← Book details Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 86

Sashe 28

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ganin ya fita ta fad'a kan gadon ta sake rushewa da wani kukan tana sake fad'in "Wai me yake shirin faruwa ne da ni?"

Umad na fita kai tsaye b'angaren Joyran ya nufa inda ya ga mahaifinsa yayi, bai samu kowa a b'angaren ba haka ma a falon, tsaye yayi a tsakiyar falon yana dubawa, a ranshi ya tambayi kan shi "Ina kuma suka nufa?"

Hannu d'aya yasa ya shafi sumarshi ya d'aga kafad'a alamar ohon nan sannan ya juya zai fita, ya fara takawa kenan ya ji sautin Joyran ta kwamtsa k'ara da "Ahhhhh."

Dakatawa yayi ya juya ya kalli k'ofar da ya ji sautin, da d'an sauri ya fara takawa dan ya ga ko lafiya, sai kuma ganin mahaifinshi yayi ya fito daga d'akin Joyran a bayanshi ta rik'e babbar rigarshi tana share hawaye.

Wani irin mummunan bak'on yanayi ne ya ziyarceshi sanadiyar abinda zuciyarsa ta hasko masa lokaci d'aya, gagara komai yayi sai zuba musu ido suna ta kame-kame, daga bisani kuma sai mahaifinshi ya juya gareta a hassale ya fincike rigarshi ya nunata da yatsa yace "Na gama magana Joy, ko kina so ko ba kya so yanda na fad'a haka za'a yi, dan ba zan yarda ki zubar min mutumci ba, kowa laifina zai gani a ce da saka hannu na a faruwar komai."

Juyowa yayi dan fita har ya zo daf da Umad zai rab'ashi ya wuce, da kallo Umad ya bishi yace" Sarki na, meyake faruwa ne?"

Wani huci ya dinga saukewa yana hararen Joyran data k'araso garesu, cikin shashek'ar kuka tace" Umad, mahai..."

Da sauri ya katseta da fad'in" Ciki ne da ita, ni kuma ba zan yarda wannan labarin ya fito ba."

Da matsanancin mamaki ya kalli sarki yace" Ciki?"

Kallon Joyran yayi data shiga k'yabta ido, a razane yace" Ta ya ya? Goggo wa ye ya miki ciki kuma ba..."

Da sauri sarki Wudar yace" Waziri ne, dama soyayya suke amma rashin lafiyar mahaifiyarka ta sa ta k'i aminta da maganar auren."

Wani iska Umad ya huro daga bakinshi ya dafe goshi, shiru kamar ba zai ce komai ba, ya d'an jima haka suma kuma jiran abinda zai fad'a suke, can ya d'ago ya kalleta yace" Amma gwoggo m yasa zaki yarda da haka kamar wata k'aramar yarinya, yanzu gashi ya kike so muyi?"

Sarki Wudar ne yace" Abinda nake fad'a mata kenan, na ce a zubar ta dage ita ba za'a zubar ba."

Zaro ido yayi ya kalli mahaifinshi yace" Sarkina zubarwa kuma? Gaskiya ni ma ban goyi da bayan haka ba, kar a zubar mahaifina."

A d'an hassale yace" To yanzu ya kuke so a yi? Ba fa zan yarda a haifa min shegen nan ba."

Da wani kallo Joyran ta d'aga kai ta kalleshi, da k'yar ta had'iye abinda ya tokare mata ta sunkuyar da kai, a nutse Umad ya kalli mahaifin na sa yace" Abba na ka je kawai, zamuyi magana da ita, kar ka damu da abinda mutane zasu fad'a, zan ji da komai."

Kallon Joyran sarki yayi irin kallon garhad'i kafin ya juya a hassale ya fita, ajiyar zuciya Umad ya sauke ya kalli agogon hannunshi, kallonta yayi da sauri yace" Goggo zan je amma zan dawo, ki kwantar da hankalinki kinji."

Jinjina kai tayi alamar to, da sauri ya juya ya fita dan sallolin dake kan shi yae san saukewa wanda suka riskeshi a hanya.

*12:36* daga d'akin mahaifiyarshi cikin sand'a ya shigo nan ba tare da ya bari kowa ya gan shi ba, a hankali ya bud'a k'ofar ya shiga ya mayar ya rufe, yana juyawa das ya sameta zaune tsakiyar gadon, fad'uwa gabanshi yayi dan yanda ta zubawa k'ofar ido da kuma yanda take zaune ya nuna fa tun da ya fita ya barta haka take, a hankali ya k'araso yana kallon fuskarta da idonta da sukayi jajir suka d'an kumbura, jiki a mace ya zaune gefenta yana ci gaba da kallonta ita ma kuma haka.

Cikin tattausan murya yace "Me yasa da aka kawo miki abinci kika kori mai aikin?"

"Saboda ba shi nake da buk'ata ba." Kallonta yayi yace "Me kike da buk'ata yanzu?"

D'auke kai tayi daga gareshi tace "Iyaye na, ina so na gansu, ka mayar dani wajensu ni har karatun ma na fasa."

Girgiza kai yayi yana murmushi ya jawo wayarsa a gaban aljijunshi, tana kallo ya dinga danna wasu lambaobi, ko da ya danna ok ya mik'o mata wayar yace "Kiyi magana da su, hakan zai sa hankalinki ya kwanta."

Da sauri ta karb'i wayar ta d'ora a kunne jin tana k'ara, ana d'auka cikin muryar kuka da sangarta tace "Hello!"

Cikin zumud'i da karsashi Habbee ta amsa da "Gimbiyata, gimbiya kina lafiya?"

Mik'ewa tayi tsaye tace "Mah ban da lafiya, gaba d'aya bana jin dad'i, so nake na ganku."

Cikin ladabi Habbeetace "Kiyi hak'uri kinji gimbiya, zamu had'u nan kusa, ki kwantar da hankali ki saki jikinki da mutumin nan, mutumin kirki ne, na tabbata zai kula dake yanda ya kamata."

Juyowa tayi ta kalli Umad sannan tace "Mah, ni ban yarda da kowa ba, maganar gaskiya ma a tsorace nake, wasu abubuwa ke ta faruwa a nan kuma babu wanda yake min bayanin komai."

Daga b'angaren Habbee ta numfasa tace "...

*Kuyi hak'uri da wannan yan uwa, akwai gobe Insha'Allah*

*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:36 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

_SADAUKARWA GA_

*'YA'YA NA*

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

*16*

Daga b'angaren Habbee ta numfasa tace "Gimbiyata, ki gafarce mu, tabbas kan ki zai d'aure idan kika ji b'oyayyan sirrin dake tattare da ke, watak'ila ma ki kasa yarda damu, amma dai gaskiya ce wacce kowa ya san ta ban da ke kawai, fatana kawai idan kinji gaskiyar nan kar mu zaba ababen zarginki bare ki hukunta mu."

Rud'un data shiga ne yasa sai ta ji kamar bata fahimtar, sai kuma tayi k'arfin halin saurin fad'in" Dakata Mah, wai ke ma ya kike neman kin d'aure min kai ne ? So kike ki tabbatar min akwai alamar gaskiya a zantuttukan mutanen nan kenan?"

Numfashi ta sauke har saida ta ji sautinshi a kunnenta kafin tace" Hakane ranki shi dad'e."

K'ank'ance idonta tayi tana karkad'a yatsanta tace" Kenan gaske da yarinyar nan tace ni yar uwar ta ce? Kuma mahaifinmu shi ne..."

Da k'arfi tace" Kai... Ina ba zai yiwu ba, kuna yanzu Mah?"

Saida Habbee ta kalli lafiyayyen d'aki da suke sannan tace" Wani waje ne mai sirri ne, ya ce kar mu fad'a saboda tsaronmu na wuyansa."

A harzuk'e tace" Ina kuke mah? Ina son ganinku yanzu."

A ladabce Habbee tace" Kar ki damu gimbiyata, zamu had'u nan kusa."

D'auke wayar tayi a kunnenta ta mik'a masa tarz da fad'in" Ina son ganinsu yanzu, ya za'ayi?"

Mik'ewa yayi tsaye yana huro iska ya kalli fuskarta, saida ya mayar da wayar aljihunsa a nutse yace" Ki gane Ayam, rayuwarki na cikin gagarumin had'arin da ubangiji ne kad'ai yasan iyakarsa, ba wai wani banza bane ke neman rayuwarki, masarautu ne suke wawarki, yayin da wasu daga gefe ma suka nemanki ruwan a jallo, dayawansu a shirye suke da su biya bilyoyin kud'i dominki, wasu alkairi ne a zuk'atansua game da ke, wasu kuma akasin haka, na d'auki alhakin kula da ke ne dan na ga na hana masu nemanki cin nasara a kan ki, ki bani dama ki kuma kwantar da hankalinki, hakan zai bani damar ceto rayuwarki."

A sanyaye kuma a ladabce cikin sigar tausayi tace" Wane irin had'ari ne na ke ciki haka?"

Kai tsaye yace mata" Had'ari ne da ya kai matakin kisa, kamar yanda na fad'a miki kowa da manufar sa ta son samunki, wasu na nemanki ne kawai dan su kasheki."

Tsoro k'arara ya bayyana a tare da ita ta zazzaro ido ta ji kayan cikinta na neman yamutsawa, ckkin muryar d'ar-d'ar tace" Me na aikata musu haka da suke son kashe ni?"

Da hannu ya mata alamar ta zauna kan gadon, zaunawa tayi tana rarraba ido dan tsorl ya gama kamata, a cikin aljihunsa ya ciro takarda, zaune yayi kusanta ya warware takardar ya mik'a mata yace" Karanta."

Karb'a tayi ta fara karanta takardar dake nuni a cikin littafi aka cirota ko kuma an buga irinta ne, ba wani dogon bayani bane a takardar face zanannun zanen da aka tsara kuma aka wassafasu a cikin tsari ta hanyar fad'in _" A wace shekara ce? A wane wata? Wace rana ce wannan? Babu wanda zai sani a cikinmu, saidai alamun bincikenan malaman babbar fadar k'asar Texanda dake birnin Khazira ya tabbatar da za ta zo, za'a haifeta ne kawai dan zuwa da sabon tsari sannan ta wanzar da adalci, zuwanta shi zai kawo k'arshen duk wani azzalumi ko da sarkin dake mulki ne, zatayi mulki na ban mamaki da ba'a tab'a kwatanta irinshi a k'asar ba, zata kafa tarihi da dubbanin shekaru zasu shud'e ana magana a kai, tambayar a nan ita ce, *talakawan gari ne zasu haifo wannan biwar? Ko kuma cikin msu kud'i ne da iko ? Ko kuma dai wannan lu'u lu'u zata fito ne daga masarautar khazira*?"_

Da mamaki ta kalleshi dan abun bai wani d'ad'ata a k'asa ba tace" Me wannan ke nufi? Jaridar yaushe ce? Ko kuma labarin film ne, kana so na fito jarumar?"

Wani murmushi ya saki dan sosai ta bashi dariya, gyara zamanshi yayi yace"Kin fahimci me labarin ke magana a kai?"

Jinjina kai tayi ta yatsina fuska tace" Kusan haka."

Shi ma jinjina kan yayi yace" Ayam wannan rubutun wani babban mutum ne yayi shi, wannan mutumin shi ma yana da baiwa irin ta wannan da akayi magana za'a haifa, sanadin baiwar da Allah ya masa gaba d'aya masarautar khazira aka shiga girmamashi, sanda ya sanar da abinda zai faru gaba ba kowa ya yarda ba, saidai kuma an zuba ido ana jiran tsammanin a ga ta inda wannan zab'abb'iyar zata sake fitowa."
Chapter 28 · 0% Book details