← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 86

Sashe 7

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rad'a Ayam tace "Yanzu ku d'an aikin nan ne zai gagaremu? Kun manta irin tijarar da muka zuba a baya ne?"

Deeyam ce tace "Bamu manta ba, amma dai yau kam ni dai babu ruwana, inda matsalar take shine rashin sanin waye malamin, ni bansan me yasa kika damu da son sanin wane iri ne shi."

Gyara tsayuwa Ayam tayi da kyau ta kallesu tace "Ku fad'a min zaku shiga ko a'a?"

"A'a." Sabrine ta fad'a tana juya baya, jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni zan shiga ciki, amma ku jirani a nan."

Murmushi Deeyam tayi tace "Fatan nasara."

Harara Ayam ta jefa mata tana gyara hularta tace "Matsalarku ce."

Kallon k'ofar d'akin tayi tana sauke numfashi, wani yanayi na tsoro da fad'uwar gaba take ji wanda bata tab'a ji ba, hatta da jinin jikinta ji take ya k'ara gudun tafiyarshi.

Cije leb'enta tayi na k'asa sannan ta kai hannu ta k'wank'wasa k'ofar d'akin, amma sai ta ji shiru babu ko alamar motsi, sake kwank'wasawa tayi nan ma shiru, a karo na uku ta sake kwank'wasawa tana jan gajeran tsaki.

Deeyam ce tace "Ayam, tunda kika ji shiru ki zo mu je kawai, watak'ila baya nan."

Sabrine ce ta karb'e da fad'in "Ko kuma ma bai zo ba."

Juyowa tayi ta kalli Sabrine da tayi maganar tace "Hakane?"

D'aga mata gira tayi alamar e, jinjina kai tayi tace "Bari mu gani to."

Cikin sand'a ta kama hannun k'ofar ta murd'a a hankali, jin ta bud'e yasa suka kalli juna, maida kallonta tayi ga k'ofar ta tura a hankali tana shiga cikin d'akin.

Tattausan k'amshin turaren 112 ne ya fara mata maraba, sai kuma siririn hasken daya gauraye d'akin, komai na d'akin a gyare kuma a killace yake sannan a tsaftace, babu alamun da suka nuna akwai mutum a d'akin, hakan yasa ta bayan k'arewa d'akin kallo ta jawo k'ofar da niyyar rufewa.

Cak! Ta dakata sakamakon tsikayar wani k'aramin hoto a gefen gadon ajiye, sakin hannun k'ofar tayi ta k'arasa da sauri ta d'auki hoton, k'urawa dattijuwar matar ido tayi mai cikar kamala da haiba, tana cikin shiga ta alfarma kamar wata sarauniya. Samun kanta tayi da sakin murmushi sanadiyar k'aunar matar data ji, a hankali a asalin harshenta na slovaque tace "Watak'ila ya manta da hoton ne?"

Sai kuma ta tambayi kan ta "To amma wa ya zauna a d'akin?"

Rashin sanin amsar yasa kawai ta d'aga kafad'a alamar ko oho, juyawa tayi ta fara tafiya hannunta rik'e da hoton.

Tana daf da hita aka bud'e k'ofar k'aramar ban d'akin dake cikin d'akin, da sauri kuma a mugun tsorace ta kalli inda ta ji k'arar, a wani bala'in tsoracen wanda bata san sanda ya ziyarceta ba ta saki hoton wanda ke lullub'e da kwalba ya fad'i k'asa.

K'arar glass d'in da kuma ihunta a tare suka gudana, sai kuma tayi saurin yin gum da bakinta kamar wacce aka tusawa k'wallon goriba a bakin.

Idonta masu abun al'ajabi ta zuba masa tana kallo ba tare da rusunawa ko jin d'ar a yanda ta ganshi ba, a hankali take yi tana k'yabta idonta tana kuma sauke numfashi kamar wacce aka b'atawa rai, a zahirinta kamar jira take yace kul tace cas, amma a bad'ini kuma gabanta ci gaba yake da fad'uwa, ganinshi d'aure da towel d'in nan kalar shud'i ba k'aramin gigita mata lissafi yayi ba, dogo ne sosai mai k'ira da zubin jarumai, duk da ba wata murd'add'iyar sura ce da shi mai jan hankali ba, amma dai yana da fasali mai kyau wanda zai iya juyar da k'irarshi a duk ta yanda ya so.

Duk da bak'i ne amma kuma bak'inshi mai kyau ne da k'yalli kamar na macen dake samun gyara a kai a kai.

A hankali cikin b'acin rai da mamakin abinda ya kawota d'akinshi ya tsura mata ido, yana d'ora ido 脿 kan ta saida launin idonshi suka canza tsabar haushi da takaici, sai yake bala'in jin kamar ya k'urma ihu dan ya samu sassaucin abinda ya tokare masa zuciya.

Ba ma wannan ba, wai a kan wane dalili ne shi kam yake had'uwa da wannan mai zubin aljanun ruwan, ga ta dai 脿 cikin kayan bacci wando iya gwiwa da riga mai k'ananan hannu, gaba d'ayanta fa ba zata gagareshi ya dunk'uleta a hannu d'aya ya jefata a hudar hancinshi sannan ya fyatota.

Kallon hoton dake k'asa yayi, da sauri ya tako ya tsaya gabanta tare da durk'usawa yana kallon hoton, a mugun fusace ganin yanda hton ya fashe ya sa ya d'ago ya k'ura mata ido.

Ayam da tunda ya fara takowar nan da sauri gabanta ya shiga dakan uku, kasa motsawa tayi sai bakinta data warwareshi daga kumburewar da ta mishi, hannayenta ta d'ora kan mararta ta dafe tana fatan kar fitsari ya taho mata.

Umad kam cikin fitar hayyaci ya d'aga hannunshi ya wanketa da mari, a k'ufule ba tare daya bata damar gama fahimtar rad'ad'in ba ya nuna mata k'ofa da yatsa cikin hard'add'iya kuma nagartacciyar muryarshi da harshenshi da ya fi k'warewa a yaren Gallois yace "Fita a nan, kuma karki bari mu sake had'uwa, *b'arauniya* kawai."

Da sauri ta d'aga idonta dake kallon k'asa ta kalleshi jin sunan daya bata. Shi ma sai lokacin ya fahimci wani abu a tare da ita, ya mareta marin da yake da tabbacin ya ratsata sosai, to amma" Me yasa bata yi ihu ba? Kuma bata fad'i ba duk da rashin nauyinta." Abinda ya tambayi kanshi kenan, sam kamar ma ba ita ya mara ba a fuska.

A gaggauce ya kawar da tunanin ya maida hankalinshi ga Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "...

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:31 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._

_Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._

_Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._

Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299*
Amina Maikudi Abdullahi
First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba
080-38-85-69-44.

_Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._

_Bismillahir rahamanir rahim_

*5*

Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "Af Allan, ond byddwch yn mynd ar ol ar fy ol (zan fita, amma ka koreni a mutumce)."

Baisan sanda mamaki ya sake bayyana a fuskarshi ba, gyara tsayuwa yayi da kyau dan ya Fahim I shekarar da zaiyi kisan kan shi ce ta kama, nuna ta ya sake yi a dake yace" Ke, ke mahaukaciyar ina ce?"

Ba tare data rusuna idonta ba ta sake muskutawa ita m'a sannan tace" Sanin mahaukaciyar ina ce ni ba zai anfaneka da komai ba, kawai ka janye kalmar nan ta b'arauniya daka fad'a min."

Hannayenshi bibbiyu ya rabka a k'ugunshi ya dafe jajayen idonshi a kan ta, ba alamar wasa a tare dashi yace" Ke 'yar garin nan ce?"

K'urawa fuskarsa ido tayi ba tace komai ba, ganin bata da niyyar magana sa茂 ranshi ya sake b'aci, a harzuk'e ya cabki hannunta da nufin fitar da ita, da k'arfi ta fincike hannunta tana mai kallon inda ya rik'e, wani abu ta ji kamar wutar lantarki tana janta.

Kallonta ya shiga yi shi ma da tunanin ko dai abinda ya ji ita ma ta ji? Tsaki ya buga kawai ya juya ya sake shigewa ban d'akin zuciyarshi kamar zata fashe.

Ayam ma na ganin haka ta ja k'afarta data mata nauyi ta fita ita ma, a bakin k'ofar ta samu su Deeyam suna jiranta, da zumud'i Sabrine tace "Ya dai? Me ya faru 脿 ciki?"

Shiru tayi sa茂 sauka a matakalar data shiga yi, Deeyam ce tace "Ya muka ji kinyi ihu? Ko dai d'an hannu ne shi ma?"

Babu wacce ta amsa ma har suka koma ta inda suka fito suka koma d'akinsu suka kwanta, amma Ayam sai tayi zaune akan gado ta zabga tagumi tana sake kallon wuyan hannunta daya rik'e.

*A* wajen Umad ma saida ya ji an rufe d'akin ya fito, wajen hoton ya k'arasa ya durk'usa ya shiga tattare glass d'in, a kwandon shara ya zuba sannan ya d'auki hoton yana kallo, cikin yarenshi yace " *Majka* (uwata), kiyi hak'uri ba laifina bane, waccen mahaukaciyar ce da ban san me ta zo nema ba."

Ba tare daya saka kaya a jikinshi ba shi ma ya zauna kan gadon yana ta kallon hoton nan, so yake yayita zazzaga masifa ko ya ji sauk'i, amma dake mutum ne ba mai hayaniya ba sa茂 kawai yake ta tsaki shi kad'ai.

Sai dai ya k'agu gari ya waye ya bincika ya ji wacece wai ita d'in? Da wannan tunanin har bacci ya d'aukeshi bayan ya tofe jikinshi da addu'o'in tsari.

*Washe gari*
Chapter 7 · 0% Book details