← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 86

Sashe 37

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu da Ayam ta lura da shi shi ne d'anta Umad da ido take amsa mishi magana sab'anin ita, da ido ta ga ta amsa mi shi alamar e, murmushi ya saki ya jinjina kai sannan ya juya ya kalli Ayam a sanyaye yace "Nagode da kulawarki a kan mahaifiyata."

Girgiza kai tayi tace "Kamar mahaifiyata take ni ma, nauyi ne a kai na."

Kallon da suka bita da shi yasa ta jin ta tsargu, musamman ma sarauniya Kossam da ko k'yabtawa ba tayi, hakan yasa ta d'an rusuna tace "Zan barku, idan zaka tafi ka kirani sai na mayar da ita ciki."

Da sauri ta shige b'angaren nan tana jin gabanta na bugawa haka kawai, b'angare d'aya kuma zuciyarta na son kulawa da matar.

Tana b'ace ma ganinsu sarauniya Kossam ta kalleshi tana murmushi, da ido ta masa alamar" Yarinyar."

Sannan ta d'aga yatsunta biyu da k'yar a mugun wahalce tayi alamar" Kirki." Ma'ana" Yarinyar kirki ce."

Sannan ta nunashi da yatsa ta kuma nuna hanyar da Ayam ta bi sannan ta nuna yatsarta mai d'auke da zobenta na aure.

Wani irin k'walalo ido Umad yayi ya k'ura mata, a d'an rud'e yace" Mah! Kina nufin fa...?"

Sai kuma ya girgiza kai yana d'an k'ank'ance idonshi, nufinta fa ya *aureta*, ya auri Ayam take nufi? To ta ya zai fara fad'a mata ya aureta dan ya kareta? A ladabce ya mik'e tsaye ya koma bayanta kawai ya kama hannayen keken kujerar ya dinga turata zuwa ciki ba tare da yace komai ba, dan kai tsaye ba zai ce komai ba har sai ya ga abinda Allah ya yi.

*01:20*

Juye juye take a cikin baccinta tana mai fatan ta farka daga mafarkin da take na matar dake ta mata magiyar ta taimaketa, kamar daga sama ta ji an daddab'ata, a zabure ta farka tana zuba idonta akan wanda ke gabanta, ba dan fuskarshi a bud'e take ba da ba zata ganeshi ba, da mamaki tace "Yalab'ai, kai ne yanzu?"

D'ora yatsa yayi a labb'anshi yace "Shiiiii!"

Jefa mata kayan hannunshi yayi yace "Saka wannan muje."

Da kallo ta bishi ganin ya nufi taga madadin k'ofa, zura k'afafu yayi alamar dai dirawa zai yi ta nan kuma ta nan d'in ya shigo, da sauri ta sauka daga kan gadon ta warware kayan, cikin dubara ta saka ba tare da d'ar d'ar ba dan ya juya mata baya ne, tana sakawa ta kalli kanta ta madubi, sak shigarshi da ta ta iri d'aya ce, bak'ak'en kaya na sanyi masu hula da bak'ak'en takalmi, matsawa tayi kusa da shi tace "Na shirya."

Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ne ya kubce mi shi ganin kayan na shi sun mata yawa amla kuma sun mata kyau, tana kallo ya sauka daga tagar amma bata ji alamar an dira ba, hannu ya zuro mata ta mik'a masa ta haura ita ma, saida ta lek'a ne ta fahimci ashe tsani ya d'ora a wurin, takawa sukayi har suka sauka tana nan kafin suka shiga ta shukoki suna sand'a har suka isa bakin babbar k'ofa.

*Ki hanzarta ki biya na ki idan baki biya ba, domin samun na ki tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52*

_Masu buk'atar ci gaban *BADAK'ALA* ku aje hankalinku, tabbs akwai labari kuma shi ma da gaske ya faru, saidai ina so ne na ga adadin mabiya *lu'u lu'u* dan bana so na rikita kai na sannan na shiga hakk'in wanda suka biya kud'insu._

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*21*

Mai gadin dama yana d'akinshi, dan haka suka lallab'a inda Umad ya bud'e k'ofar suka fita a gidan, wani kyakyawan babur suka tarar a k'ofar, cikin salo da k'warewa Umad ya hau tare da saka hular kwano sannan ya mik'o mata ita ma, karb'a tayi ta saka kafin ta hau suka d'auki hanya.

A k'alla tafiyar minti talatin suka samu inda Umad kuma ya dakata a wata garage dake rufe, tana tsaye tana kallo ya bud'e k'ofar ya fito da mota k'irar benz bak'a wulik, saida ya koma ya rufe garage d'in sannan ta shiga suka kuma d'aukar hanya, awa d'aya suka share a motar nan suka isa wani k'arami kuma k'ayataccen gidan da ba zaka tab'a tsammanin wani daya tara kud'i sama da pan ko euro ko kuma dolar milyan biyar ba, dan k'arami ne sosai daidai da k'aramin ma'aikacin da buk'atar gida ba zata gaza samunsa ba.

Saidai a cikin gidan tsofaffi biyun ke rayuwa ko d'an aike babu, tsofaffi biyun sukan ware lokaci zuwa lokaci dan su keb'e kansu su samu lokacin farin ciki a tsakaninsu da kuma walwala ba tare da d'awainiyar al'umma ba, dan sarautar k'asar Egypt ba k'aramar sarauta ba ce kamar kowace, hatta da tsarin tafiyar da mulkin daban yake da na kowace masarauta kamar yanda tsarin shigarsu da yarensu yake daban.

Sau d'aya Umad ya buga k'ofar suka gane waye a k'ofa, tsohon ne ya k'araso cike da dattako da haiba ya bud'e, murmushi ne ya bayyana a fuskarshi sanda suka had'a ido da Umad, kaucewa yayi a hanyar alamar ya wuce sai ya rufe k'ofa, da fara'a Umad da kuma girmamawa yace "Barka."

Kamar dai kowane sarki ko jinin sarauta shi ma da ido ya amsa mi shi tare da d'an murmushin gefen labb'a, kallon fuskarshi Umad ya sake yi yace "Ba ni kad'ai bane, na zo muku da wata kyauta ne ta musamman."

Idonshi kawai ya d'aga zuwa bayan Umad d'in dan ganin menene, a hankali Umad ya rab'a gefe dan ya bashi damar ganin wacce ke bayanshi.

Suna had'a ido wani yanayi na musamman ya ziyarcesu a tare, sanyayye kuma k'akk'arfan fad'uwar gaba suka samu a tare, sai dai kuma wata irin alak'a mai k'arfin gaske da suka ji ta k'ullu a tsakaninsu lokaci d'aya.

Ayam kasa d'auke idonta tayi ta saki baki tana kallon tsohon kamar zatayi magana, sai take jin kamar fuskarshi ta mata kama da fuskar matar da take gani a mafarkinta, dan a duk sanda tayi mafarkin matar tana tashi ta kan kasa hasasho yanayin fuskarta, amma yanzu tana ganin tsohon saita ji kamar fuskar ce.

Daga can k'asar zuciyarta take jin wata narkakkiyar k'aunar tsohon da bata tab'a jin tana ma wani mahaluki a duniya ba, hakan yasa ta alak'anta ko ma menene a tsakaninsu to tabbas alak'ar mai k'arfi ce wacce ta isa ta sa su gauraya su zama dunk'ulallen abu.

A hankali ta tako ta shigo d'akin idonta akan na tsohon nan, yanda shi ma yake kallonta zai tabbatar maka abu iri d'aya suke ji a jikinsu da zuk'atansu, wasu k'walla ta gani a idon tsohon sun taru suna neman zubowa, cikin wata irin muryar kuka mai tattare da shauk'i tsohon nan ya bud'i bakinshi yace "Idan har abinda nake ji a yanzu gaskiya ne, hakan na nufin yau ni ne a gaban jikanyata? 'yar da' yata ta haifa?"

Ayam kam tuni k'walla suka zubo mata suka shiga wanke mata fuska wanda ita kanta bata san dalili ba tace "Ban san asalin me nake ji ba sanda na gan ka, amma dai ina jin daban a kan ka, waye kai ? Me ye alak'ata da gidan nan? Me yasa nake jin haka dana ganka?"

Wani lafiyayyan murmushi ya saki ya kamo hannayenta duka biyun zuwa ciki, bin shi ta dinga yi har saida suka shiga tsakiyar falon, dan yanayin ginin gidan sak irin zubin k'irar yan Turkey aka mi shi, tsohuwar data samu zaune a kan kujera ta kwanta baya sosai jikinta lullub'e da tattausan bargo ne ya nemi haukatata.

Sak fuskarta take gani a tsohuwar, abu kawai daya banbanta su shi ne ita yarinya ce ita kuma tsohuwa, ita ma mik'ewa tayi da sauri tana sake k'urawa fuskarta ido, irin dai abunda suka ji a farko haka yanzu ma suka ji, da sauri ta k'araso tana kallon mai gidan na ta tace "Habibi, kamar akwai wani abu tsakaninmu da wannan ko?"

Jinjina mata kai yayi sannan ya juya ya kalli Umad dake bayansu a tsaye, a hankali tsohuwar ta kai hannunta wuyan Ayam ta kama sark'ar nan tana kallo, fashewa tayi da kuka ba tare data saki sark'ar ba tace" Wannan sark'ar ba zan manta ranar da waccen azzulumin ya sakawa 'yarmu ita a wuya ba bayan ya mana barazana da rayukanmu."

Da k'arfi ta jawo Ayam suka rumgume juna tsam, Ayam da bata gama fahimtar me ke faruwa ba ita ma kukanta shiga rerawa, Umad kam wuri ya samu ya zauna k'afa d'aya kan d'aya yana kallonsu, sai tsohon ne ya rabasu ya ce su zauna, zaune tsohuwar tayi daf da Ayam ta rik'e hannunta gam kamar za'a rabasu, shi tsohon gefenta ya zauna suka sakata tsakiya.

Kallonsu tayi dukansu tana ziraro wasu hawaye tace" Alamu sai k'ara nuna min suke Habbee da Utais ba iyayena bane na gaskiya, sai dai kuma bana so abinda ak fad'a akan mahaifina na gaskiyar ya tabbata, da haka ya faru zan so na yi ta zama a cikin rayuwar nan mai kama da mafarki."

A tare tsofaffin suka d'ora hannunsu a kan ta da niyyar shafawa, amma da suka ji a tare suka d'ora sai tsohon ya janye na shi ya bar na tsohuwar, cike da kulawa da k'auna tace" Ayam hak'uri zakiyi, haka shi ne jarabawarki kin ji."

Kallonta tayi tace" Ku su waye?"

Ajiyar zuciya tsohuwar ta sauke ta nuna kan ta tace" Ni sunana *Bilkis* sarauniyar Egypt, wannan kuma *Abdallah* sarkin k'asar Egypt, mu iyaye ne ga mahaifiyarki wacce tayi nak'udarki wato Juman, gimbiyar Egypt sarauniya kuma a Khazira."

Juyawa tayi ta kalli tsohon ta rik'o hannunshi tana kuka tace" Da gaske ku d'in ku kuka haifi mahaifiyata? Da gaske ne sarauniyar Khazira ta haifeni kuma ta bayar dani ga jakdiyarta?"

Jinjina kai yayi yace" Tabbas gaskiya ne, duk da bamu had'u da mahaifiyarki mukayi magana baki da baki ba, amma dai abinda aka fad'a miki gaskiya, mahaifiyarki tayi hakane dan kub'utar da ke."

Cikin matsancin kuka tace" To amma ce wa suke harda mahaifina ma cikin masu son kasheni, taya haka zai yiwu?"
Chapter 37 · 0% Book details