← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 86

Sashe 49

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata tanka masa ba saida ta zo daf da k'ugunshi ta dinga zura hannu a cikin bargon daya d'an rufa zuwa k'ugun na shi, dake gajeran wando ne jikinshi mai roba hakan ya taimaka mata wajen zura hannunta ciki, tana tab'o kayan arzikin ya d'an zabura yana fad'in "Ke wai lafiyarki k'alau, me ye haka?"

D'ago narkakkun idonta tayi cikin muryar d'aukar hankali tace "Idan baka so ka dakatar mana."

Aje na'urar yayi yasa hannayenshi da k'arfi ya fincikota, kamar wanda zai cinyeta sai kuma ya cabki leb'enta ya had'a da na shi ya shiga tsutsa da sauri sauri, dake abinda take so ne sai kawai ta shiga biye masa suka dinga yamutsa junansu, sunyi nisa sosai suna neman gangarewa kawai k'aramar wayarshi tayi kururuwa.

Da sauri ya d'ago dan wannan kiran sarki Abdallah kad'ai ke da wannan k'arar, hakan kuma ya tabbatar masa da ya zo kenan? Zunbur ya sauka daga kanta daga shirin neman hanyar da yake wawuro wandonsa ya maida ya d'auki wayar, saida ya nutsu ya saita kanshi ya tabbatar ba za'a gane komai ba kafin ya d'aga ya rangad'a sallama tare da d'orawa da fad'in "Allah ya ja zamaninka mai martaba."

Zeyfi data tashi zaune kallonshi take ranta b'ace tana fatan wayar nan kar ta nesanta ta da shi, sai kuwa ji tayi yace "To mai martaba, gani nan zuwa in shaa Allah."

Da sauri ya shiga gaggautawa yayi wanka ya fito yana shiryawa Zeyfi ta sauko daga ka gadon ta d'auko doguwar rigarta ta bacci ta saka, k'arasawa tayi kusa da shi tace "Ina kuma zaka je mijina?"

Cikin b'acin rai da jin haushi yace "Ban gane ina zan je ba? Ina zamanki ne a gidan nan? Kuma ina kunnuwanki suka je lokacin da nake wayar da baki isa ki gane da wa nake yi ba?"

Kwalbar turarenshi ya d'auka ya feshe jikinshi sannan ya d'auki k'aramar hula bak'a mai kyalli ya saka, juyawa yayi zai fita ta sake fad'in" Wai ina zaka tafi cikin daren nan?"

Nunata yayi da yatsa yace" Idan kika sake min magana sai na dalla miki mari."

K'wafa yayi ya juya ya zura wasu silipas ya bud'e d'akin ya fice, wani wawan tsaki ta ja ta cije yatsarta cike da takaici kafin ta bar d'akin.

Yana fita k'ofar gidan ya samu bak'ar mota reng rover a pake, dreban motar ne ya fito ya bud'e ma Bukhatir d'in k'ofar baya ya shiga sannan ya mayar ya rufe ya tsaya bakin mota dan ya jirasu.

Wani irin zama ne yayi a cikin motar na ladabi da girmamawa, ya kasa d'aga kan shi bare ya had'a ido da sarki Abdallah, a haka suka gaisa ya masa sannu da zuwa da tambayar "Ranka shi dad'e ai bansan kana hanya ba, da na d'aukoka da kai na daga airport."

Murmusawa yayi cike da dattijantaka yace "Kar ka damu Bukhatir, da ina so a san zan dawo, da na kiraka a waya."

Da giramawa ya fad'i "Hakane ranka shi dad'e, Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana."

"Ameen." Sarki Abdallah ya fad'a yana jinjina kai a hankali, shiru motar ta d'an d'auka na wani lokaci kafin sarki Abdallah yace "Bukhatir, ka san me yasa na ta so da kai na na zo yanzu?"

Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba mai martaba, sai dai na shiga zulumi da tunanin me ya hana sarkina zaunawa a d'akinshi na alfarma ya jira na d'an lokaci ni na sameshi."

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace "Hakane, abu ne mai mahimmanci da ya shafi rayuwata, shiyasa na kasa hak'ura gari ya waye."

Numfasawa yayi a hankali yace "Bukhatir, ka san da na had'u da 'yar' yata wato d'iyar Juman Zafeera?"

Da sauri ya d'ago kai ya zuba idonshi cikin na shi, amma da sauri ya sadda kan shi yana mai jin gabanshi na tsananta fad'uwa, hatta da jikinshi saida ya ji ya fara kyarma zai d'auki rawa, yanda ya kasa furta komai yasa sarki Abdallah d'ora da fad'in" Na had'u da ita, kuma na yi farin cikin haka, saidai akwai wata babbar matsala."

Da k'yar ya bud'i bakinshi yace" Sarkina wace irin matsala kuma?"

Jim sarki Abdallah yayi sai kuma yace" Kamar yanda ka sani ne daga haihuwarta zuwa yanzu ta rayu cikin had'ari, amma ubangiji yana kareta daga sharri duk wani mai sharri, ban tab'a jin d'ar a lokacin da aka rasata ba, amma a yanzu ina jin zuciyata ta kasa samun sukuni saboda inda ta kai kanta."

A ladabce Bukhatir yace" Ina ta kai kanta haka ranka shi dad'e?"

Shiru sarki Abdallah yayi kamar ba zai yi magana ba, can ya numfasa yace" Wajen mahaifinta, sarki Musail."

Da sauri ya kalli sarki Abdallah duk da dai yasan da maganar, amma dan kar ya saka mishi wani shakku yasa shi fad'in" Wajen sarki Musail? Kasheta fa yake son yi?"

Jinjina kai yayi yace" Sanin haka yasa hankali na ya kasa kwanciya."

Shi ma jinjina kai yayi tare da tunanin bari ya fad'a masa shawarar da shi kan shi ya yanke a kan ta d'in, kallonshi yayi a hankali yace" Sarki na, kwanciyar hankalinka shi ne kwanciyar hankalin duk wani dake k'asar nan, ka kwantar da hankali, ni na ma ka alk'awarin zuwa safe zan samo maka labarin yanda take ciki, daga haka kuma sai mu san abun yi, dan gaskiya zamanta a can akwai had'ari."

A tsanake ya kalleshi yace" Ka tabbata zaka iya yi min haka Bukhatir?"

Jinjina kai yayi yace" In shaa Allah sarki, wannan alk'awari na ne a gareka."

Jinjina kai yayi a hankali yace" Shikenan Bukhatir, na yarda da kai, ina jira na ji daga gareka."

Da haka suka rabu ya fito a motar su kuma su ka bar unguwar yana mai jin ya fara samun nutsuwa a zuciyarshi.

_Ga duk wanda bai siyi *lu'u lu'u* ba ya hanzarta ya siya dan fara samun *Badak'ala* nan kusa_

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:40 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*28*

Yana shiga ciki d'akinshi ya wuce kai tsaye, ganin Zeyfi bata nan yasa ya mayar da k'ofar ya rufe, dan daya sameta korar kare zai mata dan ya samu damar yin abinda ya dace, da sauri ya cire hular kanshi ya d'auki na'urar nan ya shiga rubuta sak'o ga d'aya d'an lek'en asirin shi dake gidan sarki Musail.

Bai aje na'urar ba bai kuma rintsa ba kamar yanda bai yi wani abu da zai anfane shi ba, haka ya d'auki sama da awa d'aya yana jiran ganin dawowar amsar tambayarshi, sak'on na dawowa yayi gaggawar bud'ewa ya duba, ya d'an shiga tashin hankali daga bayanan da mutumin ya bashi, saidai kuma ya ji a ranshi su ma bayanan wasu makamai ne da zai iya sake tunzura sarakunan biyu su kaure da yak'i, dan haka ya jinjina kai yana fatan wayewar gari tare da d'an kishingid'awa kafin gari ya waye.

*Zaune* yake gaban sarki Abdallah kan kujera ya sadda kanshi sosai ya nutsu, cikin ladabi da girmamawa yace "Ranka shi dad'e, kamar yanda na maka alk'awari zan samo maka bayani akan halin da take ciki."

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace "Na'am, an samu wani abu ne?"

Jinjina kai yayi yace "E ranka shi dad'e, an fad'a min tana cikin k'oshin lafiya tare da mahaifiyarta, sai dai kuma a safiyar da ta zo wani abu ya faru wanda a zahirance ya yi kama da tsautsayi."

Da mamaki sosai sarki Abdallah yace "Mahaifiyarta kuma? Kana nufin Juman?"

Gyad'a kai yayi yace "E yallab'ai."

Da sauri yace "To ta ya? Yaushe Musail ya fito da ita daga kurkuku?"

Cikin ladabi yace "Jiya ne yallab'ai bayan zuwan ita Zafeera."

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yana murmushi a zuciyarshi yana ayyana "Kenan shi ma kwarjininta zai iya tasiri a kan shi?"

Kallon Bukhatir yayi yace "Me ya faru to?"

Cikin nutsuwa yace "A cikin d'akin da aka sauketa ne za ta shiga ban d'aki tayi wanka, kafin shigarta sai d'aya daga hadiman daya had'ata da su ta fara shiga dan tabbatar da auna ruwan kamar yanda Zafeera ta buk'ata, a tak'aice dai mai martaba sai gawar matar aka fito da ita, wai wutar lantarki ce ta ja ta har ta rasa ranta."

Lumshe ido yayi a hankali yace" Subhanallah, Subhanallah, lallai wannan kam tsautsayi ne a zahiri, amma a bad'ini da wata manufa a kai."

Sake kallon Bukhatir d'in yayi dake fad'in" Hakane ranka shi dad'e, shiyasa nake so na bayar da wata shawara idan har zai yiwu."

Cike da kulawa yace" Me kuwa zai hana Bukhatir? Fad'a mana na ji, kar fa ka manta kai d'an d'an uwana ne, kuma a yanzu dai a yanda komai ke bayyana kai ne magajin wannan kujerar ta wa."

Da sauri Bukhatir ya d'aga kai ya kalleshi ba tare daya b'oye sha'awarshi ta son mulki ba yace" Na'am ranka shi dad'e?"

Jinjina kai yayi yace" Hakane, kar ka manta da mahaifinka yana raye akwai yiwuwar shi zai gajeni, to baya raye yanzu, ni kuma bana da d'a namiji, macen kuma tana gidan mijinta, ka ga kenan kai ne magaji na na gobe."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, wani sanyin dad'i ne ya ratsa zuciyarshi, farin ciki ya mamayeshi ta yanda yake ji kamar ya zumduma ihu, sarki Abdallah ne ya katse masa shauk'insa da fad'in" Ina jinka Bukhatir, me ye shawarar ta ka?"

Cikin farin ciki da jin dad'i yace" Ranka shi dad'e, a gani na rayuwar Zafeera ta na cikin had'ari, bai kamata mu sake yin shiru ba a karo na biyu, sarauniya Juman 'yarka ce, amma azzalumin sarkin nan ya rabaka da ita ba dan ya fi k'arfinka ba, a gani na yanzu Zafeera ba yarinya ce da ya kamata mu sa ido ita ma har ya ga bayanta ba, a gani na me zai hana mu tunkareshi a wannan karon, ko ba komai zamu karya alk'adarinshi na jin cewa ya fi k'arfinmu."

Tunda ya fara magana yake saurarenshi yana jinjina kai, saida ya dasa aya ya sauke numfashi sannan yace" Na ji abinda ka fad'a Bukhatir, amma ka bani lokaci zan yi shawara, abinda na yanke a kai zan nemeka."
Chapter 49 · 0% Book details