← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 86

Sashe 66

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta zauna tana zuba masa ido dan abinda take son ji kenan, gyara zamanshi yayi a mutumce ba tare daya kalleta ba yace" Sarauniya, duk abinda zan fad'a miki abinda na ji ne daga bakin wacce abun ya faru da ita, ma'ana tsohuwar hadimarku Nanna Kapoor, ta fad'a min awa d'aya da rabi ne bayan kin haihu ita ma ta fara nak'uda, allurar da aka miki ta bacci ta sa baki samu damar ganin abinda kika haifa ba wanda bai zo a raye ba, a wannan tsakanin ita kuma ta haife abinda ke cikinta wanda sarki Musail shi ne musababbin shi, k'arfin mulkinshi ya nuna mata tare da mata alk'awarin kud'ad'e masu yawa idan har ta ba shi yarinyar da ta haifa, amma sai tayi taurin kai saboda soyayyar d'a da uwa, to fa hakan ne yasa aka koreta a wulak'ance sannan ya raba da yarinyar wacce aka baki a matsayin yar da kika haifa."

Kallon fuskarta yayi cike da ladabi yace" Amma magana ta gaskiya ke namiji ma kika haifa ba mace ba."

Yanda ta saki baki ta saki ido tana kallonshi, hawaye kawai ke malala a idonta, juyawa tayi ta kalli Musail tace" Da gaske ne abinda ya fad'a?"

Lak'was jikinsa yayi tare da komawa ya zauna kan kujera kanshi k'asa yace" Hakane, gaskiya ne abinda ya fad'a."

Fashewa tayi da kuka tace" To amma me yasa? Me yasa ka rabata da 'yar da ta sha wahala ta haifa? Ka san rad'ad'in da uwa take ji idan ta rasa abinda ta
haifa?"

A sanyaye Umad ya kalleta yace" Saboda soyayyarki ne sarauniya, a duk mutanen da na zanta da su abu d'aya suke fad'a min, sarki yana son sarauniyarsa fiye da komai."

Cikin k'unar zuci da tsana Zafreen ta fara kuka tana kallon Musail tace" Kai mugu ne azzalumi, ka rabani da mahaifiyata saboda farin cikin matarka, kun banzatar da ni kun wulak'antani saboda son zuciyarku, ba zan tab'a yafe muku ba."

K'ank'ance ido Musail yayi yana kallonta yace" Kenan saboda haka kike son kasheni?"

A harzuk'e kamar zata kai masa duka tace" Ba ma kai kad'ai ba, har da su duka iyalinka, dukanku na so kashewa, kuma sai hakan ya tabbata."

A hassale Musail ma ya mik'e tsaye yace" Saboda me za ki had'a da su, ni ne na miki laifi, me yasa su zasu fuskanci hukuncin?"

Cikin fitar hayyaci tace" Saboda dalilinsu ka wulak'anta mahaifiyata, a da ina ganin kulawarka, amma daga ranar da aka haifi wannan..."

Ta fad'a tana nuna Ayam sannan ta d'ora da" Sai ka canza min, na d'auka kana son samunta ne dan ka cutar da ita, shiyasa har na yi yunk'urin taimaka maka, amma kwanaki kad'an da suka wuce na fahimci ba gaskiya ba ne, hasalima na gano kai ne ka ke bata kariya da kulawa."

Kallon tuhuma da neman k'arin bayani ya mata, hakan yasa ta yin murmushin yak'e tace" E, na gano komai ai, ka tuna *Ahmad*?"

Rarraba ido yayi yana kallon k'asa, wata dariyar ta kuma yi tana fad'in" E mana, Ahmad ba, wanda yake isar da sak'onka a wajen su Habbee, na ganshi kuma ya fad'a min komai dake faruwa."

Dafe k'irji Juman tayi ta mik'e tsaye tace" Me kike fad'a haka Zafreen? Me ya sako su Habbee a cikin wannan maganar?"

Wani kallo ta mata tace" Saboda ba ke kad'ai su ke wa aiki ba, har da shi ma Musail d'in."

Da sauri Juman ta kalleshi tace" Da gaske hakane?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace" Hakane Juman, lokacin da aka nemi Zafeera aka rasa hankali ya tashi matuk'a, dan yanda na shirya bata kariya ban shirya da b'atanta ba, sai nayi tunanin masu nemanta ne suka sameta, a kwana biyu tak aka nemo min inda su Habbee suke da yarinyata, dan na bata kariyae data dace haka na sa Adah ya kashe abokan tafiyarsa su uku sannan ya dawo min da labarin Ayam tana cikin k'oshin lafiya, daga lokacin na canza musu gari daga k'auye zuwa Larhjadin, wanda mak'iya da dama tunaninsu bai basu wanda suka sace Ayam za ta zauna gari kusa da Khazira ba, da wannan na samu nasarar saka ido a kan duk wani motsin Ayam, sannan na ke sa wa ana k'ara bincika min haka lokaci zuwa lokaci."

Wasu hawaye Juman ta sako masu zafin gaske tace " *Abban Ayam* kasan da haka me ya sa baka tab'a fad'a min ba ko sau d'aya? Me ya sa baka fad'a min kai ma so ka ke ka ceci rayuwar 'yarmu ba?"

Girgiza mata kai yayi yana matso yar k'wallar data taru a kurmin idonshi yace "Ta ya zan fad'a miki a lokacin ki yarda Juman? Ba kya saurarata sannan kin tsaneni, bugu da k'ari kina kallona a matsayin wanda ke son kashe 'yarmu."

Numfashi ya sauke a nutse yana kallon k'asa yace "Bayan Dhurani ya sanar da ke fassarar mafarkinki, ni ma ya had'u da ni ya sanar da ni, saidai ya k'ara da fad'in wannan yarinyar da za'a haifa za ta zama tashin hankalina ce, ita ce mafarin rugujewata da kawo k'arshen mulkina, sannan ya fad'a min tabbas ita ce za ta zama silar mutuwa sannan ta kawo k'arshen mulkin zalincina, na ji ba dad'i sosai a lokacin sannan na shiga firgici na abubuwan daya fad'a min, sannu sannu na fara shiga damuwa na abinda ya fad'a min, haka na fara rasa nutsuwata saboda tunanin mutuwata, wata rana da yamma sai kawai na je fadar abun bauta Ghira dan na samu mafita a wajen Dhurani, a wannan lokacin ne na san komai na kuma fahimci komai, na samu malami Dhurani da waziri Khatar da biyu daga cikin fadawa na suna tattaunawa a kai na, kasancewata sarki ya sa masu gadin k'ofar kai tsaye suka bud'e min, shiyasa ba su tunanin wani zai iya shigo musu ba tare da izininsu ba, abinda na ji ya gigita ni, na shiga tsananin firgicin da ya fi wanda na zo da shi."

Numfasawa yayi sosai sannan ya d'ago ya kalli Juman dake ta shashek'ar kuka Ayam na durkushe gabanta tana rarrashi yace" A nan na ji duk shirin da suke na ganin bayana ne, suna shirin kashe ni dan su maye kujerar mulki na, sannan su d'auki fansa akan laifin da ni ban san ya faru ba sai a tarihi, amma sai gashi da taimakonsu suna tunzurani ina aikata abinda al'ummata zasu k'i ni su kuma kirani da azzalumin sarki, juyawa na yi a wannan lokacin na koma saboda kaina daya fara sarawa, saboda abinda na ji malam Dhurani ya fad'a, cewa ya fad'a min k'arya akan yar cikina da za'a haifa, tabbas baiwarta gaskiya ce, saidai batu na zata kasheni ta ruguza mulkina k'arya ne, shirinshi ne kawai saboda yana so na kasheta da hannu na dan kar ta kawo masa targand'a a cikin lamuransu, na jima da jimamin wannan lamarin a rayuwata, daga baya kuma bayan tattaunawa da zuciyata da kuma shawarar da amintacce na wato Adah ya bani, sai muka fara buga wasar daidai da na su, inda a zahiri na ke nuna musu na tsani Zafeera kuma kasheta shine burin rayuwata, amma a bad'ini ina kulawa da matata da kuma abinda yake cikinta, wanda wasu lokuta da gangan na ke fad'in magana marar dad'i duk dan tunanin abinda zai je ya dawo."

Sosai Juman ke kuka haka ma Ayam data girgiza kanta tana hawaye tace" Ban tab'a yarda ba har zuciyata cewa wai mahaifina zai kashe ni, duk da ban san shi ba kuma ban tab'a ganinshi ba, amma dai na ji a zuciyata ban gamsu ba, ashe duk makirci ne, kuma aka yi sa'a ya mamaye duniya har kowa ya yarda da hakan."

Yanda jikin Dhurani ke rawa ne yasa shi yin zaune k'asa d'abas kamar an hankad'ashi, zufa yake sosai yana ta zazzare ido, cikin magiya da rawar murya yace" Ran...ranka shi...dad'e, ka min...rai, na tuna."

Girgiza kai Musail yayi yace" Ba na kiraka nan dan na yafe maka ba ne, dole ka fuskanci mutuwa Dhurani, zunubinka babba ne."

Kallon Zafreen yayi yace" Abinda ya faru tsakani na da Nanna ba abu bane da kowa ya sani, ta ya kika san labarin mahaifiyarki?"

Kafin ta yi magana Umad dake k'are mata kallo a lalace yace" Dhurani ne, gashi nan gabanka, shi ne ya busawa labarin rai, saboda yayi anfani da ita ta yanda zata zama barazana a gareka, kuma yayi nasarar samun haka tunda har yanzu burinta bai wuce ta kasheku ba sannan ta maye abinda take ganin na ta ne."

A hankali Musail ya kuma kallon Dhurani yana jinjina kai, murmushin yak'e yayi yace" Kun k'irk'iri labari, sannan kun aiwatar da wasan, ku kuka samar wa da kowane jarumi rawar da zai taka, sannan a bayan fage ku kuke taka taku rawar."

Cikin takaici da hargagi Juman ta nunashi da yatsa tace" Amma Dhurani Allah ya isa tsakani na da kai, ba zan tab'a yafe maka ba bak'in munafiki, dama abinda ka shirya mana kenan? Ka tunzura mijina da labarinka na k'arya hakan yasa na dinga jin haushinsa ina wasan b'uya tsakani na da shi."

Jan majina tayi ta kalli Musail tace" Indai har abubuwan da suka faru sa saninka, kenan ka san da zuwana a lokacin da kuke tattaunawa kan yanda zaku kashe Zafeera bayan na haifeta?"

A hankali ya gyad'a mata kai alamar e tare da fad'in" Ina sane na tura jakadiya ta turo min ke, saida na tabbatar na ji takon tafiyarku sannan na fara magana tsakanina da Dhurani, na kusan kinji saboda yanda kika canza min daga lokacin, saidai ban san me kike shiryawa ba har sai ranar da na ji daga su Habbee cewa ke kika saka su."

A hankali Umad ya kalli Musail d'in yace" Shiyasa ka san komai kenan? Hatta da aurena da... Ayam?"

K'uri kowa ya masa da ido yana kallo kamar wanda ya fad'i wani mugun abu ban da Musail kawai, shi ma Umad bai yarda ya kalli kowa ba sai dakewa da yayi ya buga fuska, a sauk'ak'e Musail ya jinjina masa kai alamar e, sannan ya gyara zamansa ya kalli Adah, nuna masa Dhurani yayi yace "Ka kai min shi kurkukun Sabah."
Chapter 66 · 0% Book details