu, suna cikin shiga ta kakin ma'aikatan gandun daji, riga da wando kalar shud'i da babu kwalliya, saidai daga yanayin d'inkin da wasu ado da akayi ga rigar zai shaida maka masu tsaron k'asarsu ne, bak'ak'en huluna ne a kan su sun daidaita musu zama cikin k'warewa, ga kuma takalminsu bak'ak'e k'afa ciki sai k'yalli suke sun d'auresu tamau da d'amara.
Gyara tsayuwarta tayi tana murgud'a baki tace "Wai malamin nan bai san lokutan karatu dana hutu bane? Ya zai shanya mu a nan?"
Sergent d'in colonel ne ya tsaya gabansu cikin d'aga murya yace "Ayam Utais, yallab'ai canal (colonel) na san ganinki yanzu a ofishinshi."
Waina idonta tayi ta kalli Deeyam da ita ma ke kallonta tace "Wai ni sai yaushe ne canal d'in nan zai barni na huta?"
Murmushi Deeyam tayi tana rik'e d'amarar k'ugunta a hannu tace "Ranar da ke ma kika barshi ya huta, ba ke kullum 'yar masifa ba ce."
Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad'i sannan ta nufi hanyar tafiya tana fad'in "Sai na je kuma yayi ta sadda kai k'asa kamar ya ga gyatumarshi."
Yanda aka mata d'inkin daidai da zubin hallitarta yasa kayan suka karb'eta da kyau, duk da bata da wasu mazaunai na a zo a gani, amma dake ta d'aure da zanzaro sai hakan ya basu damar juyawa.
Motocin data gani da suka amsa sunansu masu bala'in kyau da kuma shek'i yasa ta k'ura musu ido a ranta ta ayyana "Ko dai bak'i a ka yi?"
Suna kai wa bakin ofishin ya ja ya tsaya ya nuna matata shiga, kallon shi tayi t tab'e baki sannan ta kama hannun k'ofar ta murd'a, k'afa d'aya ta fara zurawa ta shiga a matuk'ar nutsuwa da kuma wani irin kwarjini da izza, tana k'arasa shiga kamar dai mutanen ciki ita ma sai ta zuba idonta tana k'are musu kallo.
Canal dake kujerarshi ya had'e hannaye wuri d'aya sai rarraba ido yake, amma tana shigowa ya mayar da hannayenshi k'asan teburin ya koma kallon takardun gabanshi kamar wanda ya ga aljana. Waziri Khatar kuma na kujerar dake fuskantar ta canal d'in fuskarshi a matuk'ar had'e yanda zta gigita mai kallonta, ga shigar da yayi ta alfarma ita kad'ai zata sa ka rusuna mishi ka d'auka sarkin ne da kanshi.
Sai Zafreen dake tsaye bayan wazirin ta rumgume hannayenta ta k'urawa Aya d'in ido. Sai kuma wanda zata iya cewa shi bata san me ya kawoshi nan ba, dan in wannan yana zaune ne saboda marin da ta wa Zafreen, to shi kuma fa? Yallab'ai Umad kenan, gashi dai cikin kakinshi a shirye tsaf, amma kuma ya barsu suna jiranshi har yanzu gashi za'a zo a nemi b'ata mata rai.
Yanda ta tsaya gaban tebur d'in yasa canal d'aga kai ya kalleta, suna had'a ido kawai sai ya ga kamar hararanshi ma take, da sauri ya mayar da kanshi ga d'aya daga cikin fadawa biyun da Khatar ya shigo da su yace "Rufe k'ofa."
A ladabce bafaden ya rufe k'ofar a lokacin ta juya ta kallesu sannan kuma tasan da zamansu, maida kallonta tayi ga canal d'in tace "Yallab'ai ka ce kana son gani na."
D'aga kai yayi ya kalli fuskarta, amma abinda Umad dake zaune yana tsare kowa da ido ya lura da shi shine yanda yake ta yawo da idon na shi ya kasa tsayar dasu a kan fuskarta bare ya kalli idonta, hakan yasa shi dasa alamar tambaya aka wannan lamari.