Sashe 84
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yaren fulatanci tace "Minkam miwala emi boya on (Sai na kwana ina kuka)."
Tsura mata ido yayi da mamaki, d'an shafa k'eyarshi yayi ya sake jawo kugunta tsam ya matse sannan yace "Matar sarki me kika fad'a ne haka?"
Matse bakinta tayi sosai ta d'aga kafad'a alamar "Uhum!"
Marairaicewa yayi yace "Na rok'eki ki fad'a min abinda kika fad'a?"
A harshen hausar da zuwa mata kawai yayi tace "Cewa na yi zan kwana ina kuka."
Zaro ido yayi jin ta k'ara b'atar da shi, amma sai wata dubara ta zo masa, jayeta yayi daga jikinshi ya d'an had'e fuska yace "Yanzu ni kika aikawa wannan ashariyar?"
It ma kamar yanda ya zaro ido d'azun haka tayi tace "Lahhh! Wallahi ba haka na fad'a ba, cewa na yi fa zan kwana ina kuka."
Murmusawa yayi ya jayeta daga jikinshi yace "To na tafi."
Gimtse bkinta tayi ta bishi da kallo, tana so ya zauna kusa da ita saidai gaskiya ruwan nan da take ta bulbulowa sun saka ta jin tsantsenin kanta, bare har ta zauna da shi a irin wannan yanayin.
*Khazira*
Kamar yanda ya zaa sabonshi shiga wuraren da jama'a ke taruwa dan ya ji matsalolinsu da kuma ganin yanda abubuwa ke tafiya, yau ma a shirye yake cikin sassauk'an yadinshi an masa d'inkin riga yar shara, sai wata hula daya saka a kan shi ga bak'in gilashi da kuma face mask daya saka, hakan yasa kowa harkar gabansa yake babu wanda ya kula da shi.
Rab'ashi tayi ta wuce ba tare data kula da shi ba, hakan yasa shi juyawa ya bita da kallo, kallo irin na zuciya ta ga abinda take so, da sauri ya juya gaba d'ayansa sannan ya fara bin ta a nutse a nutse, alamu sun nuna masa ko dai 'yar sarki, ko wacce ta shafi sarauta, duk da abaya ce a jikinga, amma hadiman dake take mata baya suna rik'e da ledojin ke nuni ta shafi masarauta kai tsaye.
Tunda ya bi bayanta shi ma escorts d'in shi suka bi shi a baya ba tare da yanda kowa ke ganewa ba, dan ba ma a layin da yake bi suke bi ba kasancewar kasuwa ce babba.
Daidai motocinsu biyu suka tsaya, da sauri wani bafaden ya bud'e mata k'ofa tunda ya ga ta taho, hadiman kuma suka k'arasa gaban d'aya motar, ganin duk sun shiga da hanzari an tayar da motocin yasa shi juyowa inda escot d'in na shi suke, suna had'a ido da wani ya masa alama da hannu ya d'auko mota, dan in da ido ya masa ba zai gane ba dukansu bak'ak'en gilashi ne a fuskarsu.
Cikin hanzari kam aka kawo motocin guda uku da babur biyu da matuk'ansu suka bi bayan motocinsu, doguwar tafiya sukayi har saida suka ga an dunfari shiga wani makeken gida, suna kallo mai gadi ya bud'e musu suka shiga su kuma suka tsaya, a hankali ya furta "Yar sabon sarki ce kenan?"
Babban escot d'in shi ne ya juyo a ladabce yace "Ba masaniya yallab'ai, saidai idan kana so za'a bincika."
Girgiza kai yayi sanda yake d'aure d'amarar wandonshi dan har ya canza kaya a cikin motar sannan yace "Ba buk'ata, zan sani da kai na."
Yana fad'a ya bud'e k'ofar ya fito, duk fitowa sukayi sai ya dakatar da su yace "Yak'in neman aurena zan tafi, ba buk'atarku a nan."
Da d'an sauri ya d'aga k'afarshi ya tunkari shiga, mai gadi na shirin rufe k'ofar ya ganshi, saidai yanda ya fito cikin shirinshi na wanda aka sani yasa shi kwasar gaisuwa a mutumce sannan ya bashi hanya ya wuce har yana lek'awa ya ga to ina jami'ai da masu tsaro, yana ganinsu a k'ofar gidan ya jinjina kai ya koma ya zauna.
Har hadiman sun kwashi kayan data siyo sun shige da su, ita ma bakin wata flower ta tsaya tana amsa waya, hakan yasa daga bayanta ta ji an ce "Barka da warhaka."
Mamaki ne ya fara rufeta saboda yanda aka mata magana ta jima bata ji haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi, wata fad'uwa gabanta yayi saboda wanda ta gani tsaye a gabanta, wannan kyakyawan matashin mai jini a jika, wanda ya shiga sahun jerin mutane mafi d'aukaka a harkar mulki, matashin daya shiga sahun manyan mutanen da ake zana sunansu, matashin da ya shiga d'aya daga cikin matasan da sukayi mulki da k'ananan shekarunsu, *Abdul Basid' Murphy* shugaban k'asar Texanda, wanda ya lashe k'uri'ar al'umma ba da kud'i ko kyautar cin hanci ba, sai dan cancantarshi da kuma zak'wak'urancinshi ga k'asarshi.
Ba tare data sani ba ta aje wayar tace "Yallab'ai?"
Murmushi ya sakar mata yace "Yallab'iya."
Yar dariya ce ta nemi kubce mata sai kuma ta gimtse ta kawar da kanta, jim kad'an ta juyo ta kalleshi tace "Yallab'ai lafiya ko?"
Kafeta yayi da ido yace "Lafiya ba lafiya ba, na zo kama wata mai laifi ne."
Da mamaki tace "A gidan nan ?"
Jinjina mata kai yayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tace "Bismillah to, wuce ciki."
Gyara tsayuwa yayi ya kalleta da kyau yace "Yallab'iya, wajenki na zo."
Nuna kanta tayi tace "Wajena kuma? Wani abu ne ya faru?"
A tsanake yace "Ba abinda ya faru a yanzu dai, amma gaba kad'an zamu gane da yiwuwar faruwar wani abun."
Nuna masa hanyar shiga falon tayi tace "Bismillah to."
" *Ina son ki*." Kalmar daya fad'a kenan kamar saukar mari a kunci, da wani razanannen firgici ta kalleshi ta a zazzaro ido, a zuciyarta kuma tana maimaita kalmar ina son ki, me ya d'auketa to? Me ya gani a tare da ita? Wace manufa ce ta kawoshi gareta ? Yasan ma wacece ita?
A hassale ta juya da niyyar barin wurin yayi gaggawar tare gabanta yace "Baki ce komai ba?"
Kallonshi tayi fuskarta a had'e sosai tace "Me kake so na ce? Me zan fad'a maka? Kasan ko ni wacece? A budurwa ka d'auke ni? Da zaka tareni da wannan maganar kai tsaye."
Wayar hannunta ta d'ago masa tare da danna madanni hoton Ayam ya bayyana akan screen d'in, nuna masa tayi tace "Ka ga wannan? To 'yata ce, yanzu haka ita ma tsohon ciki ne da ita, dan haka ka ja jikinka malam, ina girmamaka sannan ina mutumta alak'ar dake tsakaninka da tsohon sarki *mijina* mai mutuwa."
Tunda ta fara magana yake kallonta, tana dasa aya madadin ta ji yace" Dan Allah ki gafarce ni, wallahi na d'auka budurwa ce a yanda na ganki."
Amma sai ya saki murmushi ya kuma furta" Ina son ki, kuma ina so na aureki, ba zan takuraki ba idan baki amince ba, aa dai zan tabbatar na shiga rayuwarki na addabeki har sai kin fad'a cewa kin amince zaki aureni."
Galala tayi da baki sai ta rasa me zata fad'a masa kuma, tana kallo har ya kama hanya ya fita a gidan, nuna kanta tayi a hankali tace" Ni? Ni wai yake so? Ni Juman? Ina ! Da 'yar tawa zan wani tsaya na yi aure, babba ma ba zan kula ba bare wannan da in ba tsarana bane a shekaru, to bai wuce shekaru d'aya ko biyu ne ya bani fa."
Murgud'a baki tayi ta juya ta shige ciki tana bambami a zuciyarta da harare harare tana ji ya gama kunyata ta ai da wannan kalmar daya zo mata da ita.
**************
Irin tsangwamar da matan dake magark'amar suka d'ora mata shi yayi sanadiyar zubewar cikinta wanda saida ta jikkata sosai saboda cikin ya kai wata hud'u, ta jima kwance a asibiti k'ark'ashin kulawar jami'an tsaro, yanzu kuma data samu sauk'i ta koma magark'ama sai ta canza sosai, kullum tana d'akinta ita ka'dai, idan kuma an fito da su ne to zaka ganta a rakub'e, da haka take cike da takaicin rashin nasararta a rayuwa da kuma nadamar abinda tayi wanda take ji a yanzu daa batayi ba.
*************
Babbar magark'amar dake jahar Khazira aka kai shi, wacce ke tsakiyar babban tekun Gafil, saidai shi sab'anin Joyran ne dake nadama, shi kam kullum yana cikin kula duk wanda ya kulashi, yana cikin fad'a da mutane, wata rana ya doke wata rana kuma a dokeshi, Zafeera kuma ta k'i barin tunaninshi, har yanzu da ita yake kwana yake tashi, yayin da zuciyarshi ke k'ara k'ek'ashewa da tsanar Umad da farautar dama ko ya take ya kassara rayuwarshi, da haka shi ma yake tashi rayuwar a gidan da yake fad'in baya da iko a cikinshi, madadin rayuwa a matsayin sarki, yanzu yana rayuwa a matsayin mai laifi kuma duk ta dalilin Umad ne.
**************
Tunda ta mareshi a fuska ya rasa lafiyar sa, kumburi ga dinga yi tana kumewa, kunnenshi kuma ya fara masa azababben ciwo, idan dare yayi baya iya bacci ko kad'an, sannu sannu abun ya fara k'amari har saida aka fara dubashi a asibitin masarauta, da aka kasa a nan asibitin aka turashi babbar asibiti, da abun ya ci tura kawai sarki Adah yace a dawo da shi a aje a kurkuku ya k'arasa girbe abinda ya shuka, dan a jikinshi ya ji kawai ba zai warke ba saboda wacce ta mareshi da kuma abinda ta fada bayan tayi marin.
Izuwa yanzu kunnenshi ruwa yake fitarwa, ga kumburin nan da idan ka ga rabin fuskarshi zaka d'auka wani abun aka saka masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinshi, a haka yake rayuwar wacce a kullum mutuwa yake fata ta zo ta d'aukeshi amma Allah bai kawo k'arshen kwanan na sa ba.
*Giobarh*
Adah da kanshi ya sanar da ita ai fa shugaban k'asa ne yake son mah d'in ta da aure, shi ma kuma yayi auren rasuwa matarsa tayi, d'ansu d'aya mai shekara uku a duniya, tana jin haka tace tasan me za ta yi, ai kam tsaf ta kwashe ta fad'awa su Bilkees, nan fa suka saka Juman gaba da umarninsu da shawawari, daga k'arshe dai ta amince amma fa ta rantse sai bayan Ayam ta haihu za'a d'aura mata aure, haka kawai ba zata tafi gidan miji ba ta bar yarta data haihu ba gyara, alhalin ranar da suka had'u da shi ma ta tafi siyo kayan gyaran da take tanadi ne ta ma 'yarta.