← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 86

Sashe 83

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaman dirshen yayi saboda kxantar da kanta tayi kan damtsenshi tana ci gaba da tsutsa ka rantse loli pop ce take tsutsa, da wani k'arfi k'arfi ya jawo hannunta d'aya ya d'ora kan kuncinshi yan shafawa, a hankali a hankali wasar dake tsakaninsu ta canza zuwa wani salo na daban, rana ta biyu kenan a garesu, had'uwarsu ta biyu kenan a rayuwa, hakan ya k'ara jigatasu musamman Ayam da tunda ta fahimci wani irin girma da mijinta ke d'auke da shi ta tsorata ta kuma zabura zata mik'e, amma haka ya danneta da hannu d'aya har saida yayi nasarar ida nufinshi a kan ta.

Sai ga Ayam mai kukan yunwa ta koma na wahala, dan abun ne ya mata yawa, ga rashin k'oshi ga kuma azabar daya gana mata, amma haka ta daure ta k'i nunawa a fuska sai dai ta yamutsa fuska kawai, har saida ya sa aka kawo masa abinci mai rai da lafiya ya kawo mata har d'akin baccinshi kan gado, da hannunshi ya dinga bata tana amsa a kunyace, shi kuma ya k'ura mata ido yana kallo k'aunarta na sake huda zuciyarshi, shi kad'ai yasa me yake ji akan baiwar Allahr nan, shi kad'ai yasan irin abun da yake ji idan yana tarawa da ita, shi kad'ai yasan irin gamsuwar da yake samu a tare da ita, idan har zai iya bud'a bakinshi yayi magana sai yace " *Lallai abinda aka gani a hasashe kenan, shiyasa maza suke haukacewa a kan ta, watak'ila irin albarkar dake tattare a jikinta kenan, shiyasa kowa ke son ta zama tashi, sai kuma Allah ya wanke ya bani.*"

Ta so yin bacci da ta k'oshi amma ya hanata saboda yamma tayi sosai, dole ta hak'ura ta zauna a b'angaren na shi shi kuma yana tare da ita, duk masu son ganinshi dole suka hak'ura saboda da an fana musu yana tare da sarauniya dole ka yi shiru.

Sai bayan magriba kad'ai ta samu damar ganawa da Utais, tayi kukan rabuwa da sukayi kai tsaye, sannan ta nuna bata jin dad'in duk'a matan nan da suke, haka kuma ta k'uduri niyya a ranta zata nemi sarki alfarmar ya ware musu gidansu na daban ba kusa da ita ba, dan bata so tana ganinsu suna sunkuya mata, dan ita a uwayenta take kallonsu, su kuma har yanzu girmamata suke ba kuma zasu daina ba.

*Rayuwa* kenan, sai gashi komai na tafiya daidai, duk da anyi rashi amma dake hukuncin ubangiji ne manta abinda ya wuce, sai suma basu yarda mutuwar iyayensu ta hanasu rayuwa ba, Umad na tafiyar da mulkinsa yanda ya dace, da taimakon dattawan zaurenshi da kuma fasihar matarshi, wacce a zahirin gaskiya baiwarta ke dad'a fitowa fili a yanzun ana gani, indai har zata bashi shawarar yayi kaza, to In Shaa Allah za'a ga da kyau ko da wajen yanke hukunci ne a tsakanin talakawan gari.

Sannu sannu sai wani abun mamaki ya dinga bayyana, inda sunan Umad da masarautarshi ke bunk'asa a dalilinta, sai mulkinshi ya fara zama na al'ajabi da d'aukar misali ga sauran masu mulki da sarakuna, ta ko ina maganarsa ake ana bayar da misali da shi, hatta da harkar kasuwanci da Ayam ta bayar da shawara aka kuma rairaye matasa aka sama musu sana'oni, sai gashi Giobarh tafara karb'ar bak'in mutane suna zuwa ci rani a garin.

*Bayan wata bakwai*

Kallon shugaban yan kasuwan yake yana bayaninshi a tsanake da ladabi, saida ya kai aya kafin ya numfasa ya d'an muskuta, buk'atar da ya zo da ita yana son neman shawara dan yasan matakin da zai d'auka, saidai babban mai bashi shawarar ya barota ta koma bacci saboda sammakon da tayi ta je asibitin cikin gidan ta yi awo, idan ya tasheta yanzu rigima ce ta bugawa a jarida zata saka mishi, idan kuma ya yanke hukunci ba zai samu nutsuwa ba, dan shi kanshi yanzu yake yarda da abinda aka canfa a kanta, har wani lokacin ya kan takura zuciyarshi ta k'aryata abinda ake fad'a d'in, dan a matsayin shi na sarki baya so a ce ya yarda da irin wannan abun ta yanda zai kawo masa cikas a tafiyar mulkinsa, hakan zai sa wata rana ya ji lallai lallai sai da ita ne zai ciyar da mulkinsa gaba, kamar dai yanda mahaifinshi da Bukhatir suka canfa, amma da ya tuntub'i malaminshi sai ya nuna masa ba komai, indai har shawarar ta ta mai kyau ce kuma tana kawo ci gaba, saidai kar ya zama kullum zai shawarce ta kan lamuran mulki saboda wasu dalilai, dan haka yanzun ba kullum yake tuntub'arta kan abu ba.

Hohoho! Ina masoya kuma makaranta litattafan hausa novel? Yau ma ga jarumar ta ku ta dawo a cikin sabon littafin ta mai taken *MALLAKINA CE*, *MALLAKINA CE* littafine da ya k'unshi wata irin cakwakiyar soyayya, sark'ak'iya da kuma ban al'ajabi gami da barkwanci, zai fad'akar ya nishad'antar da masu karatu, albarkacin sabuwar shekara da za'a shiga, littafin zai fara zuwa muku *15/01/22*, domin samun na ki da wuri ki/ka hanzarta biya dan karatu cikin salama, ka da ki bari a baki labari maza hanzar ta ki nemi naki akan farashi mai rahusa. Ga mutanenmu na Niger zaku biya katin dala dari Cfa zaku tura akan lamba kamar haka *94-98-56-52*,
ga mtanen mu na Nigeria kuma zaku tura Naira 300 ta wannan account d'in 0594148516 lubabatu shehu Gt bank, bayan kun tura sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar *94-98-56-52*
Mun gode sai kun zo.

*Alhamdulillah.*
01/01/2022 脿 11:47 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*Fin*

*Fin*

*Fin*

*50*

Kiran da ya shigo wayarsa wacce ba k'ara take ba saidai vibration yasa shi duba wayar, duk da jininshi har gudu ya k'ara saboda son ya kai hannu ya d'auki kiran, amma dake jikin har ya fara sabawa da tsaiko da jan aji irin na sarakai, sai ya zura hannu a hankali ya d'auki wayar, hakan ma wai dan daga shi sai shugaban yan kasuwan ne, da yana tare da babban amintaccen bafadansa ne da shi zai d'auko ya mik'o masa.

Danna ok yayi ya kara a kunne yyi shiru, a k'asan zuciyarshi ya tambayeta "Me ki ke so sarauniyata?"

A zahiri kuma sai yayi shiru saida ta furta "Sarkina."

Lumshe ido yayi sannan cikin nutsuwa ba tare da wanda ke kusanshi ya ji ba yace "Sarauniyata."

A shagwab'e ta furta "Ka dawo dan Allah, bana jin dad'i."

Tsai yayi da idonshi zuciyarshi na dokawa da k'arfi yace "Me kike ji? Cikin ne?"

Kamar za ta yi kuka tace "Bayana ke ciwo, ji nake kamar zai rabe biyu."

Kallon shugaban yan kasuwan yayi ya taso daga cikin kujerar yana shirin mik'ewa yace "Ka gafarce ni, iyalina ce ba lafiya."

Bai jira amsarshi ba kawai ya fice a falon na shi na karb'ar bak'i hannunshi rik'e da wayar bai kashe ba, ta k'ofar sirri da shi kad'ai ke bi ta nan ya shiga wanda yana bud'e k'ofar ta sadashi da k'aramin falonta, da sauri ya ratsa ta tsakiyar kujerun alfarmar dake zube ya bud'e wata k'ofar, turus ya tsaya sai kuma ya tafi a sukwane gareta yana jefar da wayar hannunshi.

Juyowa Ayam tayi ta kalleshi wacce ta sauko daga kan gado tana matse fuska, b'ata rai tayi tana mai rashin jin dad'in ganinshi saboda abinda ta ji a jikinta, ita dai tana baccinta kawai ta ji wani lema mai d'umi na fitowa a k'asanta, tana tashi zaune ta ji abun na dad'a k'aruwa, a k'ank'anin lokaci sai ga ta tayi jagaf a cikin wannan abu da ita take ganin fitsari ne.

Zagayowa yayi inda take ya rik'eta yana k'are mata kallo ganin sai tattare doguwar rigarta take marar nauyi, kallonshi tayi a marairaice tace "Sorry...na kasa rik'e kai na, tahowa kawai ya..."

Wani zul ta sake ji ruwan nan sun b'allo mata, hakan ya sa ta ja baki tayi gum ta damk'i hannunshi, k'asan data kalla shi ma ya bi da kallo, ganin ba zata iya da abun kunyar nan ba yasa ta durk'ushe tace "Dan Allah ka kira min Mah, ka ce ta zo da sauri wallahi fitowa yake."

Zaro ido yayi yace "Yaron? Yaron ne ke fitowa ? Amma fa wata bakwai ne."

Yarfa hannunta tayi tace "Ni ban sani ba, kawai ka kira min Mah ni dai."

"To to." Ya fad'a yana laluba wayarshi, dan tazara ce mai tsayi tsakaninsu da Mah d'in, hango wayar da yayi a k'asa ya hanzarta d'auka ya saka lambar Mah d'in ya kirata.

Ko da Kossam ta zo saida kunya ta kamata, dan matsayinta na babba wacce ta yi haihuwar nan ta san ko menene, hakan na nufin haihuwa ta matso saidai ba lallai yanzu yanzu ba, hakan yasa ta umarceta ta shiga ta gyara jikinta, saidai kafin ta fito daga ban d'aki har ta sake b'acewa, hakan yasa ta ma kanta dubara wajen yin k'unzugun data tabbatar zai tare mata wannan ruwan, ko da ta saka kaya sai ta ji tsaf yanzu, yana zuba saidai baya b'ata mata jiki, tana fitowa ta samu Umad ne a tsaye amma Kossam bata nan, rumgumota yayi jikinshi yace "Kin d'aga min hankali sarauniya ta, na d'auka zaki haifa min yaro bakwaini ne."

Cikin fara'a tace "To ai hakan na nufin zan haifi bakwaini ne."

Murmushi ya sakar mata yace "Ba zaki yarda ba kema, e yasa to?"

Kallonshi tayi tace "Saboda ni ce ke yi."

Dariya yayi yace "Allah baki hak'uri Hajiata, tunda magana ce aka fad'a min."

Tureshi tayi kad'an a jikinta tace "Ni dai ka tafi ka bani wuri."

"Korata ki ke?" Ya fad'a yana k'ura mata ido, girgiza kai tayi tace "A'a, bana dai jin dad'in yanayi na kawai."

Rumgume ta yayi sosai yace "Ni wannan bai dameni ba, ke kawai nake so Ayam, ke kawai."

Cikin harshen Italy tace "To ai ni bana jin dad'i, salon ka min kishiya kuma ka fad'a mata ni k'azama ce ko?"

Yar dariya yayi yace "Dan Allah kar ki fara hassala ki fara canza min yare."

A harshen Gallois tace "To idan baka so ka tafiyarka."

Raba jikinshi da na ta yayi yace "Idan na k'i fa?"
Chapter 83 · 0% Book details