Sashe 65
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Umad* ma na idar da sallah wayarshi k'arama ya rik'e ga hannu yana kallo, tunane tunane kala daban daban ne suka ziyartarshi a lokacin, yana so ya kira wayar tangarahon dake falo da kowane d'aki dan yayi magana da Mah d'inshi, jiya ta kasheshi da al'ajabi kafin bacci ya d'auke shi, sanda aka kirashi ya ga sarki Wudar ne, amma yana d'agawa ya ji muryar da tun yana shekara shida rabonshi da ita, saida ya jiri ya jefashi kan gado ya fita a hayyacinshi, sai ga shi yana zubar da hawaye abinda ya jima bai yi ba, ita kuma shi kuka aka rasa mai rarrashin wani.
Da k'yar Kossam ta rarrashe shi sannan ta tambaye shi inda yake, k'in fad'a mata yayi da fari sai dai kawai ya tabbatar mata yana lafiya, saida ta yi ikrarin zata nemeshi sannan ta je inda ya ke kad'ai ya fad'a mata yana Khazira, abinda ta fad'a masa a lokacin ta kuma kashe waya shi ne yasa shi shiga wani yanayi na daban, sai ya rasame zai yi a lokacin, gashi daya maida kira sai aka k'i d'agawa har ta tsinke.
Yana so ya ji da gaske mahaifiyarshi zata iya aikata abinda ta fad'a cewa " *To ni ma zan zo Khazira gobe da safe, za mu had'u da kai sannan mu je masarautar Musail, zan nema ma ka auren 'yarsa Zafeera yarinyar da ta kula da ni, kuma a dalilinta na samu sauk'i yau, na gani a mafarki na Umad, aurenka da ita alkairi ne.*"
Abinda ta fad'a kenan ta kashe wayar, ganin tunanin ba zai gyarashi sai ya kai hannunshi zai aika kiran, jin jiniyar motocin jami'an tsaro da ya yi yasa ya mik'e daga kan sallayar ya soka wayar aljihun wandonshi ya fita a d'akin da sauri.
Yana k'arasowa falon daidai da zuwan Haman, haka ma sarki Musail ya zauna kan kujera haka ma sipetan yan sandan, su Ayam ma suna sallame sallarsu suka gyara zama, kan kujera Juman ta zauna amma Ayam sai ta gyara zama a k'asa.
Jami'in ne ya kallesu a harshen slovaque yace "Ina tayaku jimami sarauniyata."
D'an lumshe ido tayi ta gyad'a kai alamar ta amsa, d'orawa yayi da fad'a musu sunanshi da kuma aikinshi sannan ya ci gaba da fad'in "Me zaku iya cewa game da wannan abun da ya faru?"
A tare kuma a sanyaye suka girgiza kai alamar ba komai, gyara zamanshi yayi dan su fahimce shi da kyau yace "Am sarauniyata, ina nufin..."
D'aga masa hannu Musail yayi fuskarsa a had'e yace "Jami'i, ka dakatar da tambayoyinka har sanda mai laifin ya k'araso, su basu san komai ba game da abinda ya faru."
A ladabce jami'in ya kalleshi yace "Ranka shi dad'e, muna so mu tattara bayanan da zamu samu wata makama ne, bincike muke so mu yi game da al'amarin nan, duba da cikin maharan duka dakarun masarauta sun kashesu, guda biyu ne muka samu a raye kuma mugun rauni ne a jikinsu, wanda kafin mu iya ji daga bakinsu zai d'aukemu kwana uku."
Shirun da Musail yayi ya tabbatarwa jami'in ya yarje masa kenan ya ci gaba, sake gyara zamanshi yayi cikin kujerar ya juya ya kalli wata jami'a dake sanye da kayan aikinta hannunta rik'e da alk'alami da takarda yace" Ki d'auki duka bayanansu."
Jinjina kai tayi tare da kafa alk'alaminta akan takardar tana kallon Juman da Ayam, a tsanake ya fara tambayarsu inda kowace tambaya da wacce ke amsa mi shi ita.
Umad na ganin haka ya nufi d'akin Zafreen, yana tura k'ofar ya shiga babu kowa a d'akin sai hasken fitila, d'akin shiru kuma a gyara tsaf babu wani abu da ya same shi, da hanzari ya nufi wajen drowerta ya bud'e, bincikawa ya fara yi yana d'add'aga kayan yana dubawa ko zai samu wata makamar.
A k'ank'anin lokaci ya hautsina d'akin da bincikenshi, har k'ark'ashin gado saida ya lek'a amma babu abinda ya samu, mik'ewa yayi ya rik'e k'ugu yana kallon d'akin, tsaki yayi zai fita na jin haushin bai samu komai ba, har zai fita sai kawai wani abu ya zo masa a rai, lokacin daya taka kujerar dake gaban madubi ya lek'a sama, daya sauko ya manta ya rik'e drower sosai ta yanda indai aje ne take to tabbas za ta motsa, amma sai ya tuna batayi motsi ba alamar a kafe take.
Da sauri ya dawo tare da dubawa, sai kuma hasashenshi ya bashi daidai, komawa yayo b'angaren shi na hagu ya tura kwabar zuwa dama, jin bata motsa ba yasa ya koma b'angaren dama ya tura zuwa hagu, sai gashi kamar k'ofa mai taya drower ta motsa k'ofa kuma ta bayyana.
Murd'a k'ofar yayi ya shiga d'akin mai duhu, wayarshi ya ciro ya kunna fitila da taimakonta ya kunne hasken wurin, hanya ce doguwa da zata kai ka har zuwa fita a bayan garin, wanda kowane d'aki na sarki da iyalansa akwai hakan.
A hankali ya fara takawa da san tabbatar tana ta fita ko kuma ta k'ofar gida, ya taka d'aya biyu kenan ya ji k'afarshi ta taka wani wuri kamar dai wanda ya rizga, cak ya tsaya ya maida dubansa k'asa d'aga k'afarsa yayi yana sake kallon wurin da aka d'an rufe da babban carpet, jaye carpet d'in yayi sai gashi tilles d'in da aka jera a wurin d'aya an d'orashi ne kawai.
Yana d'aga tilles d'in fari mai fad'i sai ga takardu sun bayyana da k'aramar wayar salula.
D'aukar takardun yayi ya fara dubawa, abinda ke ciki y so zautar da tunaninshi, dan haka yayi gaggawar maidawa ya aje sannan ya fito daga d'akin ba tare daya gyara komai a yanda yake ba.
Yana zuwa falon ya samesu yanda ya barsu, saidai a yanzun Dhurani na tsaye kan k'afafunshi yana fuskantar Musail, sai kuma Adah na bayan Musail d'in a tsaye, jiki a sab'ule ya k'arasa ya zauna kusa da Juman inda Haman ya ke, muryar Musail ya ji yana fad'in "Nagode jami'i, zaku iya tafiya."
Jinjina kai jami'in yayi ya mik'e tare da juyawa suka fita, suna fita Zafreen na bud'o k'ofar d'akinta ta fito rai b'ace, ta fito ne da niyyar yin rashin mutunci ta ji wa ya shigar mata d'aki, dan ta wannan k'ofarf sirrin ta fita sannan ta dawo ta nan, amma ganinsu zaune babu mai magana yasa ta ja tsaki.
Tsakin da tayi shi ya dawo da hankalinsu kan ta har suka d'aga kai suka kalleta, ta juya zata koma Musail yace "Zo nan."
Tsayawa tayi amma kuma bata juyo ba, a tsawace abinda bai tab'a mata ba yace "Na ce ki zo nan."
Sakin k'ofar tayi ta turo baki ta shiga takowa da takalminta k'afa ciki, saida ta zo tsakiya ta tsaya tana yatsina fuska tace "Ga ni, me ye?"
A hankali Juman ta kalleta wacce tayi lak'was ta sare da lamarin Musail tace "Zafreen, mahaifinki ne fa, haka ya dace ki amsa masa kiran da ya miki?"
Juyowa tayi ta kalleta a wulak'ance tace "Ban saka da ke ba, ki bari na ji me zai fad'a min mana."
Rai b'ace Ayam dake zaune k'asan carpet ta mik'e tace "Ke Zafreen, ya kamata kisane zai dinga fitowa daga bakinki, wannan iyayenmu ne, idan ke ba zaki girmama su ba to kar ki raina su a gabana."
A hassale kamar dama jira take ta matso kusan Ayam tana fad'in "Me za ki yi? Idan na musu rashin kunyar me za ki yi?"
A hassale ita ma tace "Zan yi abinda ba ki yi tsammani ba ne, kuma ki jaraba ki gani."
Waina idonta tayi ta ja tsaki tace "Ohh! Wai ni ban san ya aka yi kuka kub'uta ba, sai yaushe ne wai?"
Da mamaki Musail yace "Sai yaushe me?"
Daga zaune ba tare daya d'aga kai ya kalli kowa ba yace "Sai yaushe ne wai za ku mutu?"
Da sauri duk suka kalleshi sai Juman data dafe k'irji tace "Me?"
Sannan ya d'aga kan shi ya kalleta yace "Abinda take nufi kenan, sai yaushe ne za ku mutu ta gaji masarautar nan, ita da kuma *mahaifiyarta*."
Ido Juman ta zaro haka ma Musail, Adah da kuma Haman da Ayam, da sauri Musail ya mik'e tsaye yana kuma zazzaro ido yace "Me ka ke fad'a ne haka? Kan ka d'aya kuwa?"
Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek'e cikin isa da k'asaita yace "...
*Domin samun lu'u lu'u ko badak'ala tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52*
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LU'U LU'U*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*38*
Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek'e cikin isa da k'asaita yace "Ina nufin mahaifiyarta, yallab'ai duk abinda ya faru jiya zuwa yau, yarinyar nan ce Zafreen, kuma ta yi hakane da taimakon wasu da suke da burin ganin bayanka, daga ciki akwai Bukhatir, wannan malamin da kuma tsohuwar hadimarka *Nanna*."
Juman dake tsaye kallonshi tayi da mamaki amma kuma ta kasa cewa komai, cikin jin haushi Zafreen ta matso kusan Umad ta nuna shi da yatsa tace" Dama kai ne ka shiga d'akina ka min bincike? Akan wane dalili? Baka da wannan damar malam."
Galala ya kalleta tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace" Ba yau na ke bincike a kan ki Zafreen, tunda na fara aiki na ke bincike akan duk wani dake zagaye da Ayam, sannan na kan dasa ayar tambaya akan duk wani dake da kusanci da ita, na nesa ko na kusa, musamman ma ke da kika sake tabbatar min da zargina ta hanyar shiga makarantar da ta ke."
Kamar wacce kanta zai yi bindiga Juman ta dafe kai ta kalli Musail tace" Ban fahimci komai ba, Zafreen dama ba 'yata ba ce?"
Wuru wuru ya fara yi da ido yana sinne kai k'asa, a gadarance Umad ya kalleta yace" Sarauniya dan Allah zauna, ni zan fad'a miki komai, dan na gaji da wannan nuk'u nuk'un."