Sashe 48
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jim tayi alamar tunani sai kuma ta jinjina kai tace" Lallai biri yayi kama da mutum, hakan na iya faruwa."
Da mamaki Juman tace "Amma kum..."
Bata gama fad'a ba aka bud'e k'ofar aka shigo, Juman na jin haka ta tabbatar da sarki ne, Ayam kuma juyawa tayi da sauri, tana ganinshi ta shiga k'ok'arin sauka daga kan gadon, da fara'a ya k'araso yana fad'in "Kaga 'ya da uwarta, ana tattaunawa?"
Murmushi Ayam tayi a ladabce ta juya ta kalli Juman data had'e fuska tace "Mah zan fita, sai anjima."
Da kai ta amsa mata alamar to, sannan ta mayar da dubanta k'asa tana sake cije fuska.
Saida ya ga fitar Ayam ya haura kan gado tare da fizgo gashin Juman cikin b'acin rai yace "Me kuke tattaunawa da ita haka tsawon awa d'aya? Gulma ki ke koya mata? Ko wani abu ki ke fad'a ma ta game da ni dan ta bijire min?"
Cike da bushewar zuciya ta fizge gashinta tana fad'in "E d'in, sai me? Tsoro ka ke ji ne kar ta san wani abu a kan ka?"
Hab'arta ya rik'o ya matse yace "Ki saurare ni da kyau, ko ki fad'a ma ta ko kar ki fad'a dai mutuwa za ta yi, dan haka ki shirya ganin gawarta gabanki."
Murmushin mugunta tayi tace "Ka jaraba ka gani mana, me ye na fad'a min idan ka yarda za ka iya kasheta d'in, ka je ka jaraba ka gani."
Jinjina kai ya yi yace "Shikenan za ki gani."
Ita ma jinjina kai tayi tace "Za ka gani mana in shaa Allah."
Sakinta ya yi ya sauka daga kan gadon ya juya zai fita sai kuma ya tsaya cak ya juyo yace "In shaa Allah? Ki sani na hane ki da yin duk wani abu daya danganci addininki, daga yanzu kuma bana so na sake ji."
Da sauri ta sauko daga kan gadon tace "Saboda me? Ka fara jiyo k'amshin sub'utar mulkinka daga hannunka ne?"
Bushewa tayi da dariya tace "To ka ji wani abu da ba ka sani ba, ita kan ta wannan addinin take bautawa, kuma ina mai tabbatar ma ka lokaci kad'an ya rage ka fara ganin sahu sahun masallata a farfajiyar gidan ka."
D'aga murya ya yi yace "Ba zai yiwu ba, sam haka ba za ta faru ba Juman, idan kuma haka ta faru sai dai in bayan ba rai na."
A hankali ta d'auke kan ta ta furta "Ai dama haka aka fad'a ma ka, komai zai faru ne bayan ba ranka d'in."
Da azama ya yi kan ta yana d'ga sandarshi da niyyar maketa, sai kuma wata zuciya ta horeshi tare da tuna mi shi Ayam, da k'arfi ya sauke hannunshi ya juya ya bud'e k'ofar da k'arfi ya fita kamar zai tashi sama.
Tana ganin fitar shi ita ma tab'e baki tayi ta gyara zaman mayafinta da kyau sannan ta fita, jakadiyar ta da hadima d'aya za su rakata tace "Ku barshi kawai, wajen 'yata zan tafi."
A ladabce suka amsa ma ta ita kuma ta wuce, dake ta san b'angaren sai gashi ta iso a sauk'ak'e, zaune ta samu Ayam kamar mai lissafin kud'i sai nuni take da hannaye, zaune tayi tana murmushi tace "Me ki ke yi haka?"
Murmushi tayi ita ma tace "Ba komai Mah, sannu da zuwa."
Numfashi ta sauke kafin tace "Yawwa sannu."
A tsanake ta kalleta tace "Yawwa Mah! Ina so ki d'ora min karatun nan daga inda kakata ta tsaya min."
Jim tayi tana kallon fuskarta tace "Ayam, ya ki ka ga iyaye na? Suna cikin k'oshin lafiya?"
Cike da tabbaci tace "Mah suna cikin k'oshin lafiya, saidai na tabbata suna kewarki, zai fi kyau ki ware rana ki had'u da su ko da sau d'aya ne kafin waninku ya bar duniya."
Jinjina kai tayi tace "Zan yi k'ok'arin haka In shaa Allah, ganinki ya haifar min da k'warin gwiwa."
Da fara'a tace "Ni kuma idan za ki tafi wajensu to zan tafi tare da ke."
Dariya tayi tace "To shikena', yanzu mu fara karatunmu ko, dan ya kamata ki san mahaliccinki da kuma yanda zaki bauta masa."
Daga haka suka shiga karatu ta dinga sanar da ita abinda ya kamata ta fara sani a farko.
*Giobarh*
Tunda suka had'u bai ce masa komai ba, yanda ya zuba masa ido tuni ya gigita tunaninshi yasa jikinshi kwasar b'ari da tunanin ya gama gano manufarshi, coffee da yasa aka kawo musu ya kasa kurb'ashi saboda baya da nutsuwa.
Ganin dai shirun ba zai fishesu ba yasa shi muskutawa yace "Umad ina saurarenka, me yake faruwa ne wai dan Allah?"
Ba tare daya daina binsa da kallon nan ba hannunshi tallabe da hab'arshi yace "Wani sabon aiki za mu shiga."
Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Haba Umad, yanzu abinda zaka fad'a kenan amma ka min shiru duk ka d'aga min hankali, ina jinka to me ye aikin?"
Gyara zamansa yayi ya d'auke hannunshi daga hab'ar ya sauke numfashi, cikin nutsuwa yasa hannu yana juya kofin dake d'auke da coffee yace "Na fad'a ma ka Ayam tana masarautar nan, kuma kafi kowa sanin had'arin hakan, shiyasa ni da kai zamu je fadar da nufin masu neman aurenta."
Da k'arfi ya zaro ido yana kallonshi yace "Me?"
Zuba masa ido yayi amma bai ce komai ba, Haman kam firfita ya fara yi da hannunshi saboda gumin da yake ji, sai ya ke ganin kawai yasa da shirinshi akan Ayam d'in, yasan niyyarshi shi ma ta son aureta dan ya samar da farin ciki ga yar uwarsa.
Umad kuma daya gama karantar yanayinsa kuma dama tun ranar da Ayam ta fad'i abin nan akan Haman d'in ya samu shakku a kan sa, daga ranar ya fara saka ido da bincike a kan shi, yanzu haka dai zai iya cewa Haman a tafin hannunshi ya ke tsaf, kallon duk wani motsinshi yake.
Gyara zama yayi ya d'an sassauta had'ewar da ya ma fuskarshi yace "Haman na gama shirya komai, kai zaka shiga gidan a zuwan d'an kwamishin kud'i, saboda na samu labari sarki Musail na son k'ulla wata hark'alla da shi, kafin su had'u mu za mu gabatar da kanmu a zuwan masu neman auren d'aya daga cikin 'ya'yansa."
Da mamaki Haman yace" Dakata Umad, idan har sarki Musail na son had'uwa da kwamishinan kud'i, me zai sa mu yi kasadar zuwa gidansa kuma? Asirinmu zai tonu kuma rayuka zasu b'ace."
Wani malalacin murmushi yayi yace" Tuni ai sarki mahaifina yayi magana da kwamishinan kud'in, ba matsala game da hakan tunda kai ne zaka je a matsayin d'ansa."
A kid'ime yace" Me yasa sai ni to?"
Kai tsaye yace" Saboda ni akwai abinda zai kaini gidan."
Murmushi Haman yayi yace" Idan na fahimta za ka shiga gidan nan ta hanyar d'ana tarko da ni, kana so ka samu damar yin abinda kake so a cikin gidan ta dalilin d'auke ma kowa hankali da sunan neman auren d'aya daga cikin yaranshi, hakane?"
Jinjina masa kai yayi yace" Hakane, dan haka ka shirya zuwa dare jirginmu zai sauka a Khazira."
Zaro ido yayi yace" Zuwa dare? Da wuri haka?"
Mik'ewa yayi ya d'auki wayoyinsu guda biyu babba da k'arama da makullin mota yana fad'in" Me za'a jira kuma? Ka shirya kawai."
Da kallo kawai Haman ya bishi har ya shige motarshi ya bar wajen parking d'in.
*Yana* isa gida kamar yanda ya saba b'angaren mahaifiyarshi ya fara nufa dan duba halin da take ciki, yana zuwa ya samu Joyran bakin k'ofar d'akin na ta tana ta rok'on masu gadin su barta ta shiga, tana ganin Umad ta gyara tsayuwarta ta shiga rera kukan k'arya tana fad'in "Yawwa d'an yar uwata, ka duba ka ga tsarin nan da aka yi, yar uwata data rage min a hanani ganinta, tunda yarinyar nan ta zo gidan nan ban sake saka yar uwata a ido ba, ka rok'esu su barni na shiga na ganta ko hankalina ya kwanta."
Saida ya d'auke kai daga gareta ya had'e fuska sosai muryarsa ba alamar wasa sannan" Doka ce, daga ni sai mahaifina zamu ganta, idan na fitar da ita shan iska zaki iya hangota daga nesa."
Yana gama fad'a mai tsaron ya bud'e k'ofa ya shige ya barta baki bud'e tana mamaki, dan kawai ta gama gane ta kare mata, sarki Wudae ya daina kulata, yanzu Umad d'in ma mai mata biyayya shia ya daina, duk a dalilin yarinyar nan? Juyawa tayi a fusace ta bar k'ofar d'akin da tunanin sake b'ullo da wata hanyar dan ba zata hak'ura ba.
*Egypt*
D'an dakatawa yayi daga danna na'urar da yake ya zubawa k'ofar ido, ganin Zeyfi ta shigo yasa ya d'auke kan shi ya mayar kan na'urar ya ci gaba da dannawa
Tana shigowa ta mayar da k'ofar ta rufe, hannu d'aya ta sa ta dafe bango d'aya hannun kuma ta sa a mad'aurin rigar dai dai k'ugunta ta warware k'ullin, cike da salon jan hankali ta cire rigar ta zubar da ita k'asa, hakan ya rage mata daga bras sai pant kalar ja da suka kamata suka mat kyau.
Duk da ba kallonta yake ba, amma ganin abinda take ta wutsiyar ido sai ya sa ya d'aga kai ya kalleta, wasu mayatattun yawu ya had'e kafin ya sake d'auke kan shi, hak'ik'a kam shi namiji ne mai buk'ata, kuma a yanzun daya gan ta a haka ta tayar masa da duk wata tsohuwar sha'awarsa daya jima bai sauke ba sakamakon rashin samun kwanciyar hankali, saidai a yanzun ma baya jin zai iya samun nutsuwar da har zai yi hak'urin ya gamsu, dan labari ya samu wai Zafeera tana wajen sarki Musail, shi da ya zuba kunnuwa yana jiran ya ji yak'i tsakanin sarki Musail da sarki Wudar, a cikin wannan tartsatsin shi kuma zai zagaya ya d'auketa ba tare da shan wata wahala ba, sai kawai ya ji wai tana can kuma babu abinda ya faru.
Ganin bai kulata ba yasa ta shiga takawa cikin kwarkwasa da kissa tana karairaya tana kashe masa ido, har saida ta hau kan gadon tana rarrafawa, k'afafunshi dake mik'e ta shiga shafawa tana sumbatarsu cike da k'warewa da son kai shi bango dan ya karb'i tayinta, d'aga jajayen idonshi yayi ya sauke kan ta, cikin dakusashiyar murya yace "Kk...e, la..fiya?"