← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 86

Sashe 75

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin haka kamar wacce ta farfad'o daga doguwar suma ta bud'e idonta ta zabura, da k'arfi ta d'auke kanta dake had'e da na shi ta sake rik'o hannunshi daya gama shiga cikin rigarta yake rik'e da mamanta, da sauri ya bud'a idonshi shi ma ya sauke kan wuyanta tare da d'auke labb'anshi dake sumbatarta, a hankali ya fara shirin ciro hannun na shi amma kuma sai ya ji ta rik'e hannun na shi sosai, d'agowa yayi a hankali ya kalli fuskarta da idonshi da suka fara kad'awa yace "Hannu na malama."

Saida ta d'an wurga masa harara ta k'asan ido sannan ta turo baki kamar zata tsinkashi kafin ta sassauta rik'on data masa, wani murmushi ya saki a gefen labb'a sannan ya zaro hannu daga rigarta, gyara tsayuwarshi yayi ta hanyar d'an bata baya kad'an saboda asirinshi daya fara tonuwa, yana so yace mata "To tafi."

Amma kuma sai bakinshi ya masa nauyi ya kasa furtawa, dan haka kawai shi ya fara d'aga k'afarsa da d'an sauri ya bar gurin kamar wanda yayi k'aro da wani mugun gani.

*Bayan kwana hud'u*

Duka ranakun nan da suka gabata irin shagalin da aka gudanar shi ake sake maimaitawa, sai dai na yau ya fi na jiya bambamcin mutane da kuma k'ayatuwar wurin had'e da canja wata al'adar na gudanar da shagalin bikin amare.

Yau ma suna zaune kan wasu sababbin kujerun da aka kawata musu, inda Umad ya shirya cikin doguwar riga har k'asa da wandonta, saidai sak d'inkin irin na tubawa ne, inda rigar ke d'auke da kwalliya a gabanta har zuwa tsagar dake tsakiyarta, da kuma gefe gefe inda shi ma aka tsaga sai hula mai sunan dara bak'a wacce ta dace da kayan.

Saida ta duba ta ga kowa hankalin shi na kan abincin da aka cika gabanshi da shi sannan ta zura hannunta a hankali zata tsakuri cake d'in dake gabansu wanda ta ji yawunta sai tsinkewa suke saboda ganinshi, ta lak'ato zata kai bakinta ya rik'e hannun hakan yasa suka kalli juna, cikin rad'a tace masa "D'and'anawa fa zan yi, yawuna gudu suke."

Wani kallo ya mata mai kama da tsokana sannan ya jaye hannunta ya kai yatsun bakinshi ya lashe cake d'in na hannunta, lumshe ido yayi yace "Ummm! Ya yi dad'i gaskiya."

Bud'e ido yayi ya kalleta yana murmushi yace "Me yasa kika cika kwad'ayi ne wai? Kullum rigimata da ke bata wuce hanaki ciye ciyen nan ba."

K'ura masa ido tayi tana auna kalar rashin mutumcin da yake tata mata kwanakin nan, kullul cikin bibiyarta da tsokanarta yake, duk ya bi ya addabeta ya takurata, da gangan zai kai ta mak'ura idan ta bar wurin kuma ya bi bayanta ya mitseta son ranshi, dan jiya ma har zip d'in rigarta ya cire yana k'ok'arin kai bakinshi a inda bata so ya kuma kai wa na biyu ta raba kanta da shi, dan haka yau ba zata tashi ba kuma ba zata yarda ya kai ta mak'urar ba ma.

Jaye hannunta tayi daga na shi ta kawar da kanta kawai, murmushi ya mata shi ma ya d'auke kan na shi, yanda yake matseta a bango yana masa dad'i musamman idan ranta ya b'ace ta fara masa wani yaren da bai sani ba, hakan na masa dad'i matuk'a idan ta juyar da harshenta, dan dama tana canza yare ne idan ranta ya b'ace ko ta shiga halin d'imuwa ko kuma mamaki, yanzun abinda ya fahimta game da ita shi ne babu kalar yaren da baya zuwa mata, sai ta furta abinda zuciyarta ta raya mata sai kuma ta koma wulwula ido tana so ta ji wai me ta fad'a ma.

Babu abinda ya fi birgeshi kamar idan ya titseyeta ya tambayeta me ta ce? Sai ta gyara kalamanta ta fad'a masa wata fassarar daban cike da girmamawa.

Cikin ma'aikatan dake raba abinci ne wani ya zo wucewa da faranti a hannunshi, d'aga masa hannu tayi ya k'araso a ladabce tare da gaisheta yana sunkuyawa, hannu ta kai zata d'auki farantin dake d'auke da wani d'an gassashen nama da parsil an masa ado da shi.

Da sauri Umad yace "A'a, me ki ke yi haka?"

Kallonshi tayi ranta na neman harzuk'a tace "Yunwa fa nake ji, sai na mutu ne."

Kallon ma'aikacin yayi yace "Je ka."

Da sauri ya bar wurin dan dukansu kowa d'an sarki ne, babu wanda zai bashi umarni ya kasa bi, tana ganin haka ta sake juyowa ta kalleshi, cike da tausar kanta na wani haushi haushi da take ji wanda da ba haka take ba cikin harshen Arabic tace "Wallahi idan ka cika damu na yanka ka zan yi, haba."

Mik'ewa tayi da sauri ta sauka daga kan damdamalin ta nufi hanyar madafa, saida ya ga shigewarta ciki sannan ya saci kallon mutanen wurin ya mik'e shi ma ya bi bayanta.

Haman da komai ke faruwa kan idonshi wani guntun tsaki ya ja sannan ya kawar da kan shi cike da k'una da takaicin kasancewar Umad ne mijin Ayam ba shi ba, asara goma da casa'in ce ta same shi, ba ga mulkin ba haka kuma ba ga Ayam d'in ba, shiyasa har yanzu k'udirinshi bai canza ba na burin mallakarta, kuma ko yanzu ya samu dama zai yi yanda zai sameta, tunda dukansu babu wanda ya fahicme shi bare a agaza masa, dan haka inhar ya samu damar aiwatar da wani abun to zai yi.

*Ayam* na shiga madafar suka sha kicib'is da Zafreen ta fito tana b'oye abu a bayanta, kallon tsaf Ayam a mata take kuma ta fahimci bata d gaskiya, girgiza kai tayi irin ko a jikina sannan ta rab'ata ta wuce, dan tunda abun nan ya faru ko sannu bata had'asu, mamaki ma Ayam take abinda ya zaunar da Zafreen d'in, dan ita gani take da ita ce da ta koma gaban mahaifiyarta, duk da nan ne ya dace ta zauna wato gidan mahaifinta.

Da sauri Zafreen ta k'arasa fita tana b'oye kwalbar gubar dake hannunta wacce ta so zubawa a abinci kowa ma ya ci ya mutu, amma sai ta ji ana shigowa ashe kuma babbar mak'iyarta ce, tana daf da kai wa k'ofar suka had'u da Umad.

Babban abinda ya b'ata mata rai ko ya ke had'ata da shi bai wuce yanda yake shareta d'in nan ba, saika rantse d Allah idan ya ganta to makaho ma zai ganta, sam yi yake kamar bai ga mutum ba ta yanda zai iya shiga ta jikinta ma ya wuce tsabar sharewa, k'wafa kawai tayi tana ayyana komai ya kusa zuwa k'arshe, saidai dukkanmu mu rasaka Umad.

K'arasa shiga yayi kamar dai bai ganta ba, kuma ya ganta kawai baya son raini ne bare ta kawo masa wargi, k'arasawa yayi kusan Ayam daya samu tana yanka gasashen bredi mai rid'i, jingina yayi kan dask d'in da ta aje ketch up da mayonnaise yana kallonta yace "Me zakiyi haka?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Ci zan yi, yunwa nake ji sosai, kuma na rasa dalilin da yasa kake hanani cika cikana."

Murmusawa yayi yace "Ni ba hanaki nake ba, kawai dai ina kishin na ga kina tauna abu ne da bakin nan na ki a gaban wasu mazan."

Kallonshi tayi tace "Amma kai za ka iya cin komai kenan a gaban wasu matan?"

Da sauri shi ma ya kalleta yana hango wani abu a k'wayar idonta, sake murmushi yayi ya d'auke kanshi yace "Idan kina so sai na daina."

Murgud'a baki tayi tare da yanka bredin a tsakuyarshi, ajewa tayi kan pate sannan ta d'auki kecth up da mayonnaise d'in nan ta had'ase wuri d'aya ta motse, duk yana kallonta hannayenshi hard'e a k'irji yace "Yaushe ne wai zamu tare gidanmu?"

Ba tare data kulashi ba tace "Randa kake so mana yallab'ai."

A take yace "Gobe ya min, gobe, kin shirya?"

D'an kallonshi tayi na dak'ik'u sannan tace "Ba damuwa, ai dai ka shirya ko?"

Jinjina kai yayi tare da kallonta yace "Ina so na baki mamaki zuwan goben, ki shirya da kyau."

Kallonshi tayi sanda take shafa had'in nan a cikin bredi tace "Bayan wanda ka bani?"

Sai kuma ta girgiza kai ta ci gaba da abinda take, sauke hannayenshi yayi ya matso kusanta ya zura hannunshi ta k'ugunta ya zagayo da shi, kwance yayi a gadon bayanta ya d'ora hab'arshi a kafad'arta yace "Wannan ai na musamman ne."

Dakatawa tayi da abinda take tace "Yallab'ai wai me yasa ka zama wani iri ne? Dan Allah ka dinga jin kunya ka ji."

Da k'arfi ya juyowata gabanshi hakan yasa ta shiga wuk'il wuk'il da ido saboda yanda ya juyota kamar b'era a kwano, had'ata yayi da teburin dake bayanta suna kallon juna yace" Bana da kunya kike nufi?"

Da sauri ta girgiza kai tace" A'a ba haka nake nufi ba fa."

Sake matseta yayi sosai yana matsa kanshi sosai kusanta kamar zai had'e bakinsu, baya ta dinga jan kanta tare da saka bredin nan a tsakiyarsu tace" Please yallab'ai, yunwa nake ji fa."

K'ura mata ido yayi yace" Kwanan nan kin cika son ci dayawa ko?"

Galala ta kalleshi tace" Amma ai da ba haka nake ba ko?"

Da alamar tuhuma yace" To me ya kawo haka yanzun?"

Sinne kanta tayi tace" To ai ni ban saba da zama wuri d'aya bane, nan kuma kullum zaune nake ban aikin komai, gashi da na ce zan motsa jiki sai Mah ta hana ta ce wai ni mace ce ba zan dinga bud'e jikina ba."

Tuunda ta fara magana yake k'are mata kallo kamar yana neman wani abu a jikinta, saida ta dasa aya ya kalli idonta yace"...

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:45 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*44*

Saida ta dasa aya ya kalli idonta yace "Wani abu ne ya ke damunki to?"

Kyab'e baki tayi a sanyaye tace "Ni ma ban sani ba."

Jinjina kai yayi ya d'an ja baya kad'an yace "To ci."
Chapter 75 · 0% Book details