Sashe 40
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rintse idonshi yayi ya cije leb'en k'asa, a hankali ya shiga sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da sassauta rik'on daya mata har ya saki hannunta gaba d'aya, bud'a idonshi yayi a sauke a kan ta, da k'yar ya k'ak'aro maganar yace" Kuskure kike aikatawa, karki aikata haka Ayam."
Cikin rad'a tace" Me yasa? Da matsala ne?"
Kawar da kan shi yayi yace" Babba ma kuwa."
K'ura masa ido tayi tace" Wace iri yallab'ai."
Sarki Wudar ne ya katsesu da fad'in" Tunda kin min alk'awarin haka ki shirya, zuwa wayewar gari zan sa a rakaki zuwa fadarki tamkar sarauniyar k'asar nan."
Da farin cikin zata had'u da mahaifiyarta ta saki murmushi, ita har zuciyarta a uba take kallon tsohon nan, musamman ma daya tara farin gemun nan kamar na kakanta, uwa uba kuma mahaifin malaminta ne yallab'ai, sai kawai ta bud'e hannaye tsabar jin dad'i ta nufi sarki Wudar zata rumgume shi.
Tana daf da kai wa Umad ya daka wani k'arajin ta hanyar fad'in "What?"
Cak ta tsaya ta juya ta kalleshi inda sarki Wudar ma ya d'aga hannaye zai rumgume ta da farin ciki sai kuma ya kalli d'an na sa, a duburburce ya canza harshe zuwa yaren Italy yace "Ki gaggauta barin nan malama."
Turo baki tayi tana kallonshi ita bata ji dad'i ba, bubbuga k'afafu tayi k'asa ta juya ta shiga haurawa sama. Da gudu, satar kallonta yayi ya d'an dafe saitin zuciyarshi yana sauke numfashi mai nauyin gaske, idonshi ne suka k'yallara suka had'u dana mahaifinshi, ganin wani tuhumammen kallo da yake masa yasa shi juyawa da sauri ya fice a falon yana godiya ga Allah da basu had'a jikin nan ba, a gaskiya rasa nutsuwarsa yake wasu lokuta, gashi bai san e ke damunsa ba da yake jin haushi haushin mahaifins1 wasu lokuta a game da ita, shin niyyarsa ce a kan ta ba mai kyau ba? Ko kuma dai kishinta ne yake?
Saidai tashin hankali shi ne da ta ce zata had'u da mahaifinta kuma mahaifinshi ya amince da haka, me kuma zai faru a gaba? Me hakan zai janyo musu ko kuma zai janyo mi shi? Da wannan tunanin ya k'arasa b'angaren shi gaba d'aya jikinshi ba k'wari, da haka yayi alwala yayi sallah ya zauna kan sallayar yana jiran ya ji me zai faru.
*Khazira*
Kamar ba mahaifiya wacce ta haifeta ba, haka ta tsaya gabanta tana girgiza kai da murmushi d'auke a fuskarta tace "Mah, me yasa kika aikata haka? Ni dama na zargeki tun a waccen ranar, to me ye ribarki a yin hakan?"
Girgiza kai sarauniya Juman tayi cike da takaici tace "Kaico Zafreen, hak'ik'a ubangiji yayi gaskiya da ya ce yana fitar da rayayye a jikin matacce, sannan ya fitar da matacce a jikin rayayye, ko da yake zan iya cewa sak halin mahaifinki kika d'auka, amma ina bak'in ciki da haka, dan na so a ce kin d'auko ko da kad'an daga halina ne, ki sani kuma wannan banzan halin na ki shi zai nesantaki da burinki."
A wani wulak'ance ta kalleta tace" Me kike nufi Mah? Kin kuwa san girma da cin muradin burina? Shin kin ma san me ye barin na wa?"
Ita ma a gadarance ta kalleta tana gyara zamanta tace" Me ye burin na ki daya wuce ki gaji mahaifinki, duk fafutukar da kike Zafreen kina yi ne saboda idan ya mutu ki hau kujerar mulkinsa."
Cikin jin haushi ta kalleta tana mai d'aga murya tace" Kinsan da haka kuma shi ne kike min fatan rashin cikar burina, a kan me? Me yasa kike nuna min banbanci ne tsakani na da waccen banzar yarinyar da kika haifa?"
D'auke idonta tayi a kanta tace" Ni ban nuna banbanci tsakaninku ba, saidai nasan na yi abinda kowace uwa zata iya yi ne, sannan abinda na mata ko kece a halin da take ciki zan mata."
Tsugune tayi irin na mazan nan ta had'e hannayenta tana murmushin mugunta tace" Kinsan wani Mah? Na fita neman yarinyar nan ne dan na kasheta, sanda na fara had'uwa da ita da nasan ita ce, hak'ik'a dana fara canza mata kamanni, a ranar data mari fuskata kuma da ina da sanin ita ce, tabbas dana shak'e wuyanta har sai na tabbatar ta daina numfashi."
Wani shu'umin kallo ta mata tace" Kinsan me zan aikata yanzu da nasan wacece ita?"
Murmushin gefen labb'a tayi tace" Idan har muka sake had'uwa da ita saina kasheta ko ta wane hali, ba zan tab'a bari ta zama silar dakushewar rayuwata ba, na rantse miki sai na kasheta."
Malalacin kallo ta mata tace" Na so a ce kan iyalina a had'e yake tamkar tsintsiya, ba zan hanaki yunk'urin d'aukar matakin da kike ganin shi zai kaiki ga cimma ga ci, amma ki sani zakiyi dana sani wata rana, yar uwar ki kuma ba zaki iya kasheta ba, dan rayuwarta ba a hannunki take ba."
Mik'ewa tayi ta harareta tace" Ni kuma na miki alk'awarin zan nuna miki gawarta ganin idonki, sannan idan har burina ya cika, ke da masu bin addini irin na ki duk sai na hukuntak..."
Bata bari ta dire maganarta ba saboda haushi duk da bata da kuzari haka tayi azamar mik'ewa ta d'auke fuskarta da lafiyayyen mari.
A gigice ta kalli mahaifiyar ta ta tana rarako idonta hannunta dafe da kunci, rai a b'ace sosai sarauniya Juman ta nuna mata k'ofar fita tace "Fita ki bani wuri tun kafin na sab'a miki kamanni."
Mugun kallo ta wurga mata ka d'auka ita ma yanka mata tapi zatayi, a hassale sosai ita ma ta juya zata fita tana yin k'wafa, ta fita kenan mai tsaron k'ofar ya rufe Juman ta matsa kusan k'ofar tace "Ki ji da kyau, ki rik'e abinda zan fad'a miki yanzu da mahimmanci, ki rubuta ki ajiye Zafreen, addini na zai mamaye k'asar nan, dan ina ji a jikina a duk inda yar uwarki take tana cikin hasken rayuwa mai cike da saitin shari'a."
Tana gama fad'a ta juya ta koma inda take zaune, ita ma a hassale ta wuce inda Adah ma ya dinga binta da sauri har suka bar kurkukun.
*A* wajen sarki Musail ma dako yake hakan yasa ko rintsawa bai yi ba kamar dai sarki Wudar, ya kasa ya tsare yana son gari ya waye ya gae sarki Wudar d'in zaiyi, idan har ya turo masa yarinyar sa to ya zab'i zaman lafiya kenan, idan kuma rana ta fito babu labarinta hakan na nufin ya zab'i tashin hankalin da salwantar da rayuka, kuma shi tun jiya ya shirya ma hakan haka ma dakarunsa.
*Giobarh*
Kayan daya tura aka kai mata su ta saka, riga ce doguwa kalar bleue mai haske, bata da wata kwalliya ta zo a gani, sai dai daga k'asa tana da kwalliya kamar bakin lesh, haka dattijuwar jakadiyar ta nad'a mata d'an kwalin gwanin sha'awa, hakan yasa tayi kyau da ita duk da ba kwalliya tayi ba.
Fitowa sukayi zasu wuce amma ta nemi izinin shiga d'akin sarauniya Kossam dan ta mata sallama, dan ita kad'ai tasan me take shiryawa a zuciyarta, indai har ta tafi kam ba zata dawo ba har sai ta gyara tsakaninta da mahaifinta.
A hankali ta shiga d'akin tana mai zuba idonta akan gadon, k'arasawa tayi kamar kullum ta zauna kusa da ita, rik'o hannunta tayi tana mai fad'ad'a murmushin fuskarta cikin sanyin murya tace "Madam, ni zan tafi gidan mahaifina, ban sani ba ko zan dawo, amma dai nasan zanyi kewarki, kuma wata rana zan zo na ganki."
Hannunta dake cikin na ta ta sumbata tare da sakin hannun ta mik'e tsaye, sake sunkuyawa tayi ta sumbaci goshinta sannan ta kalli idonta tace" Na barka lafiya, ina rok'on ubangijina ya dubi lamarinki ya ci gaba da tsareki, Allah ya baki lafiya."
Juyawa tayi ta fita ba tare data juyo ba dan tausayin matar yasa yar k'walla taruwa a idonta, sarauniya Kossam ma k'ura mata ido tayi tana son tace" Tsaya." Saidai ya gagara hakan, tana ficewa a d'akin ta lumshe ido sai taji kamar zatayi kuka saboda tafiyar yarinyar da ko sunanta bata ji ba har yanzu.
Tana saukowa daga matak'alar daidai Joyran tana tsaye, ko kallonta ba tayi ba ta nemi wucewa ta barta, cikin jin haushi ta shak'o wuyan rigarta ta nunata da yatsa tace "Ke ce kika bada izinin a hanani shiga wajen yar uwata?"
Da k'arfi ta fizge rigarta ta kalleta sama da k'asa tace "Ba ni ba ce halinki ne."
Zata rab'ata ta wuce ta sake rik'o wuyan rigarta, cikin jin haushi Ayam ta buge hannunta da k'arfi tare da turata baya tana jan dogon tsaki, da sauri Joyran ta dafe mararta tare da fad'in "Kai kai kai!"
A hankalce ta bita da kallo ta kuma kalli marar data dafe, sarki Wudar dake tahowa kusansu cikin shigarshi ta alfarma ganin abinda ke faruwa yasa shi saurin k'arasowa, babu wacce ta kula da shi sai ma wani malalacin murmushi da ta saki ta gyara tsayuwa tana k'are mata kallo tace "Ya kamata kisan wani abu, dan kin kassara rayuwar uwar gidan nan ba hakan ke nufin zaki samu nasarar maye gurbinta ba, haka zalika ko da kin samu ciki da wanda kike ganin makusancin gidan nan ne, ba zaki samu abinda kike da buk'ata ba, dan sarauniya ta kusa samun lafiya da izinin Ubangiji."
Hanyar fita ta nufa haka shi ma sarki Wudar ya bita ba tare daya kula da Joyran d'in ba, cikin takonsu d'aya bayan d'aya sarki Wudar ya kalleta yace" A ina kika san tana da ciki?"
Da sauri ta kalleshi a zuciyarta tace" Kenan dai gaske tana da cikin?"
A zahiri kuma dakewa tayi tace" Yallab'ai ba fa iya gandun daji na ke da burin karanta ba."
Jinjina kai yayi ya saki murmushi har suka fita, motoci ta samu a laye da tarin dogarai duk suna jiranta dan su rakata, kallonshi tayi tace" Yallab'ai wannan tawagar fa?"
Da fara'a yace" Karki damu kan ki gimbiya, zasu rakaki ne har masarautarki."
Cikin damuwa tace" Amma ai sun yi yawa."
Girgiza kai yayi yana murmushi yace" Ba zaki gane ba, amma idan kika isa masarautar Khazira zaki fahimci girman matsayinki."