Sashe 62
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wani mamaki ya d'aga kai ya kalleshi yace "Jika kuma? Zafreen ta samu mijin aure ne?"
D'an murmushi yayi a hankali yace "Ba Zafreen ba ce, Zafeera, ko kuma na ce Ayam."
A gigice ya d'aga kanshi ya kalleshi, cikin fitar hayyaci da mantawa yace "Zafeera ce za ta yi aure? Ina raye?"
Da kallon tuhuma sarki Abdallah ya kalleshi d kuma mamaki yace "Kamar ya kana raye? Kana son ta ne?"
K'iri k'iri ya masa da ido yana kallo ba rusunawa, sai ya ke ji kamar ya hau sa da duka ma, yanda shi ma ya ga yana kallonshi yasa sarki Abdallah fad'in "Lafiya dai Bukhatir?"
Da sauri ya sauke kanshi k'asa yana girgizawa yace "A'a, a'a ba komai."
Jinjina kai yayi yana murmushi yace "Shikenan, ka je ka shirya tare da iyalinka za mu tafi, sannan a can gida ma (gidan iyayen Bikhatir) ka sanar da su, zamu tafi a jirgin safe in sha Allah."
Nauyayyen numfashi ya sauke yana jinjina kai amma bai ce komai ba, dan abun ya fi k'arfin yace komai, irin yanda aka shammace shi haka sai ya ji kamar zai mutu.
*Alhamdulillahn*
01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*36*
Sai daf da yamma ta farka daga nauyayyen baccin, idonta ta fara saukewa akan Juman dake kusa da ita tana kallon d'inkin da aka mata a gefen wuyanta, cike da kulawa Juman tace "Ayam, kin farka?"
D'an rufe idonta tayi sannan ta bud'e kafin ta muskuta tana son tashi zaune, dage d'aya gefen na ta taji an rik'eta an rumgumata a k'irji da niyyar taimaka mata, k'amshin turaren ya fara kai mata a hanci, hakan yasa ta zabura ta d'aga kai ta kalleshi, iskan bakinshi ne ya fara dukan hancinta yanda iskar hancinsu ya daki na juna.
K'ok'arin janyexa tayi daga jikinshi da mamakin wane rashin kunya ne kuma haka? Sai sarki Musail daya mik'e a lokacin zai fita ya kalleta yace "Bari ya taimaka miki, jikinki ba k'wari."
Yatsina fuska tayi ta d'an sake satar kallonshi, kawar da kai tayi tana kallon Musail ta d'aga bakinta da k'yar tace "Pah, ba na son...ganin sa a nan, please ka ce ma sa ya tafi."
A take suka kalli juna Umad da Musail, da ido ya masa alamar ya tafi kawai, Juman kuma da mamaki tace "Me yasa Ayam? Ya zo taimaka miki ne fa."
K'ofar d'akin aka bud'e aka shigo, kallon Haman d'in sukayi da ya shigo yanzu har da ita kanta Ayam, k'arasa zame jikinta tayi daga na shi tana kallon Haman tace "Ai ga mijin da zan aura nan, me zai hana shi ya taimaka min madadin mai kula da shi?"
Wani kallo ya watso mata daga tsayen da yake ba tare daya mik'e daga rank'wafawar da yayi ba wajen taimaka mata, sai kuma ya kalli Haman d'in dake ci gaba da takowa a hankali amma alamun tuhumar kansa sun bayyana a tare da shi, kallonshi yayi ya mik'e tsaye da kyau tare da zuba hannayenshi a aljihu.
Cikin kulawa Haman ya kalleta yace "Ya jikin na ki? Da sauki?"
Ayam ma kallon Haman d'in take dan haka kawai take jin haushin Umad da son ganin ta k'untata masa, amma da fari tana buk'atar ta samu lafiya kafin nan, k'wafa tayi a zuciyarta ta mik'awa Haman hannu tace "Dan Allah taimaka min, ina so zan shiga bayi."
Ba tare da tunanin komai ba ko ran wani zai sosu ge da hakan, duba da tsarin da suke kai shi da Umad, da kuma yanda ya dinga jadadda masa shirin su kar kuma ya yarda ya kwafsa, sai kawai yayi azamar rik'o hannunta sannan ya matso daf da gadon.
Daga cikin aljihun ya nemi damk'e hannunshi ganin yanda gaban idonshi ya rarumi hannunta, wasu d'atattun yawu daya had'e yasa Musail waro ido da kyau ganin yanda mak'wallaton dake wuyanshi ya wani yi sama da k'arfi sannan yayi k'asa, a hankali ya taka zuwa kusan Umad d'in ya dafa kafad'arshi yana murmushin mugunta.
Suna kallo har ta sauko da k'afafunta ta saka takalminta suka nufi hanyar ban d'akin dake cikin d'akin, bud'e mata k'ofar yayi ta shiga sannan ya tsaya yana jiran fitowarta.
A wani hassale a kuma dak'ile Umad dake hango ta ya ma zai tsaya kuma a k'ofar? Sai ya jira ta fito ko me? Uzirin na ta zai saurara? Cike da takaici yace "Zo ko?"
Saida ya gyad'a sannan ya tako ya dawo gabansu ya tsaya, Musail da har lokacin bai d'auke hannunshi a kafad'ar Umad bane ya kalleshi cike da son k'ular da shi yace "Gaskiya dokin k'arfe, da ba buk'atar b'oye b'oyen ai."
Da mamakin dake neman kasheta Juman tace "Wai me yake faruwa ne? Umad...?"
Kallonta Musail yayi yace "Kin tuna shi kenan? Na d'auka ba zaki ganeshi ba, saidai na manta akwai kamannin Urab a fuskarshi."
Girgiza kai yayi da dariya irin na "Haba yara." Sannan ya d'auke hannunshi a kafad'ar Umad ya kama hanyar fita, da kallo duk suka bi shi kuma kowa da abinda ke ranshi, Juman mamakin yanda ta ji yayi wasu maganganu yanzun take, ba ma yanzu na ita fa tun daren jiya duk ya sauya mata, wasu abubuwa yake yida suke sakata cikin rud'ani suna kulle mata kai, kamar ya san da faruwar komai? Kamar kuma yana hankalce da komai? To in hakane kenan me ye sunansu? Me suka aikata su? Me kuma zai aikata musu tunda ya san gaskiyar?
Haman kuma maganarshi a cikin tsoro ta antayashi, dan shi ma dai tunaninshi kenan, idan har ya sani wane mataki zai d'auka a kan shi? Me zai iya yi masa? A matsayinsa na wanda ya taimaka ana so a raina masa hankali, gashi shi kuma ko shirin bai gama sani ba, dan sai Umad na son wani abun ne kawai zai ce masa yi min kaza, amma har yanzu bai san dalilin zuwansu gidan nan ba da dalilin da yasa ya ce ya nemi auren Ayam, wacce a yanzu dai ya gama fahimta shirin shi na farko ba zaiyi tasiri na dan ita kanta Ayam d'in tsoronta yake ji, ama shiri na biyu na zai kasa aiwatarwa ba tunda ba shi kad'ai ke farautar wannan matakin ba.
A wajen Umad kuma kallon tsana ya bishi da shi da jin cewa lallai shi ya *kashe masa d'an uwa*, sannan a dalilin *mahaifiyar shi* ta fad'i sumammiya, wanda daga wannan ne suka rasa lafiyarta, sannan shi ne yayi dalilin mutuwar *mutumin* daya taimaka masa har ya samu masaniya akan inda zai samu Zafeera, haka kuma yanzun yake farautar rayuwar su Habbee dan ya kashesu, uwa uba kuma yake farautar masa mata, ita ma so yake ya hallakata.
Dan haka ba zai yiwu ba, tabbas ya zo gdan nan ne saboda Ayam, amma da niyyar ya k'ara samun wasu sirri da hujja da zasu nuna sarki Musail azzalumi ne sannan makashi, ba kuma zai bar nan ba har sai ya tabbatar an zartar masa da hukuncin da ya dace, ba zai tab'a bari burinshi da wahalarsa ta shekara da shekaru su tafi a banza ba.
Dalilinsa na shiga aikin hukumar sirri shi ne dan ya gano abinda ya faru a k'asar Egypt shekaru ashirin da shida, yana so ya san asalin abinda ya kawo wannan hatsaniyar, ya kuma samu da haka ya dinga bibiyar lamarin, hatta Ayam ya shiga rayuwarta ne a dalilin yayanshi.
Sai dai a kowane lokaci sarki Musail yana sake tabbatar masa shi mai laifi ne da baya son a tonaasa asirinsa, dan a lokacin daya gano wani muhimmin anfani da waziri Khatar zai masa, sai kawai d'azu ya ga gawarshi akan titi wanda Adah ya jefar, bayan ya bar wurin ne ya zo ya su a ya kuma tabbatar, dan haka yanzu makaminsa d'aya daya rage shi ne *Adah*.
Kowane sarki, kowane mai iko, kowane mai mulki yana da na hannun dama, kuma na hannun daman sarki Musail shi ne Adah, dan haka Adah ne harinsa na gaba kuma zai yi nasara wannan karan da yardar Allah.
Murd'a k'ofar da Ayam ta yi ta sa suka kalli k'ofar, da sauri Haman ya d'aga k'afarshi da niyyar k'arasawa ya kamata duba da yanda ta ke tafiyar sannu sannu tana ciccije fuska, saidai kafin ya d'ora k'afar a k'asa Umad ya sha gabanshi tare da nufa inda ta ke, ya na zuwa bai tsaya komai ba ya rik'o hannunta sannan ya fara takawa da ita a hankali.
Cak ta tsaya tana kiciniyar yakice hannunta, jin ya rik'eta sosai yasa ta sake k'ok'arin kubcewa tana fad'in "L芒che moi ma main (sake min hannu na)."
Kallonta yayi, duk da fuskarshi a had'e take kuma ranshi a b'ace, amma dai sai ya ji ba buk'atar ya had'e mata fuska yayin da zai mata magana, dan haka a sanyaye ya furta "Ko mu je ki taka da kanki, ko kuma na taka miki k'afafun, wane ki ke so?"
Kamar jiranshi take sai kuwa ta d'aga murya har da lik'e ido tsabar masifa tace "Ba na so d'in, na ce ba na so, dole ne malam? Sake ni zan tafi da kai na."
Sunkuyawa ya yi kamar zai gyara d'amarar takalminshi, kafin ta ankara sai ji tayi ya kwashi k'afafunta ya yi sama da ita, wutsil wutsil ta fara da k'afafun tana fad'in "Mahhh! Mah ki na gani fa? Ki masa magana mana ya sauke ni."
Saida ya kawota kan gadon ya dire sannan ya rik'e k'ugu yana kallon fuskarta, wata masifa da ya ga tana neman koya daga jiya zuwa yau, rigimar da take neman d'orawa kanta, jinjina kai ya yi ba tare da ya d'auke idonshi daga kan ta ba.
Juman da abun ya d'aure mata kai ta rasa me za ta yi tunani a kai, ga wanda ya zo maganar aurenta, amma kuma ga wanda ke matse mata waje, kallonsu kawai take kamar bak'in fuska a gabanta.